Haleematu (14)

71 4 0
                                    

**Na:Reedahmz
**Page 14

Saukarsu keda wuya almajiran gefen gidansu Amina suka dau kaya suka shiga dashi cikin gida iyaye da kannen Amina sukayi farin cikin zuwan Amina da iyalan nata akayiwa Malam iro karamci kunsan Katsinawa da karrama bako yayi sallah suka sake gaisawa da yan gidansu Amina.

Amina itace ta uku a gidansu, su biyar babansu ya haifa Malam Usman Safana yanada matarshi guda wato Mama Deeja itama garinsu daya Safana Yayansu sune Abubakar, Hamza, Amina, Hayatu, da auta Jidda Mahaifin Amina baitaba wani Aure ba inbanda Mama Deeja itace tahaifi yara biyar dinan.

Amina itace diyar dasuka fara Aurarwa don dukkan mazan basu taba aure ba Malam Usman yanada rufin asiri don yana siyar da kayan abinci ne a can Kofar marusa bai ragi iyalanshi da komi ba kuma zasuyi sa'a da Malam iro ganin hankali da kamala irin ta Malam iro yasa aka bashi auran Amina.

Yayun Amina duk suna buga buga don samun nasu dakuma ragewa Mahaifinsu nauyi.

Washegari Malam iro ya shirya tsaff don komawa Bauchi sammako yayi yace yanaso ya isa da wuri nan Baban Amina yasake yiwa iro nasiha don rike mata biyu sai hakuri yatashi yaturo Amina don suyi sallama da mijinta da yaranshi tafito zaure yace toh zanwuce a kula da yara in sha Allah sati biyu zanzo intafi daku.

Tayi murmushi yace zanyi kewarki yake matata mai hakuri tace Malam kayi hakuri kamar gobe ne in sha Allah zaizo, yadau dubu uku yabata yace ki rike ko ke ko yara zasu bukaci wani abu duk da nasan baba bazai rageki da komi ba tace dashi kaida kake hanya aida ka rage yace da ita inda babu bazan baki ba tasa hannu biyu ta amsa tayi godiya da addu'ar Allah ya tsare Ummi tace byee byee Babaaaa ..

Haleematu Where stories live. Discover now