"yauwa ya Abdallah kasan aure ko? Wanda ake biki mutane da yawa suzo ace an ɗaura auren wane da wace, wanda liman yake ɗaurawa? Aure? Kagane?"

Sai da ya kaɗa ido, sannan ya kaɗa mata kai alamun ya gane.

Tace "Good yauwa, to sai anyi irinshi sannan ake cewa miji da mata kagane ko, to mu" ta faɗa tana nuna shi da ita sannan ta cigaba "mu ba muyi ba shiyasa mu ka zama mu ba mata da miji ba ka fahimta ko?"

Ɗaga kai yayi kan yace " To Asmah yaushe zamuyi?" ya faɗa yana taɓa kumatunshi da duka hannayenshi yana ƙunshe dariya.

Da ƙarfi Asmah tace "Mehhh?" tana sakin baki.

"Aure" ya faɗa yana ƙara ƙunshe dariya.

"Dawa"

"Dani da ke mana" ya faɗa tare da nunata sannan ya nuna kanshi yana haɗa hannayenshi guri guda.

Girgiza kai tayi alamun a'a, in a convincing voice tace " kagani matsayina dabam naka dabam, duniyata dabam taka dabam akwai banbanci sosai a tsakanin mu" tana gama faɗin haka ta tashi da sauri ta bar wajen kan ya ƙara ritsota da wata tambayar, da idanu ya bita har ta fice, cewa yayi "duniyata? duniyarta? me hakan ke nufi?" sai kuma ya ɗan saki ƙaramin tsaki tare da faɗin "duniyarmu ɗaya mana" kana ya furzar da iska daga bakin shi yana faɗin "rubish".




##################

Abbah ya kalli Ammie yayi murmushi yana faɗin
"Aiko kin kawo shawara Ammiensu, amman kina ganin ba wata matsala kuwa, kuma kina ganin yarinyar zata yadda kuwa"

"Haba Abbansu na gaya ma da yardar Allah ba wata matsala, dan Allah ka bar faɗin matsalar nan, ina ji ajikina ɗumɓin alkhairi ne"

"To in alkhairinne Allah ya tabbatar mana dashi cikin gaggawa"

"Ameen ameem Abbansu"

"yanzu ke zaki mata magana ko?

"Ay Abbansu kamar yadda mukai ni zan mata, muɗe zaɓin Allah muke nema dan haka za mu cigaba da addua'a in alkhairi ne Allah ya tabbatar mana in kuma akasim haka ne Allah ka kawo makushinta"

"Hakane kinyi magana mai kyau, Ameen summa ameen"

"Wallah abbansu a jiki na inaji alkhairi ne abun nan?

Nan suka ɗaga hannayensu suka kwararo adduo'i kana suka shafa.



×****//******/***///**/**

Washegari ammie na zaune kan kujera a falonta, "yauwa" tace kamar ta tuna wani abu, jawo wayarta tayi wata number ta nemo cikin contacts ɗinta, sannan tayi dialing, ringing ɗaya biyu aka ɗauka, daga ɗayan ɓangaren aka fara magana

"Salamu alaikum hajiya Amina mun wuni Lafiya"

"Wa alaikumissalam Nafisa yakike ya hidindimu"

"Lafiya lau masha Allah ya naku, ya fama da yaran mu, ya kuma wajen masu jiki ince dai duk lafiya ko?"

"Lafiya lau masha Allah ya ƴan makaranta"

"Ana can dai ana ta fafatawa da litittafai"

" To Allah ya bada sa'a ince dai kina ji daga gare su ko?"

"ƙwarai kuwa Hajiya dan yanzu ma muka gama waya da MARWAN"

"To masha Allah, yauwa nace ba, iba damuwa ko takura dan Allah in kin samu lokaci ki ɗan shigo akwai maganar da nake so mu ɗan tattauna dake"

"Insha Allahu kuwa hajiya, ba wata damuwa zan shigo jibi, juma'a kenan  dan gobe zan ɗan kai ziyara ƙauyenmu ne, amman dai ina fatan ƴannan ba laifi ta maki ba ko?"

"Kinji ki wane irin laifi kuma, in ma laifin ne ai tsakanin mu ne ni da ita sai mun saki? bama san shigar shugula da ƙwala kai a faranti" Ammie ta faɗa cikin muryar zolaya

Gaba ɗayansu suka kwashe da dariya, Aunty Nafi tace " Tuba nake hajiya, nayi laifi ina ni ina maku shigar shigula"

"To gwanda dai maki, to sai kim shigo ina duban hanya, a gaida mutan ƙauye da kyau"

"To zasuji sai na zo ɗin"
daga nan suka yanke wayar.




A/N

Salam readers

How was this chapter
Its all about conversation huh? but dix conversations are not just there, there is really an information i want 2 pass, hope u got my message huh?

Insha Allah i will update more sooner this tym, infact tomorrow i will be updating, yah stay tunned, ohhhhh b4 i forget i'll lyk to thank those who voted 4 my story it really means alot, so don't forget to vote and comment i love 2 hear ur oppinions.

Fiamanillah
👸🏼QUEENBK👸🏼

ZAN SOKA A HAKAWaar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu