A Chance

8.9K 727 3
                                    

Geography lecture din da muka yi was very interesting. Sai yanzu na fahimci abinda Hasiya take nufi lokacin da tace yana bin komai dalla-dalla. He makes sure He carries everybody along. Yana making references da abubuwan da na fada rannan kuma yana kara buda su dayi mana bayani using simple terms wanda ko the most stupidest person zai gane. Anan na kara fahimtar cewa shi mutum ne mai tsantsar nutsuwa, komai nasa a hankali yake yinsa. He is very gentle, bashi da hayaniya sam.

Toward the end of the class sai ya bamu classwork, kowa ya rubuta abinda ya fahimta a game da topic din yau for 10mins. Kowa ya dauko takarda ya fara rubutu, ni kuma na duba takarduna na rasa fullscap sheet, sai na juyo gurin Hafsat nayi mata alama da hannu akan ta bani paper, take mutuniyar tawa sai ta makale kafada tare da murguda baki. Takaici ya ishe ni gashi time yana tafiya. Sai na juya gurin Amira. Kafin Amira ta fallo min sai naga an ajiye min paper a gaba na, na daga kai na kalleshi na ce "thank you sir" ya amsa da "don't mention, what are friends for" tare da yi min irin kallon nan na 'kin tuna?'. Nayi murmushi nima na fara rubutu.

Ga mamaki na sai na ganshi ya zauna akan desk dina kusa da takardar da nake rubutu a ciki. Lokaci daya wannan special kamshin nasa ya ziyarci hancina, naji wani iri a jiki na tun daga kaina har zuwa yatsun kafata, nan tubutun ya gagareni dan duk ideas dina guduwa sukayi suka barni na kasa hada koda cikakken sentence ne. Na saba jin masculine scent a wajan su ya Walid but it never have this effect on me, nashi is like special, it tells me that he is very much male.

Na zama very uncomportable har absentmindedly na fara fidgeting da kasan hijab dina. A hankali ya sunkuyo da kansa sai tin kunnena, unexpectedly naji yayi min magana yace "am I making you uncomfortable?" Ya fada in a very low whisper. A firgice na dago kaina sai ga idona tsaf cikin nasa with his face few inches from mine. In that instance da muka hada ido dashi, everything froze, me, him, time, the class and even my heartbeat. Ido na ya rufe bana ganin komai, kunne na ya toshe bana jin komai. A cikin wadannan seconds din (or maybe minutes, I don't know), babu abinda yayi existing a duniya ta sai shi, only him. Fuskarsa kadai nake gani, kamshinsa kadai nake shaka. Apart from him komai ya zama blank. A hankali na fara jin muryar Hafsat tana cewa " sir, sir, sir" sai muryar kuma ta fara karfi sannan ta zama tamkar kara a kunnena. Nayi blinking once, twice sai a sannan common sense dina ya fara dawo wa, sai a sannan na fahimci abinda ya faru. We have been staring at each other for a while (I don't know for how long). Take naji tamkar kasa ta tsage in shige ciki, na dauke fuskata da sauri zuwa daya side din. Sannan na lura cewa kusan duk 'yan class din mu suke kallo. Hafsat naji ta sake cewa "sir" da karfi, daga jin muryar ta nasan cewa she is really angry. Yau na san na shiga uku. What is happening to me? What just happened? Murya can kasa naji yace " yes, what is it?" "I am through sir" " through with what?" Ya tambaya har yanzu muryarsa bata dawo dai dai ba kuma clearly kansa ma bai dawo dai dai ba. "Through with the class work sir, you gave us classwork, remember?" Ta fada tamkar mai shirin tashi sama, "ohhh" shine abinda kawai yace yana shafa kansa. Sai kuma ya mike ya kama hanyar fita yana cewa "keep it with you. I will collect it tomorrow" daga haka ya fice ba tare da ya juyo ba, ba kuma tare da ya dauki glasses din sa, handset da papers dinsa da ya ajiye akan podium ba.
.
Yana fita Hafsat ta zagayo gaba na tare da saka duk hannayenta biyu ta rike kugunta ta na kallona fuskarnan filled with fury ta fara yi min masifa " were you flirting with the thin tall man ko idona ne yake min karya" na bita da kallo ina mamakin mai take nufi, I still don't fully understand what happened, ni ina ganin kamar stroke na samu, for all I know I could be sick or something "answer me" ta sake doka min tsawa. Kafin in bata amsa teacher din mu na physics ya shigo, a dole Hafsat ta zauna tare da zagaya hannun ta a wuyanta alamar I will kill you.

Muka gaishe shi, ya amsa da fara'arsa, ni dai duk jikina a sanyaye. Bayan mun zauna ne ya kalleni yace "Moon, what is wrong with you?" Hafsat tayi sauri tace "help me ask her oo". Da yake teacher din mai barkwanci ne Sai yayi dariya yace "maybe the geography was so boring, worry not my dear, I will cheer you up with physics " akayi dariya gaba daya.

MaimoonWhere stories live. Discover now