Haleematu (15)

74 5 0
                                    

*Na:Reedahmz
**Page 15

Malam iro yakama hanyar komawa Bauchi lafiya lau yasamu mota ya isa yaje gida yayi sallama Inna Larai ta amsa baya bo ba fallasa yara suka yi Mashi barka da dawowa yazauna yace da Larai nasameku lafiya ya yaran tace Alhamdulillah yatashi yatafi dakinshi yacire kayan jikinshi yawuce wanka kafin yafito inna larai takawo mashi fara da mai yana fitowa yabude yagani ya girgiza kai yabude kwanon sha ruwan sanyi na randa yahau cin abinci a hankali yana tunanin hali irin na Larai sam badadi bakamar Amina ba.

Kafin yagama saiga ta shigo tazauna gefen tabarma tace Malam dama ina da magana nace barin bari saikaci abinci yace inajinki dabaka nan naci bashin dubu uku don cefane nace inka dawo zamu biya yadubeta yace Larai ashe bazaki canza ba aina barmaku komi yaushe har takai ga saikin ci bashi Wato bakya tsoron Allah ko ta tura baki tace oho nidai kabani yafito da kudi ya kirga yabata ta tashi fuuuu ba sannu nagode tayi waje.

Haleematu Where stories live. Discover now