Haleematu (66)

32 3 1
                                    

**Na Reedahmz**
*Haleematu 66*

Alh mustapha yace shigo mana Abdul kayi mamaki ko Abdulhalim yashigo cikin sanyi ya nemi wuri ya zauna yace Abba kayi hakuri kayafemin nima bada son Raina hakan yafaru sai bisa wani dalili na fita neman inda iyayena suke ne don maganar danaji Hajia da Husna sunayi akaina saboda Magana ta Aure dakace zaka hadamu shiyasa.

Alh mustapha yace Abdul kawuce riko a hannu na kai dane miyasa maganar su zaisa kabar gida? Amma inason kasani yau zanfadama yadda kazo hanuna, kasan banida da Namiji toh watarana nafito Kano daf zuwa Shiga na Bauchi na tarar dawani accident daya rikitani nan na tsaya aka duba har ambulance tazo takwashesu kafin nan na gangara donyi fitsari kwatsam na ganka kwance hannuka na jini da kafarka, nataba ka baka motsi Amma kuma kana numfashi dasauri nadauke ka nasa a motata na shigo gari nayi emergency dakai, namasu bayanin komi tunda sun sani niba boyeyye bane nan akayi maka treatment nasa bincike wurin gano inda iyayenka suke, Amma shiru Babu wani labari..

Haka tun ina cikiya harna hakura nadauka Kai din dana ne kawai shiyasa naso hadaka Aure da diyata Husna, kwatsam bayan tafiyarka nasake sa cikiya bayan kwana uku saiga wani dattijo yazo yace dani yaga wannan sanarwa gidan TV kuma yayi Mashi Kama da wani dansu daya bace shekara kusan ashirin da wani abu shine shima yace bari yazo tawurina na tambaya ya danshi yake lokacin dayake yaro? Sai ya dauko hoto daya taho dashi naka kana yaro yabani Ina gani nace tabbas kaine, yace don Allah inhadaku nace zancigaba da bincike duk randa nasamoka zan nemeshi.

Sannan lokacin daka farfado a asibiti na tambayi sunanka kace Abdulhalim sannan shi Wanda yazo yace shi Yayan babanka ne kuma kai din twins ne yayarka ita Mace ce sunanta Haleematu Ummi zumburr Haleematu tamike Imam yace tabbas Baba ga twins dinshi kuwa don haka sunanta yake kuka suka sa ita dashi Saboda murna nan ne su mikel sukace Ashe ku Yan biyu ne ma shiyasa Kamar tayi yawa..

Nan aka kiran kawu Umar aka shaida mashi Komi yayi Farin ciki ya sanar dasu Baba Laraba kowa da kowa.

Haleematu daki tayi takira Shamsu bayan sun gaisa take fada mashi yau ansamu twin brother dinta fa gasu suna tare ta warware mashi komi nan ya tayata murna yace idan yasamu lokaci zaizo in sha Allah don su hadu da juna.

A falo Kowa ya hallara sai mamaki suke Alh mustapha yace toh yanzu Abdulhalim ya maganar Husna fa ? Abdulhalim yace Abba aidama da din na amsa ne don biyayya Amman Husna tanada wanda takeso a cikin ranta itama biyayya kawai tayi a baya shiyasa baka fahimci inda ta dosa ba don haka Abba Husna Yar uwata ce bazan so in rabata da abinda takeso ba. Husna sai hawaye take saboda batasan makomarta a zuciar wanda take son ba kartayi biyu babu fa babu wan babu kanin!

Alh Inna yace toh shikenan indai har hakane kayi tunani mekyau Allah ya maka Albarka duk sukace Amin sannan Alh Inna yace toh ni zanbaka Mata a gidanan yadda aka dauko yayarka kaima saika dauki kanwar shi, duk sukayi dariya Alh mustapha yace wannan gaskiya ne su Hajia sukace tsarin yayi.

Alh Inna yace Zaid yakira Sorayah tana zuwa Alh Inna yace toh kinsan komi na rayuwa na zuwa da kaddara don haka inason shaida maki cewa nayi maki miji dafatan zaki karbi wannan kyauta, cikin natsuwa tace Bakomai nagode da wannan zabin alkhairi.

Alh mustapha yace toh Allah ya maki Albarka sannan bawani bane illa Abdulhalim dasauri tamike ta bar falon cikin farin ciki dama dazu data ganshi taga yabirgeta Ashe ma yana gab da zama mijinta Alhamdulillah tace godiya ga Allah.

Bayan komi ya lafiya washegari duk sukayi shirin komawa zuwa karshen wata don suyi taro gabadaya shine time din tafiyar Haleematu da Hamza.

Sarah white ce takira tace ke Haleematu tace kawata miye duniya Amarya bakya laifi murmushi kawai Haleematu tayi tace kinki zuwa Sarah Kuma karshen wata Zamu wuce Haleematu tace uhmm zanzo dole ai ...

Sarah white tace inada gulma dazan baki daria Haleematu tayi tace baki raboda rigima sukayi dariya takashe wayar ta ajiye gefenta tana farin ciki sosai..


Haleematu Where stories live. Discover now