Haleematu (29)

49 5 1
                                    

Na: Reedahmz
Page 29

Baba Laraba tace zauna Larai Ashe baka da hankali wannan yuyun zaka daukomin toh baka isa ba koda wasa Rabi'a ta fashe da kuka Haleematu sai zuru tayi kawai don tadade da fahimtar Yaya mu'azzam kawai dai tana zubar hawaye natausayin kanta cikin dangin mahaifinta ace tazama abin kyama haka Baba Laraba tayi gyaran murya tace Mu'azzamu idan nice na haifeka toh bakai babu Haleematu har abada indai zancen Aure ne sannan idan nice na haifeka baka da mata sama da Rabi'a fakat tayi shigewarta ta daki.

Mu'azzam yayi shiru yarike kanshi dake saramishi yace wayyo Allah yatashi yayi dakinsu Haleematu tabishi tace sannu kayi hakuri duk dan Adam baya wuce kaddararshi yaya idan ni rabonka ce zakasameni idan kuwa ba rabonka bace duk yadda ka kai da sona bazaka samu wuf Rabi'a tashigo tace kije mama na kiranki ta fice tabarsu yana kwance yace don Allah Rabi kice bakyason aurena please tace aa Yaya bazan cuci kaina ba wallahi inayinka sosai ya rarumi filo zai jefeta dashi tayi waje da gudu suka ci karo da shamsu yashigo takusa bigeshi ya zare ido yace to mahaukaciya kalli gabanki tace yi hakuri yawuce ta Haleematu tazo ta amshi kayan kamar batacikin damuwa tace Yayana Barka da dawowa yace Nagode kanwata sukayi cikin gida tare.

Haleematu Where stories live. Discover now