"yanju kai ma'u yaja kayi kacan halin gwoggon ka ba dae rahin mutunshi da bala'i ba, gaci jauro ba amo bare labarita gaci kuma ko rabi baka ciyar ba"

ma'u ta nisa tare da fadin,

" to ya ja'ayi duka ne dae na shaba sanshi don baffah ma bata gari tayi tafiya caido sanunta burni, kuma aradu gwoggo bahi da imani ko kadan"

lamunde ta tab'e baki tace

" to ma'u ya xakayi yau gahi nima kinga shed'i wala (banda kudi), dashe in baki to kaga yau ba muyi wani shiniki ba"

ma'u tad'an juya idanu tace " aradu kar ka wani damu kanka kai inma kudin gare ka in ka bani me xaka shewa inna, in dae nice na saba bari ma kaga wannan furar shanyeta zanyi don nasan gwoggo koda gajeran wando da tocila da adda nake kwana, wato ina kwana da shirin fada kena ko? ba zata bani abinshiba, sai baffah ta dawo kuma ma rabon da ta bani abinci tun shekaran jiya da baffah ta tafi sae dae in naje kiwo in sha nono"

Lamunde tace " a kul dinki ma'u kin dae shan halin shi kamar yunwar shikinki"

ma'u ta kyalkayle da dariya har da buga cinya, tace " lallai kai kana nufin damammar furar zan kai mata, kace yau tayi k'uli na kenan, kai kacika shoro wlh" dukkansu suka kwashe da dariya😂

ma'u tace, " bari ma kagani", ta buda k'aramar kwaryar da ta damama jauro fura wadda tasha nono da sukari nan ta soma sha har ta shanye.

NB:
ZA KUGA HAUSAR TASU BAD'AD'I, TO HAKA SUKE YIN TA, INBA ITA BA TO FULATANCI, FULATANCIN MA YAFI YAWA, AMMAN ZANNA MUKU NORMAL HAUSA DON KU FI GANE LABARIN.

Haka wunin suka k'are zaman su amman ba cinikin da suka k'ara, don yau kamar ana kore mutane, ba mutane da yawa a waje sakamakon wata kwalleliyar ranar da aka tafka kasancewar yanayi ne na muku mukun zafi.
Ma'u ce tafara cewa

" uhhhm lamunde garin mu da nisa tashi mu tafi kinga yanma ta k'arato"

Nan suka nad'a gammansu suka kwashe tarkacen su da kwarerayin su, suka shiryasu tsab a kansu suka d'au hanya, suna tafe suna y'an hirarrakin su sae da suka zo wajen rabuwa inda kowa zaeyi hanyar gidansu sukayi sallama, har sunyi nisa da juna laminde ta d'aga murya tareda cewa " in mun had'u gobe da safe a rafi kya labarta mun ya kukayi da gwoggon taki, suka sa dariya kowa ya d'au hanya.

Sai da ma'u ta fara hango soran gidan su, sannan gaban ta ya fara dukan 3 3, gabanta ya fara fadi sosai ta tsorata don tasan halin gwoggo kamar yunwar cikin ta, haka ta k'araso cike da fargaba ta tsaya a zaure tana lek'a cikin gida,
ta
d'au ak'alla minti biyar a waje, kamin daga baya ta shige, nan ma a zaure ta kuma
tsayawa tana lek'en cikin gidan
sai lek'e take, taga ina gwoggo
take? kuma me takeyi?,
Can na hango wata y'ar dattijuwa ta fito daga wani k'aramin gini, da alama bayi ne dan naga buta a hannunta, da ganin ta kaga bak'ak'en fulanin nan wanda ba sa son raini ko k'adan,
Da alama ma'u bata lura da ita ba, don tana can tana lek'a cikin gidan, tana sand'o, can dattijuwar ta hango ta tace

" haba y'annan sae ki tsaya a zaure kina lab'e kamar wata marar gaskiya_"

bugun xuciyar ma'u yaka'ru a sadda ta jiwo muryar gwoggo ta fara magana, kuma da alamu ta bayan ta take,
ta had'e wani wahalallan miyau k'uttttt, sannan ta juyo a kasalance tana firi firi da idanuwa,
Gwgo daganin haka tasan an dab'o dan tasan halin ma'u,
taci gaba

"shigo mana ki ban kud'in kike wani xare ido kamar bak'ar angulu dama ga ido kamar na mayu"

ma'u tayi shiru

Tace " to ko dae baki saido bane"

nanma shiru
taci gaba, "a'h da alama ko!"

