Sakin ajiyar zuciya tayi ganin maganganun nata kamar suna tasiri a wajen Abdallah dan yadda ya natsu yana sauraronta da yadda ya cigaba da zubar da k'walla kamar yana nadamar abunda ya aikata, a hankali ta cigaba.







"Be kamata ace muna fad'a a tsakaninmu ba, kamata yai ace mu had'u mu tara k'arfinmu guri guda domin mu shiga wannan fagen dagan muyi yak'i da mak'iyanmu free palour dan yanzu maganar tsoro ta k'are, maganar kwantan b'auna ya k'are dan ina ga kamar shi yasa ake cin galaba akanmu, yanzu kawai karo da karo za ai ga fili ga mai doki saura sukuwa kawai duk wanda ya iya allonshi sai yaci nasara, insha Allahu ko da rainane zan fanshi rayuwarka ya Abdallah" sai ta fashe da kuka tana sadda kanta kasa.







Ga mamakinta sai taji hannu Abdallah akan kumatunta yana k'ok'arin share mata hawayenta, da sauri ta d'ago tare da cusa idanunta cikin nashi abubuwa da yawa ta karanta a k'wayar idon nashi da sauri ta fad'a jikinshi tana k'ank'ameshi cecin k'arfinta, hannunshi ya zagaye a bayanta yana jijjigata, duk da bai ce komai ba amman hakan da yayi ba k'aramin sanyaya ran Asmah yayi ba, duk sai taji k'amshin jikinshi ya mata yar wani dad'i take ji inta shak'eshi kamar kar ta tashi a jikinshi taji, d'agowa tayi tare da kamo hannunshi ta shiga yi mai dressing d'in ciwon da yaji.




Sai da ta gyara wajen tsab sannan ta kunna suratul bak'ara a falon kira'ar sudais tasa k'arar yar dai dai, tunda taga Abdallah baya nan tasan yana d'akinshi kamar taje sai kuma wata zuciyar ta hana ta, babbar kujera 3 sitter ta zauna can gefen k'arshe cike da rashin sanin abinyi, Abdallah ne ya turo k'ofa ya fito har ya sauya kayan jikinshi zuwa jeans da riga, rigar maroon ce kamar yayi ne dan Asmah, itako a ranta take cewa "shikenan ya gama dani" kallo d'aya ta mashi ta sauke kanta dan ya mata kwarjini da yawa.








A hankali ya taka har inda take ya zauna kan kujerar d'an nesa da ita shiru ba wanda yayi magana har tsawon y'an mintocin da ba zasu fi biyar ba can Kuma Abdallah ya zame ya kwanta tare da d'ora kanshi a cinyar Asmah hannunta d'aya ya kamo ya had'e da hannayenshi ya d'ora bisa k'irjinshi har tana iya jiyo harbin zuciyarshi, kulle idanunshi yayi yana sakin ajiyar zuciya, a hankali itama Asmah ta saki ajiyar zuciya sun kuyowa tayi dai dai fuskarsa ta sumbace shi a goshi, d'an k'aramin murmushi ya bayyana a fuskar shi duk da bai bud'e idanunshi ba, d'ayan hannunta tasa cikin sumar kanshi ta shiga shafawa tana lailayawa a hankali, a haka har bacci ya sureshi, itama kanta ta maidar jikin kujerar a haka itama baccin ya saceta.












8:00pm...............


Asmah ce zaune tana cin dambun da tayi dan sai yanzu taji marmarinshi a hankali ta fara sak'a da warwara a cikin zuciyarta, "to ko dai ya Mahmud yasan abunda Auntyn yara take aikatawa ne?, In ba haka ba me yasa yace in sa mata idanu a wayance dan akwai abunda ya ke so na fuskanta tattare da ita, ko dai shima ya sani ya bar ma kanshi sani ne kamar yadda nayi?, Ko kuma wannan zuwan nashi ne ya lura da wani abu? Am really curious to know what he knows, anyway zan dai ji Dan komin nisan jifa k'asa zai dawo kuma na k'agara nasan wane yak'i ne yake fad'in zamuyi dani dashi, ya Allah kasa yak'in da nake fad'in zanyi shi Ya Mahmud ke nufi in dai haka ne zan ji dad'i sosai atleast bani kad'ai bace ba I have one to side with me ko ba komai tsoro na zai ragu, oh my Allah see me through i really want this thing to go as fast as possible, ya Allah ka kawo mun kariya daga gareka kuma ka taimakemu da taimakawarka ya Allah.




Ok now I need to set the ball rolling, mission d'ina yanzu in sama Auntyn yara ido ko? Ok let's get to dat and it will be very easy dan dama na saba so it's not going to be a problem" wani murmushi tayi da ita kad'ai tasan ma'anar abunta, gani nai ta d'auki bak'ar abaya ta d'ora bisa kayanta sannan ta fita bayan ta kauda plate d'inda ta gama cin abinci...............










ZAN SOKA A HAKADove le storie prendono vita. Scoprilo ora