Haleematu (62)

34 1 0
                                    

**Na: Reedahmz**
*Haleematu 62*

Nishadi Sosai sukayi cikin gidan da kannen mijinta Wanda suka jawota a jiki rayuwarsu tayi matukar birgeta gwanin sha'awa daga kan iyayen zuwa Yayan tayi farin cikin samu surukai masu dattako da nagarta ana hakane wayar ta yayi Kara bayan tadaga taji Amira tace Inna tayi hatsari nan take Haleematu tasaki wayarta a kasa tana salati Nadiya tace minene kawai tafara hawaye tace step mom dina tayi accident Sorayah tace ohh ya rabbi sorry barin fadawa Abba Nadiya kuwa takira Imam a waya ta shaida mashi immediately suka dau hanyar Bauchi dasu Hajia Sumayya da Saifullah ...

Shamsu yana zaune wurin aiki umar ya buga mashi waya ya sanar dashi abinda ke faruwa kanshi ya rike gam maza maza ya nemi excuse yayi shirin tafiya gida yakira Mu'azzam wanda Jirgin su ya sauka a Lagos daga south Africa Bayan shafe watanni na course din shi dayaje ya fadamishi yace shima zaitaho Bauchi yau su hadu kawai don Umar yace anje dauko su da motar asibiti yace toh.. Shamsu bai dauki lokaci ba yadiro yawuce Teaching hospital nan ya samu kowa likita yafito yace toh sai dai suyi hakuri don dukkan su sun zubar da jini ita dayan ta cika itakuwa dayan rai a hannun Allah, Dr yace Ummi kawai shine a bakinta Shamsu yace Dr kabari mushiga nida wannan don Allah yace suje suna shiga sukaga yadda take kawai Haleematu batasan yaushe ta kankame Shamsu ba tana salati Inna Larai tana ki yafemin Ummi kiyafemin don Allah dakyar Haleematu tace nayafemiki duniya da lahira Inna Shamsu kayafemin yace Inna bakimin komi ba aka kira Umar Rabi'a da Amira da Baba Laraba,kawu Umar a cikin haka Inna Larai jini yaki tsayawa zokaga tashin hankali wurin Rabi'a da Amira da Ummi likita yace za'a shiga da ita tiyata..

Abdulhalim bai tsaya ko ina ba sai garin Katsina wurin wani abokin shi dayake kasuwanci Yana da shagon shi a kofar marusa gidan su yana wurin bayan yakirashi a waya suka gaisa ya zayyana mashi komi ya amshe shi hannu biyu haka iyayen Nafi'u suka amshe shi, Abdulhalim yace yanason ya fara business din takalma ne saboda yanada dan kudin shi a hannu sai Nafi'u yace aikuwa akwai mai gidana Kwana ki yake mani maganar Mahaifin shi yabude company na sarrafa fata zuwa abubuwa dayawa yana neman ma'aikata masu neman aiki harna tura Mubarak da Musa kasan sungama ND babu aiki, kaga sai in mishi Magana koh? Abdulhalim yace aikuwa danaji dadi wannan taimako Nafi'u Allah ya bar zumunci Amin..... Nafi'u yace kasan shi yakeda  MUSAWA KAFTAN COLLECTION Abdulhalim yace wow aikuwa ana maganar kayan shi haka sukayita hira har sukayi bacci akan Nafi'u zai bincika idan ogan nashi yana gari don yakai Abdulhalim wurin.

Alhamdulillah anfito da Inna Larai daga tiyata Shamsu yace da Hamza yadauki Matarshi sukoma Imam yace aa yayanmu a dai barta zuwa jibi, Shamsu yace aa kadai kawota jibin in sha Allah don yanzu kota zauna babu abinda zatayi yace toh shikenan dama already iyayen shi dasu Nadiya suntafi Haleematu tayi sallama dasu taceda Amira ta turo account number dinta karta fadawa Shamsu tace in sha Allah tayi sallama da kowa tasameshi a mota ya shiga suka nufi yimir hotel don su kwana su wuce Jos da safe in sha Allah.. bayan yakama masu daki sukayi sallah yayi masu oda din abinci suka ci sukayi shirin kwanciya gashi basu zo da kaya ba tadai rage kayan tabar vest ne datasa cikin material iya gwiwa ta kwanta shikuwa da boxer sai singlet suna kwance yace kinga ikon Allah ko? Yanzu idan ba tsautsayi ba inda akace ankwaso su miya kaita wurin, Haleematu tace uhmm Habibina Allah sa muyi kyakkyawan karshe amma matarnan ta cutar dani don ko bance Allah ya sakamin ba zata ganin masifa... Imam yace share my life yafara lalubota yana neman bakinta ba abinda yakeso face yaji wannan dadin dayaji jia, itakuwa tafara mashi nagiya yace karkidamu slowly kinji a hankali yake sarrafa dukkan ni gabobin jikinta yakashe mata jiki harta bada kai bori yahau sukayi wanka suka gangara bacci mai nauyi abinsu.

