Haleematu (31)

51 4 0
                                    

Na: Reedahmz
Page 31

Rabi'a nashiga daki ta samu Baba Laraba da Inna Larai tace Hmmmmm wallahi Yaya shamsu son Haleematu yake naji tattaunawarsu da Yaya Mu'azzam tsaf ta zayyane masu yadda taji da kunnenta wuf inna larai tace bazaiyuba shamsu ni ina Baba Laraba tace barshi muga gudun ruwanshi shiru sukayi duka don neman mafita don kuwa deeni yadauko dala ba gammo can Inna Larai tace Ashe duk take takensu shiyasa yake hanata ashe duk muzuranan danake ganin yanayi burga ce ni zai ninke baibai toh baka isa ba indai nice nadau cikinka na haifeka bazaka Aure ta ba.

Cikin daki sunyi shiru mu'azzam yace inaso kafadawa Haleematu yau abinda ke cikin ranka kafin gobe kabar garinan kasan kar azo a sami matsala bata san kanayi ba gara tasani kuma ko wurin kawu zaka iya zuwa don kar ayi maka irin nawa tunda kaga misali dai Shamsu yace hakane Dan uwa zanyi haka tunkafin asamu akasi suji kuma afara yawo dani nace inason Haleematu sukayi dariya yace kasan fa iyayen namu ne sai addu'a maza jeka idan bakowa cikin gida ya sauri ya leka wundon dakinta yaganta shiru yayi gyaran murya yace da ita kisameni a zaure inada magana.

Tayi firgigit tamike tafito tayi zaure da hijab dinta tasaka nan tasameshi ta tsaya gefenshi tace Yaya gani ya gyara tsayuwa yace Haleematu kikara hakuri da rayuwa don Allah sannan kidinga tunawa a rayuwa kinada dani ni mai kaunarki inasonki kinsani kanwata tace eh Yaya tadauka yana fadamata ne a matsayin Yayanta sai taji kwatsam yace So nike in aureki intafi dake inda ko kuda bazan bari yatabaminke ba a firgice ta kalleshi yace Yes kobaki yarda ba bugun zuciarta yakaru tace Yaya miyasa kukeson daukar abinda zamusha wahala akai Shamsu yace Kamar ke ko me akayi akanki ba wahala.

Haleematu Where stories live. Discover now