Haleematu (17)

68 5 0
                                    

Na: Reedahmz
Page 17
Dasafe malam iro yatashi ya shirya tsaf don tafiya katsina dauko su Amina da yara yace da inna larai zai wuce tace Allah yakiyaye hanya yace Amin yadau jakarshi ya fita yasamu mashin yakai shi tasha yasamu mota saura Mutum daya shikenan yabiya yazauna yayi zugum bai hira da kowa harsuka isa Katsina lafiya ya isa gidan surukan nashi yara sunganshi sunata murna aka kawo mishi abinci yaci yahuta Amina tazo suka sake sabon gaisuwa ta tambayi yara da mutanen gida yace kowa yana lfy yace gobe da safe in sha Allah sammako zamuyi don mu isa da wuri tace Allah ya kaimu nan sukayi ta hira har dare ya raba yace taje ta kwanta Asuba nayi tahada wuta tadora masu ruwan wanka suka shirya tsaff don tafiya Amina ta rungumi mamanta sosai tana kuka aka fito gabadaya don yi musu sallama Baba yakara musu nasiha suka dau hanyar tasha sun sami mota saura seat uku sunfara tafiya kenan sai malam iro yace Amina wallahi ina tausayawa rayuwar yaya na idan babu ni tace Malam kadaina irin wannan magana don Allah kana sa jikina sanyi yace toh aidole ne sai dai muyita addu'a ta samun sauki tana gama rufe bakinta yashare hawayen daya zubo mishi sun iso kano lfy suka hau motar bauchi daganan bacci yadauketa yara ma sunayi Malam iro ne kawai yaketa tunani kwatsam sunzo Durun sunkusa shiga Bauchi motar su ta hadu da wata sukafara salati Amina tafarka tana ta salati motar tasu takama da wuta.

Haleematu Where stories live. Discover now