Haleematu (8)

95 7 1
                                    

*** Na:Reedahmz
*** Page 8
Tayi alwala ta gabatar da sallar La'asar dinta tayi addu'ointa na neman sauki takuma yi wa mahaifanta ta tashi tana nade sallayarta taji muryan yayanta yana kwala mata Kira Haleematu! Haleematu! Haleematu! Ta fito a firgice saboda irin yanayin kiran wato tallar ma har tasha kike zuwa ko daga yau nakashe talla a gidanan in kuma naganki sai na karyaki wuce kibani wuri tace dashi kayi hakuri yaya yawuce yabarta yashiga dakin mahaifiyarshi suka gaisa yace inna don girman Allah daga yau nasoke tallar yarinyar nan a gidanan ko nawane zandinga tura miki tunda ina aiki tace naji Allah yasa tana zuwa makarantar yace aa Inna harda laifinki shin bake kike sa sauran yaran sutafi ba ita miyasa bazaki bude mata ido ta tafi ba tace toh ubana kafadamin yadda zanyi baba laraba dake gefe bata ce komi ba don tasan sune suke hanata zuwa makaranta yatashi yace zai fita zuwa unguwa wurin wani abokinshi sukace Allah yadawo dashi lafiya yayi tafiyarsa haleematu tafito takama share tsakar gidan daga can taji yaro yana sallama wai ana sallama da Mai talla yace ace Adam ne tace kace dashi ina zuwa Inna larai tace tohh mekuma kika debo mana har gida tace aa dan gidan Alh Dikko ne na bayan layi bude baki baba laraba tayi tace meye hadinki dashi tace bakomi suka tabe baki don mamaki tawuce taje tasameshi tace yashigo zauren.

Haleematu Where stories live. Discover now