Haleematu (10)

71 4 0
                                    

**Na:Reedahmz
**Page 10

Bayan Auran Malam iro da Amina mahaifiyar haleematu da kusan watanni Allah yabawa Inna larai ciki tana ta fice fice iri da kala batasan cewa Amarya Amina tana dauke da juna biyu ba ita gadarar ta an auro juya cikin ikon Allah cikin inna larai yana girma haka na Amina farin cikin wurin malam iro ba'a cewa komi lokacin da cikin Amina yakai wata biyar Ita kuma larai nata wata hudu nan ta farga tafara yada magana wai anshigo gidan Dan uwanta da cikin shege har Baba laraba tazo suka yabawa Amina magana Amman bata tanka musu saidai kuka dakyar Malam iro yataka masu birki har kanwartashi duk da haka dai anayi mata kasa kasa cikin ikon Allah lokacin haihuwa yazowa Amina Malam iro baya gida inna larai kuma taki taimakawa kuma taki fadawa koda makota ne har Allah yayi tasauka lafiya yarinyar tana fadowa da kuka yayi daidai da shigowar Malam iro yashiga dakin dasauri tanata hakki yayi maza yasa aka kira tasallah ungozoma tazo ta gyara jaririya can sai wani murdawan cikin ashe yan biyu ne nan tasake tayata saiga sanbalelen Yaro yadiro Malam iro yayi kabbara nan sai Inna larai ta leko taga Yan biyu aikuwa sai bakin ciki karara a fuskarta tajuya ko sannu batace da Amina ba nan da Malam yaje yanemo mota taxi aka tafi da Amina asibiti da yaranta aka dubasu aka bata magunguna bayan karin ruwa leda uku da jini daya don ta zubar da jini kwananta biyu aka sallamota Baba Laraba tazo barka fuska ba yabo ba fallasa malam iro kullum sai yayo wa Amina cefane maikyau nadaban yan uwanta sunzo daga Katsina Shiyasa bata sha wahala ba har ranan suna Malam iro ya yanka Manyan Raguna biyu Baba Laraba tace ai macen da tinkiya aka yankamata.

Haleematu Where stories live. Discover now