Haleematu (51)

32 2 0
                                    

***Na: Reedahmz***
***51***

Shamsu yace Ummi! Cikin tsawa ta farga ashe bai fita dakin ba lallai Hamza ya kama zuciar ta... Yazo daf da ita ya fizge wayar yace uban wa yabaki daman soyayya? Dawani dan iska kike cewa kina sonshi ashe bakida kunya ? Tace Yaya Hamza ba dan iska bane shut up! Tayi shiru to daga yau bake ba waya,tace Kayi hakuri Yaya don Allah yace nagama magana yadannawa wayar switch off... Duk wannan badakalar kunnen Hamza, Inna larai ta leko wai miye yake faruwa ne nikejin hayaniya?

Baba laraba tace uba na miyafaru yace wannan yarinyar tanason jamana magana wai jinayi tana magana da wani dan iska a waya fa Inna larai tace hmmmmm ai da kadauka ba ruwanta ko? Dama lumbu lumbu ce munafika tasha a nono, Baba laraba tace ahir dinki bazaki dauko mana abin kunya ba sukayi mata tatas tasha kukanta tace gobe zata koma kawai abinta.

Mu'azzam ango anata cin Amaarci ba'a ko jin kansu Rabia kuma ansamu duniya anbude faifan rashin mutunci.

Hamza yayi shiru yace to wai miye laifi don takula saurayi su zasu aure ta ne? Allah ya kyauta yayita kiran wayar akashe ai bashiri yafara shirin komawa.

Washegari Haleematu tashirya tsaf Shamsu yazo yabata kudin Komi don shima zaikoma osun da yamma Inna larai tace toh kai kafada mata idan aure takeso ta turo yaron don bamaso tajamana abin kunya yawwa! Baba laraba tace wannan gaskiya ne Shamsu yace toh ai tanaji, Inna larai tace ai kamar tafi tsoronka ne.

Shamsu yace toh zanyi bincike dai Inna larai ta cafke wani bincike ai itasan cewa yanada hankali yasa ta amince mashi Wai shin a ina yake nema? Tace a Zaria muna makaranta daya amma dan mangu ne hmmmmm Shamsu yace toh zanyi bincike akai.

Amira tafito da kayanta itama zatayi Katsina Shamsu ya bata nata kudin ta tafi Haleematu tace toh Inna nabarku lafiya ko kallo bata ishesu ba Inna larai a zuciarta cewa take Allah sa kiyi hatsari ki mutu irin na uwarki... Wai wannan cousin din Baban ta kenan fa amma tadauki kishin data keyi da uwarta ta mayar kan yarinya Mata muji tsoron Allah karmuce don bamu ne muka haifesu ba muci zalinsu uwa uba Marayu....

Hamza yana dawowa school yatafi shago daya bude domin aski yashare tas don fara aiki. Haleematu kuwa bayan isowarta Zaria dama Shamsu ya bata wayar yaja Mata kunne sosai tahau adaidaita zuwa gida tashiga side dinta ta ajiye kaya.

Tadauko wayarta ta bude sakkoni Kala Kala suka shigo na Hamza saikuma white.

Tadauki waya takira layin shi bugu biyu yadaga yana murmushi kamar tana ganin shi tace tuba nike yace karkidamu naji komi zanzo da daddare in sha Allah sai mu tattauna koh? Tace Allah ya kaimu Aamin sukayi sallama..

Shamsu yakama hanya zuwa airport don wucewa osun yana zaune jiran time Haleematu takirashi tace ta isa lfy lau.

Inna Larai da yamma takama hanya zuwa gidan tasallah tace Baba Laraba tazauna gida daf gidan tasallah mota yabige Inna Larai....

Haleematu Where stories live. Discover now