Haleematu [18]

50 6 0
                                    

Na: Reedahmz
Page [17]
Mota takama da wuta sosai tana ci dakyar aka kawo taimakon gaggawa akayi dasu Babban asibiti rai a hannun Allah cikin jami'an tsaro wani yaga wayar malam iro cikin ciyayi yadauka yakira lamba daya gani last ta Baba Laraba ce yafadamata halin da ake ciki tayi salati tace tana zuwa yanzu.

Bayan nan akayi dasu dakin yan hatsari Malam iro dai babu inda yake haka Halimatu ta suma Amman ba'a ga Abdul dan uwan ta ba Amina kuwa tabugi kirjinta sosai batasan halin datake ba anata kokarin basu taimakon gaggawa Malam iro yacika daidai lokacin da Baba Laraba da Inna Larai suka shigo asibitin sun iso akace dasu yacika nan suka zube sai kuka ba'a fi minti biyar ba akace Amina ta rasu sukayi ta kuka akace suyi hakuri Amman akwai diya datana nan sukace babu karamin yaro kusan sa'ar diyar sukace aa wannan kawai aka kawo daga hanya nan dai akafadawa yan da abokan arzikin Malam iro da yanuwan Amina sukazo aka gama komi akai kaisu makwancin su akabar marainiyar Allah Halimatu inda akayi ta fama da Yan uwa akan bazatabi dangin mahaifiyarta ba zuwa katsina dole tazauna gidan mahaifinta wurin Inna Larai da Baba Laraba tana kuka sukayi tafiyarsu suka barta da kewa tun bata da wayo.

Rayuwa Halimatu tafara ganin yanayin canji wurin Inna Larai tun tana da shekara biyar hantara zagi kai in yakama harda duka babu mai hana Larai saboda zalunci abinci kuwa saita sa mata kadan kota koshi ko oho.

Haleematu Where stories live. Discover now