Haleematu (56)

33 2 1
                                    

**Na: Reedahmz
**56**

Hamza sundawo Haleematu ta kwashe labarin yadda sukayi da Sunusi ta fadamishi yace ki rabu dashi masifa yake nema kuma in sha Allah bazai samu ba tace Allah ya sa Aamin ya rabbi Farin ciki na nan tayi murmushi suka cigaba da hirar su ta masoya har lokacin sallah yayi suka kama gabansu don yi Sallah..

Inna Larai tana zaune tana cikin kaza sai sallamar tasallah nan tace tashigo daga ciki don Baba laraba tafi gidan kawu Umar, nan Inna Larai tamika kwano wa tasallah tasa hannu ta debi tsoka tanaci suna hira har hirar tasu tadawo kan Haleematu nan Inna Larai take shaida mata komi, tasallah tace ohhhhhhh ke har kinbarta tayi Aure? Inna Larai tace keda Allah ai wannan Auren jeka nayika ne, yaron aski yake yi fa dakyar suka zo tambaya, tasallah tace kai Larai kin san kan mugunta... Suka sheke da dariya tace atoh shiyasa niketa so ayi ai tafara dandana kudarta natsani inga tana walwala, tasallah tace maganar Deeni kuma ga wannan dole yaji tafita ranshi kisa cikin abincin shi kawai duk sai yadda kikace haka zaibi. Larai tace nagode Kawata ta dunkula dubu ashirin tamika mata, itakuwa tayi tafiyarta cikin jindadi.

Rabiatu tadawo gida ciki yasata a gaba shikuwa Mu'azzam antura shi course din 3 month a South Africa shine Baba laraba tadaukota tana kula da ita ga tarairaya itakuwa sai zuba iskanci take shafi shafi.

Shamsu yadauki waya yakira Mu'azzam suka gaisa yake shaida mashi baya son Auren Ummi da mai askin nan, Mu'azzam yace yanzu kai kayiwa Ummi adalci? Kai kaki aurenta babu wani dalili sannan kace bakaso wani ya aureta wani irin son zucia ne dakai? Shamsu yaja dogon numfashi yace Dan uwa ka fahimci abinda nikeso ka fahimta bawai ban yaba da natsuwar yaron bane sana'ar shi ce batamin ba. Mu'azzam yace ai tunda ba sata ko zaman banza yake ba dasauki kaidai ka tayata da addu'a ok shikenan. Ya Africa Alhamdulillah to Allah yabada sa'a yadawo daku lafiya Amin Dan uwa sukayi sallama yakoma bakin aiki...

Malam Hamid tareda Alh Muhammad suke tsara Auren Hamza cikin natsuwa Alh Muhammad yace yanzu saura a koma don da rana ko yakagani Yaya? Malam Hamid yace eh in sha Allah hakan za'a yi suka gama yace toh Yaya nizan wuce gida, toh ka gaishe da mai dakinka da yaran...

Exam yayi Zafi kan Haleematu yadau zafi sosai donkuwa karatu take sosai don ganin burinta yacika Hamza yakance tayi hakuri tabi komi a sannu in sha Allah za'a yi nasara, takan ce Habibi bakasan wahalar danasha ba a rayuwa kaga dole in yi karatu yace Hakane Allah ya sa mudace...

Angama exam lafiya Haleematu ta tattara kayanta tsaf Hamza suka zo da motar su Hashim suka dauketa don zuwa tasha cikin mota yake cewa nifa zan rufe shagon askin nan fa sai bayan aure Iliyas yace munji zumudi suka fashe da dariya yace toh kudai Sanaa zan canza dukkan su sukayi mashi addu'a ta dacewa da bukatar shi Amin sukace..

Cikin Tasha Hamza yace kinsan kuwa wata sati su Baba Hamid zasu zo batun sa Rana? Tayi shiru tace sai yanzu dakake fadamin yace to kishirya dai zaman mangu tace ai tunda ina kaunarka ko cikin daji ne zan zauna yace shiyasa kike kara shiga zuciata ta rufe ido tace Alhamdulillah daga can Dan Union yace hajia mota tacika tace to gani zuwa Hamza ya biya kudin motar tashiga suka tafi tana daga mashi hannu..

Sunusi yace Sagir dole muje Bauchi fa, Sagir yace tayaya? Ta Ina zamu fara? Yace karkadamu zan tambayi Hashim cikin dabara hummmmm cewar Sagir babu Kyau nema akan nema fa yace nidai saina mallaketa Sagir yace shikenan yaushe zamu tafi? Gobe da safe in sha Allah toh Allah ya kaimu...


Haleematu Where stories live. Discover now