nan ma'u ta fara takowa a hankali kamar wadda kwai ya fashe mawa a ciki,
sae da tak'araso daf da ita sannan ta dire kwaryar a gabanta tare da tsugunnawa tana fad'in

"washh gwoggo yau ba sa'a hamsin nayo, tana k'ok'arin kwance xanin ta ta fiddo mata kudin, ji kake tassss

Gwgo ce ta kwashe ma'u da mari, ko ni da bani aka mara ba sae dana tsorata na dae saita birona na maida duba na ga ma'u,
ma'u kam sae da taga wuta dan saeda idanun ta suka dauke wuta na wucin gadi,
dan gwgo cecin k'arfinta ta zabga mata mari gurin ya tashi sosae yayi ja 😈
abunka da farar fata,

Ba abun da ma'u ke inba kuka ba gwgo taci gaba da bambaminta tana fad'in

" kaji y'ar k'ota me k'ashin tsiya dan uwarki kuma inga kinxo min da sunan kina jin yunwa, in b'an b'ab'b'alla kiba na murde maki wanan tsinannan bakin naki ba"

Duk da k'arancin shekarun ma'u kuma duk da batasan wacece uwar ta taba amman tana matuk'ar jin zafi in gwgo na xagar mata uwa,
Dama ita ma'u bata barin ta kwana komin wuya, dan
haka cikin k'arfin hali tace

" ba dae uwa taba wlh" ta k'are tana turo baki,
Gwgo ta aje butar dasauri tana tafa hannu tana salati, maaaa'u wato ba dae uwar ki ba sae dae in tawa kenan ko?, ma'u tace
"ni dae bance ba"
Gwgo tace " babbar magana biredi na sosa d'uwawu to meki ke nufi nenene, in banda kin maedani yarinyar goye ko?"
nan ta shiga kirb'arta kamar Allah ya aiko ta ita ko ma'u in ban da ihu ba abun da take, ko dan akawo mata dauki duk da tasan ba wanda zaeyi kasadar ceton nata, don kowa yasan halin gwgo yanxu sae ta had'a maka wani bomb d'in,
Koman
girman ka sae ta iya zage generation dinku kaf.

Duk kuwa da mutanan da suke ta lek'e ta katanga wasu har turmi suke takawa, amman ba me iya ceton ma'u, sae dae su bita da addu'ar Allah ka rabata da muguntar hanne ( sunan gwgo kenan)

Itako ma'u tun tana ihun kukan har tagaji sae gunjin kukan da take kawae,
Sai da gwgo tagaji dan kanta sannan ta sake ta, sae haki take tsabar gajiya, ta wawuri kudin da ma'un ke bata wanda suka fadi sanadiyar bugun da take mata, sannan
taja kwaryar furarta ta d'irga ta tsab taga ba ta saba'in tace "kan uba keee zonana" ma'u ko da har ta lallab'a ta tashi tana son tashige d'akinta
Kasancewar sanin halin gwgo da tayi, dan in har ta dakeka ka jib'e a gurun, to ko dukanka xa tai tayi har sae ka tashi kabar wajen, ma'u jin gwgo tace taje yasa ta tsayawa cak don a gaskiya bazata iya komawa ba dan da kyar ma
ta kawo in da take da jan gwiwa,
Kuma tasan dawan garin dan tasan akan me yasa gwgo ke kiranta,
Gwgo da
Kanta tak'arasa har inda take da empty butar ta a hannu, ta sake mai mai ta mata tambayar ta a k'ufule,
Ma'u ta ansa da
" yoo ni yunwa nai taji kuma wani kad'o ne yace in dama mashi kuma ya gudu be xo ya karb'a ba, ni kuma na shanye kar ayi asara"
Ma'u dae bakin ta bae mutuwa in dae akan ta ma gwgo rashin kunya ne, koman wahala kam.
Gwgo tace "asarar ubanki ne zaiyita, ba seki maidomun abata ba, ko ko da ubale muka had'a kud'i muka siyo geron?"

Ma'u ta turo baki ba tae aune ba taji gwgo ta sakar mata butar hannun ta akan ta, da k'arfi ta tattakura ta kwala mata wanda har butar sae da ta b'are, nan ma'u ta silale k'asa luuuuuuuu......

*QUEEN BK*

A / N

Assalamualaikum guys!

hope you are enjoying the story!

if yes press the vote button and also show your support by commenting too.

Till then take care and keep reading!

lots of love
QUEEN BK

ZAN SOKA A HAKAWhere stories live. Discover now