Haleematu (52)

30 1 1
                                    

***Na: Reedahmz
***52***

Hon Mustapha Annur yana karanta jarida ta punch Husna ta durkusa har kasa ta gaishe dashi yace uwata Kenan Alhamdulillah tunda an kamalla lafiya ai haka akeso, tace Baba nagode tamike zatayi ciki yace zauna inason in maki wata magana, tace inajinka Baba. Yace nikam akwai wanda kika tsayar kina so ne???

Gabanta yafadi tace um um Babu yanzu yadago sannan yace toh tunda Babu ni namaki miji dasauri tadago idonta tana kallon shi yace yes, amma karki damu banmiki zaben tumun dare ba, itadai ta kosa taji waye yace ai  Abdulhalim  ne what yace haka nace...

Tace toh Baba nagode sosai Allah ya bamu ikon cigaba da maka biyayya yace Amin Allah ya miki Albarka Amin

Tana Shiga dakin mamanta tafada kan gado tace Mama kinji me Baba yace Hajia saude tace ai yamin maganar Kuma hakan ne daidai ai Mama sa'a na fa ko ince na girme shi tace Koma yaya ne kiyi addu'a ta fatan alkhairi kawai shikenan mama.

Shamsu zaune wurin aiki yarasa mike mashi dadi gabadaya baya gane kanshi kuma idan yatashi wurin azkar ko nafila sai yaji duk baya iyawa jikin shi yamashi nauyi sosai amma yanata Addu'oi dai don samun sauki..

Haleematu tagama girkinta tsaf Hamza yazo yakirata a waya tafita kofar gidansu suka zaune a gefe suka gaisa tace inkawo maka indomie yace aa ya koshi Ina Ilyas da Hashim yace suna daki nabarsu yanzu saboda zamuyi tattaunawa ta sirri yasa nataho ni kadai, tace hakan ma yayi kyau yace bani labarinki tace tohm... Nan ta shaida mashi bata boye mashi yace in sha Allah zanshare maki hawayenki tace nagode sosai Allah ya tabbatar mana da alkhairi Habibi yayi dariya yace amma fa kinsan ni talaka ne iyaye na basuda komi kina ganin za'a bani ke? Haleematu tace ai Yadda Inna Larai batason naji dadi ai da gudu zata yarda, bata san ni samunka da kyawawan halayyarka nike so ba.

Hamza yace kidai kara hakuri dani tace please kadaina cewa haka in sha Allah lokaci kankani zaka samu budi ninki ninki yayi murmushi yace Allah ya amsa Habibty barin wuce koh ha fruit nazo maki dashi ta karba sukayi sallama tana godiya...

Tana shiga daki White taxo tazauna suna hira White tace amma dai kina ganin Hamza zai iya aurenki yanzu kuwa? Haleematu tace in sha Allah Ina mashi fata maikyau, White tace Ina tayaki don gayen yayi ta ko ina kawai matsalar talauci shima Kuma Allah ya fidda shi Amin cewar Haleematu.

Ilyas yace amma ka gamsu za'a baka ita yace sosai Hashim yace Allah ya tabbatar Amin inazuwa cewar Hamza.. Hashim yace wallahi Hamza na kokari wurin neman na kai Ilyas yace ga iyaye yanzu ga school sai godiya kawai. Abokin su Sunusi capacity yashigo irin Yayan manya shagwababbu sai wasa da kudi suka gaisa yace Ina wancan uban girman kan Abokin naku? Sukace yafita just now Sunusi yace nifa naga wata sabuwar beb ta wurinku don ina sonta da aure Ilyasa yace toh wacece haka ne??

Haleematu Where stories live. Discover now