Haleematu ( 47)

28 2 0
                                    

Na: Reedahmz
47

Haleematu tana jindadin school kuma tana fahimtar karatun ga abokanta nitsattsu idan bata gane ba suna fahimtar da ita shakuwa ce mai karfi take kara shiga tsakaninta da Hamza a cikin su ukun gabadaya, harta kai kullum tare suke shiga class wurin zaman kusa da juna nan abokan shi suka fara cewa anya Hamzo ba soyayya kuka fara da Yarinyar nan ba kuwa yayi murmushi yace, kubari lokaci yafada Kawai Ilyas yace muna jira Amman ai kundace ma Hashim yace sosaima zasu bada kala duk sukayi dariya yace dasu amman mizatayi da talaka? Sukace na Allah ne...

Haleematu tana kwance Shamsu yakira ta yace da ita yaya yanayin makaranta tace Alhamdulillah tana fahimta sosai yace hakane yakeso tace in sha Allah banda kawayen banza kinsani tace nagode Yaya sukayi sallama. Tace ko anyi hutu bazan tafi ba gara in nemi wani abu da in koma ukubar su Inna larai, cikin tunani wayarta tayi Kara taga Hamza tadaga tace Ina zuwa tafito waje tasameshi suka gaisa yace yazo yaduba yatake ina Sara? Tace tana dakinta yace zai wuce tace dasauri haka sukayi dariya Duka ya miko mata lemo da yazo mata dashi tayi godiya yayi tafiyar shi takoma.

Inna larai abubuwa sun kankama ta kwantar da kanta lub sai yadda tajuya Baba laraba da Mu'azzam kudi kuwa tatsarsu takeyi sosai wurin Mu'azzam kuma bai isa yace Babu dashi da mahaifiyar shi Rabia kuwa ga school ga Kuma shirin biki da ake tayi , Shamsu dai yazama dan kallo Saboda abin yana bashi mamaki yadda Komi Baba laraba bata jayayya da mahaifiyar shi bai san duk aikin sihiri bane shi kanshi tasa anrufe bakin shi babu dama yace komai sai ido

Hamza Ilyas da Kuma Hashim sunata maganar fara exams suka gama can sai Ilyas yace Hamzo ina da magana

Hamza yace inajin ka, Ilyas yace don Allah idan har kanason Halima kafada mata kar kwado yayi maka kafa. Hashim yace wannan magana ta Aboki gaskiya ce mu a tunanin mu dakuma zaman tare yawwa

Hamza yace Ina tunanin ko bazata Soni a haka ba tunda sanin kanku ne niba dan kowa bane kunsan Komi kuna ganin zataso talaka irina? Hashim yace in sha Allah bazata ki ka maganar gaskiya kenan..

Yace in sha Allah zangwada sa'a ta idan har ta amince nikuma namaku alkawari kunada gift..

Bayan shi baije ko ina ba saiga Halima a zuciar shi yace yawwa yanzu zan sanar da ita in sha Allah yayi Mata murmushi bayan tazo dab dashi suka sake gaisawa ta zauna bisa dakali yace don Allah wani magana nikeso muyi besty ....

Haleematu On viuen les histories. Descobreix ara