Haleematu (5)

103 6 0
                                    

**Na: Reedahmz
** Page 5

Tadauki kula tafita tana share hawaye kicibis sukayi dashi a zaure yana shigowa da Jakarsa a rataye fuskarnan a murtuke kamar an mishi mutuwa durkusawa tayi tace Ya shamsuddeen barka da sauka ya amsa ciki ciki saboda tsabar miskilanci irintashi tawuce yawuce ciki tajuyo tabishi da kallo tace shi wannan kullum fuska a daure kamar sa yana shiga akafara oyoyo yaya! Oyoyo yaya! Yadan yi murmushi kadan yace dasu sannunku ya naga bakutafi makaranta ba inna Larai tafito da murnarta don tarban Dan nata tace dashi shigo kahuta kabar yaranan yanzu suke shiryawa ja'irar nan ita tasasu makara yace to inna ita bata zuwa ne tace Dan nan ai yariyar nan taki karatu sai talla yayi shiru kanshi a kasa yana tunanin wani hukunci yadace yamata can Baba laraba ta fito daga bayi tana ahhh lale lale lale da mutanen ikko Sojana kadawo lafiya don haka take kiran Shamsu yafashe da dariya kamar bashi bane yashigo fuska a daure ba yace babata babata yana sameku tace lafiya Alhamdulillah ya aikinku yace sai godiya yadago yace da Baba laraba dama Ashe yarinyar nan taki makaranta tace eeeeey sayyadi wai sai talla munyi fadan har mungaji saikuma tasa kuka zaiyi magana saiyaji sallamar kanwartashi tashigo fusace yamike yana zare belt nima a guje nayi gefe don abin karya shafeni ina lekensu ta taga.....

Haleematu Dove le storie prendono vita. Scoprilo ora