Haleematu (49)

35 3 2
                                    

***Na: Reedahmz***
***49***

Alh Muhammad Inna Zaune bisa shimfida yana shan shayi gefen shi Hajia Sumayya ne sai Nadia,Saifullah,sorayah,Ramadan Zaidu, Khalid, Marwan da fauza suna breakfast Alh Inna yace wai kunyi waya da yaronan kuwa? Hajia Sumayya tace eh zaizo cikin satinan in sha Allah.

Nadia tace Abba ni wai Yaya bazaiyi aurenan bane? Alh Inna yayi dariya yace kinason yadawo ya lallasaki ko sukayi dariya Duka.. Hajia Sumayya tace aibai isa tabamin diya ba Alh yayi dariya kawai Saboda ba abinda yafi mashi dadi irin zama da iyalin shi.

Ramadan yadauki waya yakira Yayan su yana dagawa yace ya Imam kana hanya yace ehh zankira ku anjima in sha Allah ya katse wayar yace wai Yana hanya sukace Allah ya kawoshi lafiya.

Alh M Inna Haiffen garin plateau (Jos) ne Kuma multi millionaire nakin karawa, duk kasa an sanshi kuma shi ba dan siyasa bane. Yana harkan duwatsu tun yana matashin saurayi..

Baya zama kuma harka ta karbeshi sosai Kuma yana kyautata wa marasa karfi a karshin foundation din shi mai suna (Innah Foundation) wanda ke karkashin jagoranci Babban Dan shi Imam da Kuma Nadiya.

Sallama sukaji Marwan ke game yayi ihu Yaya is back kowa yafito..

Haleematu tarasa abinda ke mata dadi don abinda taji bamai faduwa bane don babu wanda zai yarda da ita, kawai tace a ranta tabarwa zuciar ta ita kadai zatayi wannan yaki Zata roki Allah ya bata sa'a.

Inna larai ansha kwalliyya don yau ake daura aure uwar Ango sai kallo da abinda akace daidai ne batada katabus hakan kuwa ba karamin dadi yayiwa Haleematu ba don tasan asirin yakamata dakyau.

Mu'azzam farin ciki fal fuskar shi shida Shamsu da sauran abokai aka cigaba da shagali .

Anyi biki angama yakama gida madaidaici a Bauchi unguwan sarakuna tunda itama zata koma School.

Kiran wayar yashigo dasauri tafita daga cikin gidan don samun privacy Hamza ne bayan sun gaisa yace ya biki dakowa tace Alhamdulillah yanaka yace dazu nakoma gida ai tace Sannu da gajia, ya amsa cikin fara'a sukayi hira sosai tace sotake a koma tayi missing dinsu course mate.

Yace soon ai yasu Mama da Abba yace lafiya lau suke kinsan zanfara masu maganar ki dawuri saboda sufara shiri, kinsan ance mai kwarmin ido dawuri yake fara kuka tayi dariya tace hakane kam Allah yabamu arziki mai amfani yace Amin toh dama Sundade suna tambaya ke Ummi! tsawan Shamsu taji batasan yaushe wayar ya subuce ba....

Haleematu Where stories live. Discover now