Haleematu (26)

57 5 0
                                    

**Na: Reedahmz
** page 26

Ya juya baya yace Mama akwai wacce nikeso wallahi kuma nayiwa zuciyata alkawarin aurenta matukar ba mutuwa tayi ba Baba Laraba tace karka fara ashe gida bai koshi ba yaya za'a kawai daji kasan mikake fada kuwa inna larai tace Aa Yaya Laraba kinsan alkawari yana da muhimmanci mubashi lokaci yajuyo yace nagode Baba Laraba tace a ina wacce kakeson take yace anan garin Amman kukara min lokaci kafin inkoma zan sanar maku sukace toh babu bakomi Allah ya maka albarka yace Ameen.

Baba Laraba tace toh ubana Kaifa ya sosa keya yace tana kusa zakuji in sha Allah Inna Larai tace ai shi wannan wacece zata so shi da wannan uban hadan ran mu'azzam yace aa inna gaskiya wacce tasameshi tayi nasara kuwa sukace Allah yakawo tagari dai duk suka Amsa da Ameen Inna Larai tayi kiran Haleematu don zuwa ta kwashe kayan dasuka gama cin abinci tana zuwa ta durkusa bisa gwiwoyinta tace gani kwashe kayan tace toh Shamsuddeen da Mu'azzam basu san lokacin da bakinsu ya furta tsaya in tayaki a tare ita kanta tayi mamakin faruwar hakan dasauri tamike gudun fadan Inna Larai nan mu'azzam ya kalli shamsuddeen shima kallon yamishi

Baba Laraba da Inna Larai kuwa sai abin ya kulle musu kai mike faruwa ne haka nan dai suka tashi domin tafiya makwancin su suka bar iyayensu anan suna jimami Larai mekike tunani akan yaranan da Haleematu tace abinda nikeso inyi tunani akai kenan Inna Larai tace toh ni bazai faru ba ma Baba Laraba tace ina kuwa Hmmmm kaji cin Amanar maraici kamar Haleematu ba jininsu ba karfa ku manta da Baba Laraba da Malam Iro marigayi Baban Haleematu Uwa daya Uba daya fa dakuma Baban Inna Larai da Baban Malam Iro wa da kanine kunga kuwa babu bare a cikinsu amman saboda tsanar mahaifiyar Haleematu yasa basa son diyar dan uwansu Allah karabamu da barin zumunci Ameen duniya kenan.

Haleematu Where stories live. Discover now