The Thin Tall Man

10K 750 4
                                    

💘  *Maimoon* 💘
      *2nd Edition*

*Maman Maama*

Episode Three: The Thin Tall Man

Nidai har ga Allah wannan hukuncin baiyi min dadi ba, saboda haka kawai naji raina baya son copper dinnan, he is too young to teach us a ganina. Hafsat kuwa sai na lura babu abinda ya dame ta. Da nayi mata magana sai cewa tayi "laa ni ban wani damu bafa, musamman akan geography, wancan teacher din ya fiya bayar da note, kin san ni kuma bana son note" (Yar Hutu). Unlucky for me, washe gari muna da geography. Tun safe naji raina ya baci dan ma ba shine first period ba, sai munyi biology sannan zamuyi shi. Teacher din biology yana gama yi mana sai ya bamu assignment, yana fita sai na dauko assignment dina na fara sai naji hayaniya a class anata leka window. Na tambayi Amira nace "menene wai ake wannan leken" sai tayi dariya tace "wannan yaron ne ya taho zai koya mana geography" nayi tsaki nace "zai koya musu dai" na ci gaba da zanen da nakeyi na digestive system dan shine assignment din da biology teacher ya bayar. Naji Hafsat tace "sabon shiga, ko dan late coming dinnan ma abar mutane su huta baza ayi ba". Tana gama fada yana shigowa kuma na tabbatar cewa yaji abinda tace, dariya ce ta kubce min ganin yadda Hafsat ta wani maze kamar ba ita ce tayi maganar ba. Ina kallonsa ta gefen ido na. Ya cire uniform din NYSC ya saka normal shirt da wando amma ya dora p-cap din NYSC din a kansa. Ban wani kalleshi sosai ba na maida hankali na akan zanen da nake yi. Ya jima a tsaye yana kallon mu daya bayan daya sannan a hankali yace "don't you guys know how to greet? Duk class din muka mike a tare, tare da cewa " good morning Sir" ya jima yana binmu da kallo sannan yace "sit down" ina jin Hafsat a hankali tace "finally" Nayi murmushi na zauna tare da ci gaba da zane na. Takowa yayi a hankali yazo gabana ya tsaya yace "why are you laughing?" Na dago kaina na kalle shi ido cikin ido nace "I am not laughing Sir, I was smiling". Ina jin yan ajin suna dariya kasa kasa. "Hmm" shine abinda yace sannan ya kunna board, da yake smart board muke amfani dashi. Ya saka flash drive dinsa na nemo slides din da zai yi mana ranar ya kunna. Ni kuma ina ganin haka na cigaba da zane na. Ina jinsa yace "our topic for today is rocks and their origin". Sannan yayi tambaya "who knows what this is?" Ban dago kaina ba ballantana inga abinda yake tambaya akai saboda ina expecting wani a ajin ya bada amsa, amma ga mamaki na sai naji shiru babu wanda yayi magana. Jikina ne ya bani ana kallona, na daga kai sai na ganshi a tsaye a kaina yana kallona yace "Miss Smiler, we are trying to have a class here. Can you please, out of the goodness of your heart, tell me what this is?". Ya fada yana nuna board, yayin da ni kuma nake kallon sa a raina nace lallai wannan mutumin ya raina min hankali. Ya dan bude ido yace "the picture is displayed on the board miss smiler, not here" ya sake fada yana nuna kansa. Dariya na jiyo kasa-kasa daga bayana sannan na fahinci cewa kallonsa nake tayi. A hankali na janye idona daga kansa. Kallo daya nayi wa hoton black shiny stone din da yayi displaying a board, na dauke kaina. Na mai da dubana kan assignment dina tare da daukan pencil dina na cigaba da zanen da nake yi. A hankali nayi magana nace "that's an obsidian sir". Shi kansa da yake kusa dani bai ji abinda nace ba, dan haka ya sunkuyo da kansa yace "can you PLEASE, raise your voice a little bit?" Take naji raina na sake baci. "PLEASE" Ya sake cewa da muryar challenge. Dariya na sake ji daga baya na. Ni kuma har lokacin zane na nakeyi. Har ya juya zai koma gurin board sai na daga murya ta nace "That is an Obsidian" Chak naga ya tsaya sannan a hankali ya dawo inda nake zaune ina zane na yace. "Tell me more" murmushi nayi sannnan na fara kwararo masa bayani tun daga kan yadda earth core take da yadda rocks suke melting su zama lava, yadda mantle da crust suke budewa har lava din ta fito earth surface. Daga nan na koma kan bayanin different types of cooling and solidification na lava din yadda yake producing different kinds of rocks. Sannan na dawo kan shi obsidian din, cooling process din da yake forming dinshi, dalilin da yasa yake black and shiny, composition dinsa, life span dinsa da amfanin sa a gurin mutane. Nafi 30minutes ina magana kuma at the same time ina cigaba da drawing dina. Tunda na fara magana ajin yayi tsit babu wanda yayi magana har na gama. Gamawa ta yayi dai dai da gama drawing dina. Sai da na karewa drawing dina kallo na tabbatar na gama sannan na dago kaina na kalle shi ido cikin ido tare da cewa " Is there anything more you want to know, SIR?" Na fadi kalmar sir din nima cikin challenge. Sai da wajen 30sec ta wuce sannan ya iya magana yace "wow, that is very correct. No, there is nothing more. You have said it all".

MaimoonWhere stories live. Discover now