Haleematu (50)

38 3 1
                                    

***Na: Reedahmz***
***50***

Godiya ta mussaman gareku masoya masu bibiyar wannan littafin ku Kara hakuri in sha Allah za'a dinga posting yadda yadace. Nagode Sosai jinjina gareki (Binta Yusuf Ahmed) ❤️❤️❤️❤️ Nagode wannan shafin na sadaukar maki.

Hamza yaji mugun tsawa da Shamsu yayi itakuwa duk t firgigit ta sake wayarta a kasa!

Miye haka kikeyi duk cikin gida bai isheki waya ba saikin fito waje? Tace Yaya akwai hayaniya kuma anamin bayanin abu ne cikin haryanzu Yan biki basu gama tafiya ba.

Yace banson haka kiwuce ciki wannan ba mutunci bane tace toh tabarshi a wurin.

Tana shiga cikin gida Baba laraba tafara Ina kikaje tundazu ake nemanki tace ina waya a kofar gida Inna larai ta cafke maganar wayar ne a waje kifadi gaskiya dai..

Haleematu tace gaskiyar kenan nibanyi Karya ba Inna larai tace iyye wuyanki ya Isa yanka nikike mayarwa da magana cabdi!

Haleematu tawuce dakinta tabarsu bata bi takansu bama Kawai duk sukayi mamakinta Baba laraba tace ehh Lallai sai andage saura duka.

Alh m inna zaune cikin falo da iyalinshi Imam zaune gefen shi da mahaifiyar su ... Alh m inna yace Baba na ya business ya fama da jama'a da dawainiya?

Imam yace Daddy Alhamdulillah munata kokari.. Hajia Sumayya tace toh malam imamu duk suka sa dariya Saifullah yace Umma wallahi ke comedy ce wai Malam Nadia tace ehem ehem sorayah ta kalli Nadia tace sister karki sa Yaya bacin rai Imam ya kallesu yayi dariya yace zaku sani zaid yace uhmmm.. Hajia Sumayya tace toh ya Isa hakan yanzu ya maganar Aure? Yace Alhamdulillah nasamu tana karatu kuma gaskiya bafa Yar kowa bace...

Alh m inna da Hajia Sumayya sukace indai tanada tarbiyya ai shikenan Imam yace toh daddy..

Nadia tace congratulations big boss yace thank you small Lady suka fashe da dariya Ramadan Khalid da Marwan suka ce shikenan munsamu inda zamu na zuwa cin abinci.. Imam yace hummmmm bazan amsaku ba.

Gidan Alh m inna gida ne na yanci da mutunta juna koda wasa babu raini ga son haduwa ayita raha da juna..

Bayan kowa ya watse Haleematu sati ya zagayo zata koma School tanata murna ta shirya kominta tsaf Shamsu ya shigo yayita mata fada akan kawayen banza da abokan banza, tace in sha Allah Suna cikin magana wayarta tayi ruri tadauka Hamza ne sukayi magana ta dawowa ta manta Shamsu na nan kawai tace love you too!

Haleematu حيث تعيش القصص. اكتشف الآن