Maldives 2

8.5K 650 2
                                    

Ana gama round one, Sultan ya fara shirye shiryen komawa filin daga na rike fuskarsa da hannayena duk biyun ina kallon idonsa nace "Sultan sallah fa" yayi ajjiyar zuciya ya dora kansa akan kirjina yana sauke numfashi, sai kuma ya dago kai da sauri yana kallon agogo, nima na bishi muka kalla tare 8:30pm, muka kalli juna, Sultan yace "akwai shaidan a gurin nan" da sauri ya mike ya tafi ya hada mana ruwan wanka, cewa nayi ya fara yi, dan wankan tare ma wani abin zai kuma jawowa. Dole muka hada magrib da isha mukayi a tare.

Na dauko waya ta na saita alarm for all the five daily prayers, dan in kana gurin nan ba sani zakayi ba. Ranar Sultan cewa yayi a waje zamu kwana, ya shimfida mana blanket mai laushi a kan floor din waje, ya saka mana pillow duga daya sannan ya sake daukar mana bargon lulluba. A gurin akayi serving din mu dinner, muna gamawa suka zo suka kwashe kayan. Dadin iskar gurin kadai ya isa ya saka mutum bacci ballantana ga gajiyar da muka kwaso, da assuba sanyi ne ya tashe mu duk kuwa da makalkale juna da mukayi muka kudunduna, dole muka koma daki mukayi sallah sannan muka koma bacci, duk da dai ba baccin muka koma ba dan Sultan cewa yayi shi a dictionary dinsa babu baccin safe.

Da safe na kira Mommy na gaya mata inda muke nace amma kar ta gayawa kowa, she was concerned, tace "to ke yanzu ga yanayin da kike ciki kuma in wani abin ya faru fa? Ba gwara ke ya kawo ki gida ba shi ya zauna?" A raina nace 'Mommy kenan, me raba mu ni da sultan ai sai dai mutuwa kuma, mutuwar ma in san samu ne ta dauke mu tare' na kwantar mata hankali da nuna mata cewa ai suna da asibiti me kyau anan din, sannan zanke zuwa lokaci zuwa lokaci ana duba lafiya ta data babyn, kuma nasan me nakeyi dan haka da naji wani chanjin da ban yarda dashi ba zan tafi asibiti.

Muna gama waya da Mommy na kira Ummee itama, tana jin muryata ta sauke ajjiyar zuciya, "Maimunatu I have been waiting, jiya banyi bacci ba, how are you?" na tabbatar mata cewa lafiya lau muke daga ni har Sultan, kuma zamu ke kiranta akai akai muna gaisheta. Na bata Sultan suka gaisa sannan ya kashe.

Rayuwa mai dadi muke shimfidawa a Maldives, kullum zamu dauki hayar speedboat mu fita yawo, island by island, duk inda mukaje zamu dauki pictures da camera din da Sultan ya sayo mana, in kuwa muka dawo cabin din mu to abu daya ne zamuyi tayi, sallah ce kawai da cin abinci suke raba mu da junanmu, har mamakin mu nake yi, sam bama gajiya da junan mu, yanzu za'ayi yanxu kuma za'aji kamar anyi sati ba'ayi ba.

Cikina kam tunda na shiga third trimester sai kara uban girma yake yi da nauyi. Sam girman sa amma baya hanani sakewa da Sultan, shima kuma hakan banga yana wani takura masa ba, dan kamar game muka maida abin, in mun gwada wani abin yaki yi sai mu koma wani, it makes it more fun. Sultan seems a bit gentler dai yanzu kuma nasan saboda cikin ne, amma dai he is usually rough, haka yanayin sa yake.

Bani da wani complication, dan duk wata doka da ka'ida ina bi, exercise kam wannan inda ace yana yawa da har yawa zai yi min. Lol

Muna yawan waya gida, and things seems to be happening a Nigeria, abu na farko anyi bikin Munir, suddenly abin ya faru, yaje 'yalleman da daddare ya fita aikin nasa, ya samu 'yar mutane a loko yana mammatsewa sai baban ta ya gansu, a take kuwa yaje ya gayawa Baffa wanda ya kira uncle Rufa'i yace a daura musu aure, ga kewaye nan a gidan ta tare anan, sannan shima Munir din ya baro Lagos tunda dama ba wata uwar yake yi acan ba sai kashe kudin mahaifinsa, ya dawo nan 'yalleman a nema masa ko teaching ne ya fara yi, kuma yake kula da su Baffa da matan sa tunda duk samarin yanzu babu.

Haka kuwa akayi, aka daura wa Munir aure aka tattaro shi aka dawo dashi 'yalleman aka nemar masa aikin koyarwa. Ana bani labarin ina dariya kuma ina jin tausayin yarinyar dan a kanta zai huce, ita kanta Aminar da take bani labarin dariya take yi, tace "yanzu in kika ganshi sai kinji tausayinsa, Baffa ya saka shi a gaba, dama Baffa ga tsufa da rikici, kuma gashi dama babu kowa a gabansa, dan haka tare suke komai da Munir."

Abu na biyu da ya faru shine neman auren Amina da akaje yi 'yalleman, farko uncle Rufa'i yaki yarda, amma da yaga Daddy ne akan maganar sai yayi shiru, ansha dai rigima da Baffa dan cewa yayi shi bazai bawa bayarabe jikarsa ba, Daddy ne da uncle Aliyu suka dage, suka saka Baffa a gaba da nasihohi ta lallami suna nuna masa irin tarbiyyar yaron, bashi da wani nakasu da addini zai ce kar a bashi aure, kuma suka nuna masa irin wannan intertribal marriages din shine zai kawo solution a rigin gimun kabilanci.

MaimoonWhere stories live. Discover now