Washegari dasafe suka koma Jos akan sai bayan kwana uku zata dawo amma shi kam Hamza yazo ya duba jikin..

Inna Larai numfashi takeyi Amma jikam ba dadi Rabi'a kusa nakuda ne yakamata bayan isowar Mu'azzam Amman shiru bata haihu ba saifama take har akayi tunanin ayi mata aiki Mu'azzam yace eh ya amince yasa hannu za'a Shiga da ita aiki Allah kuma cikin ikon shi ya sauketa lafiya tasamu diya Mace sak Mu'azzam, murna wurin Baba Laraba ba'a magana haka su Umar da kowa akayi waya aka fadawa Haleematu itama tayi matukar farin ciki.

Husna duk abin duniya ya dameta tarasa wani irin ganganci takeyi a rayuwarta da tayi biyayya wa mahaifinta ta amshi Abdulhalim amma kuma ai shawarar su Sholy abin dubawa ne haka tayita sake sakenta dai tarasa inda zatasa kanta don damuwa haka mahaifiyarta tashigo tasameta.

Hamza zaune bakin gado suna Shirin komawa dubo Inna Larai damasu haihuwa Haleematu tace Habibi Imam yayi murmushi yace kinji yadda kika iya fadan sunan kuwa itama murmushi tayi tace uhmm yace yawwa zamuje kiyi E passport Abba yace zamutafi London daganan muje Spain saiki fadi kasa guda daya dakikeso muje tace Ethiopia yace shikenan idan Mungama sai mubiya Saudi muyi umra batasan yaushe ta rungume shi ba don murna tayi ta zuba mashi addu'oi tace toh Habibi makaranta fa yace toh tunda strike yaki karewa dama inada niyyar nema maki admission a can wajen in sha Allah kuka Kawai tasa don murna ya rarrasheta suka fito sukaje gaishe da su Alh Inna yadauki 200k yace takaiwa masu jinya ko za'a bukaci wani abu tayi godiya tareda addu'oi na nasara Alh Inna yace Allah ya maki Albarka diyata Amin Abba Haj Sumayya tayi masu fatan Allah ya kaisu lafiya basu tsaya ko Ina ba sai Bauchi daga isowa direct aisibiti suka wuce jiki dai ba dadi shikuwa Mu'azzam yayiwa diyarshi huduba da Haleematu Sadiya yayiwa Ummi takwara Ummi Kamar ta hadiye Baby don murna. Baba Laraba tace hakan dakayi shine daidai bazan hanaka ba Mu'azzam yayi godiya sosai Rabi'a ma tayi farin ciki da hakan.

Abdulhalim zaune gefen Nafi'u suka kira uban gidan shi suka gaisa yace Mai gida dama Abokina ne yake neman aiki yazo daga Bauchi ya zayyana mashi Komi sai Maigida yacewa Nafi'u suzo Nanda minti talatin farin ciki wurin Nafi'u ba'a magana ya shaidawa Abdulhalim yadda akayi suka debe jiki don zuwa GRA layout dayake mai gadi yasan Nafi'u basu sha wahala ba. Bayan sun shiga sun zauna wurin minti goma sai gashi yafito Abdulhalim yadauka zaiga wani babban mutum kawai yaga matashi Nafi'u yace gashinan, bayan ya zauna suka gaisa yace Alh Nafi'u nawa toh ya sunan Abokin naka? Yace Abdulhalim Masha Allah Nafi'u yace Abdulhalim wannan shine maigida na danike baka labari Boss Mikel Musawa Abdulhalim yadago yace Barka dai Mikel yace kai cikin shock duk sukayi mamaki! Mikel yace don Allah kanada dangi a Bauchi ne? Abdulhalim yace eh to kusan Mikel yace kasan akwai wata Amaryas Abokina damukayi biki kwanan nan wallahi kaida ita kamar an tsaga Kara barika ga hoton su yadauki hotonsu yabawa Nafi'u duk saida mamaki takama su don kamar dasuka gani Mikel yakira Imam bugu biyu yace ango kana sha'aninka wallahi wani nagani maikama da matarka kamar twins, Imam yace ikon Allah toh turo manashi a hoto don muna Bauchi yadikon Wifey ba lafiya, Ayya sorry inji Mikel Allah bata lafiya a gaida madam suka aje waya.

Cikin Ikon Allah Inna Larai tafara samun canji Shamsu gabadaya ya rame kawu Umar yace ka natsu kadaina dorawa kanka damuwar datafi karfin kanka yace in sha Allah. yamike don zuwa siyowa wasu abubuwa yana sauri suka bige juna Jakarta ya fadi a kasa tadago!

Haleematu Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang