Haleematu (59)

34 2 1
                                    

***Na: Reedahmz
***59***

Alh mustapha yace Abdulhalim ni yanzu ban isheka ba saika tafi neman iyaye a irin Wannan yanayi da ake ciki suka koma dinning yace to Abdulhalim yatafi nemo iyayen shi saboda wasu dalilai wanda shi yabarwa kanshi, sannan Husna kiyi hakuri yace idan kinsamu Miji nitsatsse to ki aureshi ta sunkuyar dakai kamar irin tana jimamin nan Hajia tace kiyi hakuri Amman Abdul Miyasa zaiyi haka Alh Mustapha yatashi kawai yabarsu, suka fashe da dariya Mara sauti sukayi break suka gama takoma dakinta takira su Sholy tafada masu komi sukace kinhuta yanzu ai tayi dariya tace tagode.

Imam yadiro gida don karasa shirin Auren shi wanda yazo yaga gida a ciki da Yan uwa da abokan arziki na nesa duk sunzo duk wani lefe anhada shi tsaf yaji su Nadia sune a gaba wurin kai Kaya sai murna suke Sorayah tace munada shagali anbuga katuna na ban mamaki anata rabawa don shagulgulan biki Imam yawuce side din shi yakira Nadia a waya yace takula sosai idan sunkai kayan kuma a rufesu da security tace angama bro yace yawwa Besty tayi murmushi tace wai Ina mutumin ne bazai duro bane Imam ya fashe da dariya yace dolen shi.

Haleematu a garin Bauchi gidan kawu Umar da kawayenta Sara White, Safina Mashi, Aysha ingawa, Rahama kiyawa, Helena Numan dakuma manyan Aminanta na yaranta (Ummusalma Kabir Juwariyya Yusuf dakuma Sadiya Nasir) Anata shewa suna tsokanarta wai zasu zo shagon aski tayi murmushi tace duk kuzo a maku sallamar Amira tace Ummi Yaya yace yana zaure zakuyi magana, tace toh tamike tabar Amira da kawayenta tasameshi a zaure a tabarma suka gaisa ya mata nasiha sosai idon shi toshe cikin bakin glasses tayi godiya tana kuka yace munyi waya da Hamza yace Yan uwan shi zasu zo tashi kije yayi saurin fita..

Husna tana zaune takira Sholy da Sofy tace dasu akwai biki dazasuje a Jos fa yaron Abokin Babansu ne tace kunsan ba'a Nigeria yayi karatu ba bamuma taba haduwa ba duk da Ina zuwa gidansu suka ce toh shikenan nan tacewa Hajiarta zasu fara gaba dasu Sofy a fara event dasu tace toh shikenan a fadawa driver suka zo gida suka sameta suka dau hanyar Jos biki daya cika gari gabadaya Dan masu hannun da shuni masu fada aji...

Hamza yaturawa Ilyas da Hashim IV na dinner yace suzo na cousin brother dinshi ne  Ilyas yace ikon Allah dama ashe wannan multi millionaire din Alh Inna Dan uwan su Hamza ne? Hashim yace may be fa halan dai yana dan masu aikace aikace ne, Sunusi capacity yace inda Dan uwan Baban shi ne aida yakamata mugani a jikin shi Sagir yace kukasani ko Alh Inna baya taimaka masu? Sunusi yace kai Sagiru Babana duk kudin shi Alh Inna uban gidan shi ne sannan Alh Inna yayi wa bare alkhairi balle nashi suka ce shine ai baridai mukara kira Hamza yabamu bayani koda nashi Auren za'a dan rabashi, Hashim yakira yace mutumin waiko dakai za'a raba tunda da dagantaka Hamza ya washe baki yace sosai shiyasa nace kuzo ai to angama muna hanya.. Ilyas yace toh zamuje mugani kuwa Sunusi yace gaskiya don lallai zaiji kunya harna tausaya mashi shiga jama'a nan suka hau shiri sai Jos..

Karfe 12 din Rana masu kawo lefe suka iso Manyan motoci dasuke shiga layin yabawa Yan unguwar da kowa mamaki daidai kofar gidan malam iro Katagum yatsaya aka dinga fito da Kaya aka shiga dashi Inna Larai zabura tayi tace lafiya kodai batan Kai ne? Nadiya tace aa Banan bane gidansu Ummi Haleematu Amarya? Baba laraba tace e nan ne, nan fa labari yabaxa ko ina har Haleematu Sorayah tace Ina Amarya akace tana gidan kawunta Manyan sukace toh idan anyi laasar zamutafi da Amarya nan aka bude komi na kaya Inna Larai sai Eh hakane komi yayi duk tabi ta rude, aka kwashi kaya zuwa gidan kawu Umar duka komi da jama'a.

Inna Larai tace Ikon Allah uhmmm toh Masha Allah Baba Laraba tace lallai yarinyar ta shammace mu kuma fa hala haya yayi idan Kuma bahaka bane saina warware komi. Gabadaya hankalin su yatashi harta Rabia cewa take Inna Anya gidanan akace kuwa? Inna Larai tace humm kiran mu Yayanku a waya yazo tace toh, takirashi ya shigo ya zauna Baba Laraba tace Sayyadi shin kaga kaya da mutanen dasuka zo? Yace nagani kuma Ina Mamakin dagaske Hamza askin kadai yake kuwa? Inna Larai tace shiyasa nace kazo in tambaya ai Shamsu yace Mama halan yanada dalilin boye kanshi Amman nakira shi yace eh kayan Haleematu ne nikam namata murna ai Inna Larai tace toh jeka yamike yayi ficewarshi.

Kawu Umar yayi mamaki matuka sannan  yakara kiran Haleematu tace kawu bansan komi ba yadda kagani haka nagani yace to Alhamdulillah lallai kindace in sha Allah yamata nasiha sosai tayi godiya bayan tabar wurin shi Hamza yakira ta a waya yace Sultanatou Qalbee tayi shiru yakara kiranta tace Habibi wasu kaya nagani ina kasamu kudi yace nadade ina tarawa harda wani tallafi dana taba samu yasa kuma ai ina noma fa tace uhmm na rashin yarda yace idan akwai abinda za'a kara kiyi magana tace Babu yace toh barinje inada baki tace to ka kula da kanka yace kema in sha Allah.

Nadiya da Sorayah sukace a nuna masu Amarya Zainab kanwar Mu'azzam itace takaisu dakin da Haleematu take suka zauna Haleematu tadago suka gaisa sukace sune suka kawo kaya tayi murmushi suka mike suka koma dakin da aka ajiye masu komai Sorayah tace Masha Allah nan dai kafin tafiya da Amarya akayi karamin liyafa da Kowa a unguwar yayi ta mamaki.

Mota guda uku aka ware wa dangin Haleematu da mutanen Katsina don tafiya Jos mamaki baigama kama Inna Larai Baba Laraba dasu tasallah ba saida suka doshi gidan iyayen ango Inna Larai cikinta kuka kawai yakeyi Baba Laraba na cewa kodai gidan yankan kai aka kawo mune Rabia tace hmmm wayasanine wannan abun mamaki.. aka shiga gida ga dangi sai guda ake tayi aka tarbesu ita kanta Haleematu tana mamaki...

Haleematu Where stories live. Discover now