Bayan ya gama gwaje gwajensa, ya masa allurar bacci kana ya masa ta pain relieve, sannan ya bada wasu magunguna yace in ya tashi, a bashi sannan a haɗa mashi lipton da lemon tsami a bashi, insha Allah komai zai lafa.

Ammie tace "Dr. Kb har yanzu baka faɗa mun meke samunshi ba, duk ciwonsa bantaɓa ganin kallar wanda ya azabtar dashi ba kallar na yau ba, da alama wani abunne da ban"

"Ay gaskiya wani abunne da ban, amman ki kwantar da hankalinki hajiya ba wani abu bane na tada hankali"

"To inba wani abu bane na tada hankali ka faɗa mun mana"

"Ay zan faɗa amman ina so ne Alhaji ya dawo sai in faɗa maku gaba ɗaya"

"Abbansu sai fa talata zai dawo yaje dubai ne saro kaya"

"Shikenan Allah ya dawo dashi lafiya, bari in tafi da ya tashi aka bashi magungunan kukaga ba dai dai ba ku kirani"

"To shikenan Dr. mun gode"

Yana tafiya Ammie ta ƙara matsawa kusa dashi, fuskar shi tayi fayau baccin shi yake a hankali kuma yana fidda ajiyar zuciya, ta kama hannun shi tana tofa mai addu'oi.

Sai Azahar lis ya tashi duk anbashi abunda Dr. yace a bashi kuma ba laifi yasa mu sauƙi sosai, kawai dai bai iya tashi ne don daya tashi juwa yake ji.


****     ******     *********

"Ki tausaya mun wallahi ina sonki, Asmah na fara fargabar rasa ki wallahi, kin kosan yadda nake sonki bana iya tunanin zan iya rayuwa baki, dan Allah kimun magana mana ko naji sanyi a raina, rashin ansanin nan da kike wallah yana mun illa a zuciya, yana kuma samun kokontan anya baki san da maganar Aunty nafy ba?" Aliyu ne ya gama faɗin haka bayan ya gama koro ma Asmah da yadda sukai da Aunty nafy.

" ya Aliyu bana maka ƙarya kuma bazan fara yanzu ba, bansan magana ko ɗaya akan wannan batun mijin da aunty nafy take magana ba"

" To Asmah yanzu ya za ayi me kika tunanin itace mafita"

Yadda taga duk ya ɗaga hankalinshi akan batun, yasa tayi amfani da muryar lallashi wajen faɗin "ya Aliyuna ka kwantar da hankalinka Asmah taka ce, kuma ka sani nima ina sonka kuma bana fatan rabuwar mu in ba mutuwa ba saiko ƙaddara daba mu iya kaucewa"

"Hmmmmm in kina faɗin kaddarar nan sai in riƙa jin wani yanayi kuma gabana sai yana faɗuwa, dan Allah kin bar faɗin haka zanje inta addu'a kuma kema kina yi, Allah ya fishemu Alkhairi"

"Ameen ya Aliyu"

daganan kuma suka juya akalar hirar tasu...




##################

*RANAR TALATA*

Abbah, Ammie, da Dr.kabir ne zaune a babban falon Abbah, kasancewar Auntyn yara bata nan tana cikin gari gaisuwa,
Dr.KB
ya
maida kallonshi ga Abbah
kana yace wannan ciwon cikin
da Abdallah yayi kwanakin baya da suka wuce
ba komai bane illah yana da
buƙatar mace wato yana da
sha'awa wanda hakan shi
ya haddasa mashi ciwon cikin,
yanzu mafita kawai ammai
aure domin yanayin ciwon
nashi zai iya shan wahala sosai in hakan bata
samu ba, kallon kallon Abbah da Ammie suka shiga yi,
Ammie ta nisa tare da faɗin

" toooo Allah gamu gare ka, hmmmm anzo wajen inji mai kukan wanka yanzu shi Abdallah da ko budurwa baida yaza ai a shawo wannan batun?"

Abbah ya amshe da " to ƙaddara ma yana da budurwar wace ZATA SO SHI a yadda yake balle har ta aure shi?"

Dr.Kb yace "aa Alhaji kar kace
haka akwai mata da yawa
daza su so Abdallah a yadda yake,
domin abdallah gushewar hankali kawai ya
samu kuma shima muna sa
ran bana har abada ba, baya
da haka namiji kamar Abdallah har akwai wacce za amata tayi tace
bata sonsa da kamar wuya,
matsalar kawai wasu matan
ta wani fannin zasu ɗauki
abun, kasan su mata akwaisu da ɗaukar gulma,
wasu kodan kar ace wacce mijinta yana da taɓin hanakali baza ta fara ba,
wasu kuma ko dan kuɗi za
suyi, matsalal shine kuma
azo ba a samu soyyayya a
tsakani ba, domin ya kamata a ce akwai soyyayya mai karfi tsakanin shi da matar shi yadda
zatana kula dashi sosai, kuma
kaga in anyi dan kuɗi maganar so be ma taso ba,
kunga kuma ba tausayi a tsakani,
kuma mu we are not after
that, amman Alhaji mai zai
hana ku bin cika cikin dangi
nasan baza a rasa wacce *ZATA SO SHI A HAKA* ba.

Abbah yace "shikenan Doctor mun gode da shawara sosai insha Allah we will put our effort on that"

Dr yace " Allah ya taimaka bari inzo in tafi"

Ammie tace " To Dr. In ciwon nashi ya kuma tashi ba wani magani da za a bashi?"

"Ay akwai na gaya ma asmah tana haɗa mashi lipton da lemon tsami duk dare tana bashi, haka ma in ya taso kubashi shi komai zai lafa insha Allahu"

"To madallah mun gode a gaishe da iyali"

Bayan tafiyar Dr. Ammie ta dawo kujerar da Abbah yake suka zauna suna fuskantar juna, shiru ne ya wanzu na tsawon daƙiƙa biyar, kowa da kalar tunanin da yake a zuciyar shi, Ammie ta fara cewa

"Abbansu yanzu ya za'ayi kai nake jira ka fara magana"

Sai da ya saki dogon lumfashi kana yace " the issue is complicated saboda yanzu duk cikin jikokin gidanmu yara ne manyan duk sunyi aure, saiko Samira da Amiran ya Aminu ( babban yayansu) kuma ansamasu rana, to sai wa kuma?" ya faɗa tare da nuna alamun yana tunani.

"To Abbansu duk inasu sholin (Aisha) da zainab ɗin ya mustafa ai suma duk sunkai minzalin aure yanzu fa Ss3 suke, ga juwairiyyar Anty Ruƙƙayya ma"

"ohhh to to to na tuna koma dai meye zan samu ya Aminu mu tattauna, Alabashi sai inbar komai a hannunshi, zan kuma samu Aunty uwani ( ƙanwar babansu) da maganar itama bazata rasa ba tunda naga tana riƙa mata da yawa"

"To hakan yayi dai dai nima zan cigaba da bincikawa Allah sa mu dace"

" Ameen, sai dai kisani duk wacce zamu samo sai mun tabbatar zata so Abdallah a hakan da yake, so na tsakani ga Allah nake nufi"

"Ay na fahimta Abbansu Allah ya zaɓa mashi mata ta gari, sai mu dage da addua"





A/N

OUR PROPHET ❤

HE IS THE MOST BEAUTIFUL CREATION OF ALLAH TA'ALA AND HIS NOOR EXISTED EVEN B4 GOD MADE ADAM A.S

FIAMANILLAH
👸🏼QUEEN BK👸🏼

ZAN SOKA A HAKANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