Haleematu (58)

38 2 1
                                    

***Na: Reedahmz
***58***

Inna Larai tace haka nike nufi akwai kanwarta idan kanaso, yace bakomai Baba zankara dawowa tace shikenan ya sunanka yace Sunusi toh Sannu Mal Sunusi Allah ya baka hakuri yace bakomi yakoma mota yadauko Yan dari biyar yabata tanata murna ta koma cikin gida ta rangada guda.

Sagir yace nafadama karmuzo ai kayi hakuri kaki Sunusi yace kawai sai gashi Allah ya nunamin iyakata, dama bata dace da Dan iska irina ba, Sagir yace ashe dai yanzu ka fahimta kake zagina da farko Sunusi yace yanzu nabari Allah yabamu ikon shiriya kafin mutuwa Amin don nabiyyi rahamati..

Shamsu yadiro gida don dubasu da kuma maganar bikin Haleematu duk yazo bayajin dadi sai da yawuce dakin shi ya kwanta kafin daga baya ya shiga cikin gida suka gaisa da Baba Laraba yashige dakin mahaifiyar shi suka gaisa yake tambayar ta abinda yadace tace ita tacire hannunta tuntuni fa..

Shamsu yace don Allah Inna karkiyi abinda zai rage maki qima, haba mi Babar yarinyar nan tamiki ne da kullum cikin azabtar da diyarta, Inna Larai tace Deeni matukar baka cire bakinka ba zan iya maka baki, Yaushe ka isa katasani a gaba Kamar diyarka, don Allah tashi kayi wajee.

Hamza yakira wayarta yace kiyi man kwatancen gani cikin garin Katsina tace wai are you serious nan tamishi kwatancen ta tashi tafara hada mashi abubuwa masu sauki na ci ta sanarwa Mal Usman da mama deeja sukayi farin ciki nan take Malam Usman yakira Abubakar da Hamza yayun Maman ta ya shaida masu zuwan Hamza nan akayi kara. Yana iso yasamu Hayatu a waje ya shigo dashi aka fara gaisuwa Malam Usman yamasu nasiha sukayi godiya kowa ya fita Haleematu tasake gaishe shi cikin ladabi ya amsa da murmushi yace Amarya bakya laifi tace uhmm yace kinga abu kamar wasa Koh? Tace haka niketa gani yace in sha Allah zancigaba da neman taimako muketa inda zamu zauna koh tace Allah ya baka iko Amin. Tasa mashi abinci yaci lokacin Sallah yayi yatafi yace yanada wasu abokai cikin garin Katsina zai duba su sai bayan Isha zaizo mata sallama zuwa masaukin daya kama..

Inna Larai tace da Baba Laraba ai fitar datayi dazu sa'a ce nan ta fede mata biri har wutsiya Baba Laraba tace gara dai basamu wancan bakar dagar ba.

Mama shema'u yayar Inna Larai Zaune da kawu Umar da kuma kawu Usman sunata shirya yadda zasu hada kudi su siyawa Haleematu abinda ya sawwaka don abin yazo masu kwatsam ne nan dai suka gama tattauna wa sukace washegari Inna Larai da Baba Laraba suzo duk da sun san halin

Alh Inna yagama komi na bikin Imam da Amarya wanda shi akejira Kawai yadawo a kamalla komai Saifullah yace Daddy yakamata katura su can London Kawai Nadia tace good idea Alh Inna yayi dariya kawai yace toh sannunku da tsari Hajia tace dole ace dasu sannu dazu munyi waya da Imam dinma yaje Lagos dubo wasu Kaya Duka kannen sukace Allah yadawo dashi lafiya.

Hamza yagama Shiri tsaf yazo kofar durbi don sallama da Haleematu don ita sai gobe zata koma yashiga ya ajiyewa Mama deeja da Malam Usman goma ta Arziki sukayi sallama da Haleematu yadauki dubu biyar yabata yace tayi hakuri,tace aida kabarshi tunda kana hanya yace aini da aboki na ne shima zaije Jos har mangu kizo ku gaisa tayi murmushi tace bansan ai tare kuke ba naga katon mota, Hamza yafashe da dariya yace muma zamuyi in sha Allah ta leka suka gaisa yace Abokina ne Tare mukayi karamar makaranta Sunan shi Mikel suka gaisa Mikel ya ciro dubu hamsin yace Amarya gashi ki rike tace aa Hamza bakomai ki amsa tayi godiya tabarsu tana Masu addu'a suka wuce.

Bayan takoma ciki ta nuna Alkhairin da abokin Hamza ya mata Malam Usman yace Alhamdulillah kinyi sa'ar miji kuma karkidamu da sana'a wataran zai mike don naga yanada zucia matuka tayi Masu godiya da shawarari.

Mikel yace hey guy miyasa ka boye mata identity dinka? Hamza yace saboda Ina nemar soyayya ta gaskiya ba jebu ba, Mikel yasake cewa yanzu ka amince da soyayya da ita wannan take maka? Yace Sosai kuwa Mikel yasake cewa eh gaskiya naga alamar hankali da ladabi a tare da ita Allah ya baku zaman lafiya Amin..

Husna zaune dasu Sholy da Sofy, Sholy tace amma fa wani hanzari ba gudu ba shin ansamo inda iyayen Abdul din suke ne? Husna tace Ko daya nifa tunanina kenan nadai amsawa daddy ne kawai Sofy tace to gaskiya hada zuria dashi hatsari ne suka fashe da dariya Sholy tace adinga kiran yayanki da yaran shege gara dai farka.... Kunji illar shawara da wasu kawayen ko bazasu taba baka shawara na gari ba sai dai gurguwa gashi dai tunda su basu samu ba suna Shirin jefa husna ruwa tayi sake reshe kama ganye..

Husna tasamu mahaifiyarta tace tazo da bayanin gaskiya bazata iya Auren Abdul ba yanxu Saboda ta tuna baida asali fa Mamanta tace toh aini naki maki magana akai ne saboda karki badani wurin Alh amma wani asali ne dashi tunda munan muka raine shi Ashe shi Alh ya aiko yakira Hajia yaji suna wannan zance kawai sai ya koma yace tana zuwa yaje side dinshi ta baya ya hade kayanshi tsafff a jaka guda biyu da duk abinda yasan zai bukata yakai mota Alh mustapha yace a Wannan kaya fa eh wanki zankai dasafe in sha Allah toh Allah ya kaimu..

Asuba yatafi massallaci yayi Sallah yadawo yashiga ya gaida Mutan gida yadauki key din motarshi wanda yasiya bai dade ba wurin 7 nasafe yafice baisan inda ya nufa ba..

Wurin 10 nasafe shine lokacin breakfast dinsu Alh yace Ahh Abdulhalim tunda yakai wanki baidawo ba ne ke Husna jeki kirashi tana zuwa side ta tura kofar dakin tajishi a bude dakin bakomi duk ya tattara dasauri tafito ta shaida masu suka nufi dakin dasauri duk hankali a tashe nan Alh mustapha yaci karo da farin takarda a gefen side bed dinshi yabude yafara karantawa yana innalillahi minake gani anan?

Haleematu Where stories live. Discover now