Asmah tace
"yanzu dai kan wannnan zura hannunki muci" ta faɗa tare da kamo hannunta tana sa mata fork a ciki tace "ci",
ajewa tayi tana faɗin "ke a ƙoshe nake" wata uwar harara Asmah ta galla mata tare da faɗin "wasa kike wallahi, ke da na sanki da ɗan wake ai duk sona da ɗan wake kince mun kau nan, sannan kice bakici"

Tace "jiya da daddare shi naci, yanzu kuma ina ON ne kuma kinsan yadda in ina yi ban cika cin abinci ba ko?"


"Kyaji dashi ciwon ajali a ɗan yatsa, ke yau ko blood bank ne ya fashe ba damuwa ta bace all i know sai kinci ɗan waken nan" ta faɗa tare da maida mata fork ɗin a hannunta.



"Yau naga ƙarfin hali wai mai hali yana bara" Zarah ta faɗa tate da kallon Mimi.

Mimi tace "gwanda ma kici ni ba shigar maki zan ba, ki daina mun fuskar tausayi"

Suka sa dariya gaba ɗayan su ma maganar Mimin, Zarah tace " okay okay u've won the bet, i better eat if not this girl is gonna be the death of me" ta faɗa tare da nuna Asmah sannan ta fara cin abincin duk da bata so ci ba, dan bata yanaƴin cin abincin.



Bayan sun gama ci sun kwashe kayan sun wanke hannu suka dawo suka baje a tsakar ɗaki, kamar yadda suka saba Zarah ta fara basu labarin littafin da ta karanta, FULANIN DAJI, sun natsu suna sauraronta domin Zarah ta iya bada labarin littafi tana yi tana masu demostrating yadda za sufi ganewa, sun daɗe a haka har la'asar ta ƙarato, Asmah tace "kai gaskiya Joda ta birgeni" Ita kuna Mimi tace "ni soyayyar su da Mahmud yafi birgene Wallah" Asmah tace "uhm ni dai na gane tashar da kika dosa Mimi" Mimi ta kalleta tace "ban gane ba wace tasha kike nufi, yau kuji Asmah ta faɗa hausa na rasa gane inda ta dosa dako ko hausar kirki baki iya ba, hausar ƴan fulani ta iya" Zara ta kwashe da dariya tace " kash wallahi zan so inji kallar hausar da kike da" Mimi tace bari kiji sai dai kan ta buɗe baki Asmah ta bita da filo tana ƙwala mata.



Suna gama sallar la'asar, a tare Mimi da Asmah Suka hada baki wajen cewa "a cigaba da labari" wanda hakan ya basu dariya, Zarah ta katse masu dariya da faɗin "My time is off, dai dai lokacin da Mami ta ɗiɓar mun kenan"
Asmah tace " Da kinsani kinzo da ƴar lele Ikram"
Zarah tace "Ai tana makaranta kema kinsan da da ita zanzo, ko ba komai zan fake da ita"
Mimi tace "ƙarfe nawa ne Mami tace ki dawo?"
Zarah ta amsa da " ƙarfe 4:30" a tare sukai kai mata duka, Asmah ta kama kanta ta juya shi saitun agogo tana nuna mata da hannu tare da faɗin

"indai ba jan rai zaki mana a labarin nan ba, kalla lokaci ƙarfe 4:40pm, we still have 50 minutes to go"

"Ay jan ran zan maku, duk wanda keson labari ya biyoni har gidan mu, haka kawai san banza naku yayi yawa, inzo har gida sannan na baku labari" Cewar Zarah tana jujjuya idanu.


Mimi tace "ya hakuri Zarah wallah ba daɗi munsani za muzo, suprise visit zamu maki, kuma sai munyi wuni, yanzu dai a bar maganar nan mu koma kan labari"

Asmah ta amshe da "Kar ki wani lallaɓata Mimi" sannan ta juya ga Zarah tace "Wallah Zarah kar kiban haushi na fara Karanta Novel zakisha mamaki"

"Ayi mana, kullum maganar kenan ki fara mana, ni birge nima zakiyi"

" shikenan very soon kuwa zan fara"

"in zaki fi birgeni ki fara yau"

Hannu Asmah ta miƙo mata tana faɗin "Bani wanda zan faran"

Zarah ta juya idanu tace "angaya maki ɗan fashi bai yawo da makami ne"

"prove ur self" cewar Asmah

Mimi tace "kamar da gaske"

Zarah tai wata hamshaƙiyar dariya tare da janyo jakarta, ta fiddo wani littafi 1 to 3, ta damƙa a hannun Asmah, Asmah ta karanta sunan littafin "TAWA TA SAME NI" tace "daga ji zaiyi daɗi"
Mimi ta amsa tana dubawa tana faɗin "ni zan fara karantawa"

ZAN SOKA A HAKAМесто, где живут истории. Откройте их для себя