Daddy

7.3K 657 1
                                    

Kowa a gurin sakin baki yayi yana kallon Sultan, hatta Daddy rasa mai zaice masa yayi, ya jima yana kallon sa shi kuma Sultan ya sunkuyar da kansa kasa, a zuciyarsa yana wishing ina ma dai zai iya kuka, maybe in hawaye ya fito masa zai ji sanyi a zuciyarsa, wannan mutumin da yake tsaye a kansa is his only chance to happiness, idan yace yes to shi kam ya samu duk wani buri nasa na rayuwa, in yace no kuma tamkar ya saka full stop ne a rayuwar Sultan.

Daddy ya sauke ajjiyar zuciya yace "wannan shine dalilin ka na shigo min gida ka tayar min da hayaniya? Wannan shine dalilinka na dukan securities dina?" Sultan ya kuma sunkuyar da kansa yana jin bugun zuciyarsa yana karuwa. Daddy yace "tambayarka nake yi fa?" Sultan ya dago kai ya kalli Daddy da jajayen idanunsa yace "Daddy ba zasu bar ni in ganka ba ne. And I must see you. Tun a England muka shirya da Moon za ta kawo ni gurinka, bamu samu dama ba, anan ma muka sake shirin zuwa ganin ka shima still bamu dace ba. This is the only way for me to see you" da mamaki daddy yace "ita moon dince ta amince maka kazo gurina ka nemi auren ta?" Sultan ya gyada kansa yace "yes daddy, kuma yanzu I don't even know where she is"

Daddy ya jinjina maganar a ransa, in dai har Moon ce ta turo shi gurinsa then she must have her reasons, maybe reasons dinta yana daga cikin dalilan da yasa Mommy ta dauke ta.

Ya juya ya kalli Walid a gefensa yace "Walid shigo dashi ciki" ya juya ya koma ciki, Walid ya bishi da kallon mamaki amma shi yasan bai isa yayi masa musu ba, yiwa iyaye musu baya daga cikin tarbiyyar da aka basu. Ya mika wa Sultan hannu da niyar ya taimaka masa ya tashi tsaye, Sultan ya watsa masa mugun kallo ya mike sannan a hankali yadda su biyu kadai zasu ji yace "zan dawo kanka ne" bai jira Walid yayi masa jagora ba ya bi bayan Daddy.

Ya tarar palourn da yaga Daddy ya shiga babu kowa, da alama Daddy sama ya hau, akan carpet ya zauna ya harde kafafunsa ya zabga tagumi. He was ready to wait ko awa nawa ne, ko kwana nawa ne, indai har at last Daddy zai saurare shi. Walid ya shigo ya samu guri can nesa da Sultan ya zauna, babu wanda yace wa kowa komai har Daddy ya sauko, ya yi wanka ya chanza kaya sai kamshi yake, Sultan ya kalli kayan jikinsa, sun chukurkude saboda fadan da yayi da securities, babu abinda yake sai warin gumi, ya daga kafada bai damu ba.

Daddy ya zauna akan kujera yana studying Sultan. He is a perfect mixture of his father and mother. Fuskarsa sak ta Khairat sai dai kawai shi namiji ne ita mace, sai kuma duhun fata da ya fita saboda yayi mix da duhun fatar babansa, kirar jikinsa kuma sak na babansa lokacin yana age dinsa. Daddy yana hango su a idonsa suna yawo tare ko'ina a Oxford. What has gone wrong tsakanin su?

Yayi gyaran murya yace "bismillah malan Abubakar, fara daga farko, a ina ka hadu da 'yata kuma menene a tsakanin ku?" Sultan ya danyi shiru yana controlling emotions dinsa sannan ya fara bada labari, komai sai da ya fada wa daddy, da boye boyen da suke yi saboda tana tsoron kawo shi gida, rayuwar su a England da America, amma duk bluntness din Sultan bai bada labarin toilet experience dinsu ba, ya bada labarin plans din da suka ringa hadawa na zuwa ganin Daddy amma ana samun sabani, ya bada labarin matsalar da suka samu akan project dinta da fushin da yayi ya tafi bar ita kuma ta bi Amir ya kaita gurin shi, ganin da Munir yayi musu da zuwan Walid.

Sai da ya gama kaf sannan yace "dan Allah Daddy kar ka raba mu wallahi mutuwa zanyi, I have no body a duniyar nan sai ita" Daddy ya kalle shi a nutse yace "you look like your mother" Sultan ya dago kansa da sauri ya kalli Daddy yana tunanin anya kunnen sa ba karya yayi masa ba, sam babu wasa a fuskar Daddy, ya sake cewa "kamar ku daya, sai dai ta fika fari, ta fika kuma hankali da nutsuwa" da rarrafe sultan ya karaso gaban Daddy yace "you know my mother?"

Daddy ya gyara zama yana kallonsa yace "ba sosai ba, dan bamu taba magana da ita ba, amma na san ta kuma ina ganin ka nasan dan ta ne kai. Oxford sukayi karatu ita da babanka, lokacin yana kamar ka. Baban ka was exactly like you, he was a rogue too. A gang leader na 'ya'yan masu kudi" Daddy yayi murmushi yana tuno rayuwarsu ta makaranta ya cigaba da cewa "ni lokacin dan talakawa ne dan haka bana cikin su, ina dai hangen su suna yawo da motoci a cikin makaranta. He was so energetic, so stubborn like you. Duk sanda na ganshi a TV yanzu sai inyi ta mamakin yadda akayi ya koma haka"

MaimoonWhere stories live. Discover now