Haleematu (55)

32 3 0
                                    

**Na: Reedahmz
**55**

Inna Larai tace inace da bakinka kace kafasa aurenta yanzu tasamu miji shine zaka mata bakin ciki? Anya kanada tausayi kusa deeni? Haleematu ta fahimci basajar Inna Larai kawai ta sunkuyar dakai kasa tana dariya saboda tasan makirci ne... Shamsu yace Inna nifa bansan miyake faruwa dani ba, tace toh Allah ya sawwake kayi hakuri kawai don bazaka maida mu mutanen banza ba tayi wucewa zuwa dakinta cikin zuciar ta tana cewa lallai aiki yayi sanyi dole innemi tasallah a waya. Ta zayyana wa Baba laraba itama tace aikuwa bakiga tazama ba take takira tasallah a waya.

Shamsu yace Ummi kiyi hakuri kinji tace bakomai Yaya karkadamu kanka komi yayi farko zaiyi karshe in sha Allah yace hakane nagode sosai naturamiki kudi a account dinki tayi godiya sosai yatafi yabarta.. cikin ranta tace Inna Larai tana ganin kamar wani tayi mugunta batasan danta take cutarwa ba, aini gara mai aski da Mai kudin da babu kwanciyar hankali..

Shamsu wurin aiki duk ya sukurkuce shin miye ya kaishi janye Auren Ummi gashi yanzu yana danasanin hakan a lokacin da babu mafita yana cikin office har abokin aikin shi ya buga kafa yace S Abubakar karage tunani shine solution..

Haleematu tadawo cikin makaranta exam zasu fara gadan gadan don Haka babu abinda tasa a gabanta sai karatu. Zaune take cikin library tana karatu don ranan Hashim Ilyas da Hamza duk sun fita daga school yin wani abu kwatsam saiga Sunusi da Abokin shi Sagir suna zuwa sukayi sallama ta amsa bata ko kallesu ba. Sunusi yafara da Yan mata wurinki nazo kidan ara min mintoci bazan batamiki lokaci ba tadago tace ina sauraronka ,yace yawwa dama bakomai bane nadade ina ganinki cikin school dinan kuma gaskiya nakamu da sonki sannan aurenki nike sonyi, tace toh nagode da soyayya matuka amma gaskiya kayi hakuri donkuwa an rigaka bayan haka haryayi tambaya anbashi ni kaga bakyau nema Akan nema don Allah Kayi hakuri 🙏 yamike yace tunda ba'a daura aure ba ai zan iya samun ki matsayin Mata ta kowani hali. Tamike tsaye a fusace tace toh shikenan tunda bakason gaskiya ta kwashe books dinta tayi gaba tabarshi da cixon yatsa. Sagir yace calm down mutumina kayi hakuri kamar yadda ta bukata, Sunusi yace bazan iya ba Sagir yau nakara kaunarta danayi magana da ita Sagir yace amma dole kayi hakuri. Bazan iya ba Sagir ita din dani tadace Sagir hmmm.m

Haleematu Where stories live. Discover now