Haleematu (19)

56 6 0
                                    

**Na: Reedahmz
**Page 19
Nifa bana ganin comment dinku kodai littafin Haleematu baya muku dadi bana gani vote shiru nikeji kamar anshuka dusa inajira daga gareku Nagode.

Rayuwa tayiwa Halimatu zafi haka dai tunda shamsuddeen dan inna larai yasa baki a batun makarantar ta inna larai bata kara cewa kartaje ba sai dai duk azaba tana mata sukuma Yan uwan Malam iro basa cewa komi saboda ta siye masu baki haka har Rabi'a tana Ss3 Umar ss2 lokacin ne Halimatu take ss1 Amira tana ss1 itama ayyukan gida sun karu a kanta abu daya bata zuwa talle yanzu sannan kowani hutu takanje Katsina don gaishe da iyayen mahaifiyarta suma can kullum furucinsu kiyi hakuri watarana sai labari nan take hakuri a makaranta kuwa kawayenta uku Ummusalma kabir juwairiyya Yusuf  da Sadiya Nasir dukkan su iyayensu nadashi dai dai gwargwado suna kuma ganin halin da kawarsu ke ciki Amman basu fasa kawance da ita ba saima kara jawota jiki sannan ko cikin makaranta suna ganin hantarar da Rabi'a da Umar suke mata bata cewa komi lokacin jarabawa tazo sai Yayansu Shamsu yace Rabi'a da Umar suyi jarabawa tare waec/neco da jamb in sunci shikenan Inna Larai da Baba Laraba sukace hakan yayi dayake tadawo gidan da zama ana haka lokacin jarabawa yazo Shamsuddeen yayi dawainiyar kudin jarabawa yaturo don anmishi transfer an maidashi Ibadan .

Halimatu zaune tana karatu bayan ta dora ruwan girkin dare saiga kawarta sadiya nasir tazo taje ta gaidasu inna larai tadawo waje wurin kawarta suka fara tace kinsan me Abbanmu yace idan wata shekara tazagayo a ss2 zamuyi jarabawa Halima tace haba yanzu tafiya zakuyi kubarni sadiya tace kika sani ko muci ko bazamu ci ba tace aa Allah yasa kuci tace Ameen barin wuce kar Magrib yayi naga kina aiki tace eh barin rakaki bakin zaure.

Haleematu Where stories live. Discover now