Haleematu (39)

28 3 0
                                    

***Na: Reedahmz
***39

Malamar tace Ina zaki shiga tace nazo exams ne malamar taduba lokaci tace Amma sai yanzu zakizo saboda sakaci da wasa da lokaci tace don Allah kiyi hakuri wallahi akasi akasamu kitaimakeni tace zaki shiga amma anacewa kowa yatsaya zaki bari bazan Kara miki koda sakan daya bane tace nagode na Amince tashiga hall da addu'a tazauna tafara fa tanayi tana addu'a tazo part din karshe a English akace Time up kamar tayi kuka saboda takaici Amma saitace Allah kayimin zabin alkhairi Amin tayi submitting tafita takama hanyar gida don karma ace ta tsaya wani wurin dai

OSUN

HUSNA zaune shiru tana kallonsu su sunata surutu can Sholy tace ke duniyar tunanin wa kika shiga ne haka Husna tayi murmushi tace kekam aikinsan ba'a rasa nono a ruga Sofy yace kodai daren jiya ne tace shiyasa nikeson ki saboda daukar saiti Sholy tace toh yanzu yaya kenan tace zanbi komi a sannu kawai sukace ai shikenan ASMA'U (Husna) MUSTAPHA ANNUR kenan haifaffiyar garin Bauchi ce a wani LG da ake cewa Misau Babanta Dan siyasa ne don Sanata ne Husna tazo osun yin bautar kasa ne dayake ita taki fita waje tace tanaso yin karatun ta a gida Nigeria haka dayake tanada hanya tayi kokari garin data tafi bautar kasa ma da Aminanta guda biyu Zulaihat Tahir (Sholy) da Safiyya Aliyu (Soffy)  aka canza masu suka dawo osun Husna irin miskilan mutane ne da basu cika shiga hayaniya ba shiyasa wasu ke mata kallon Mai girman kai

HUSNA zaune shiru tana kallonsu su sunata surutu can Sholy tace ke duniyar tunanin wa kika shiga ne haka Husna tayi murmushi tace kekam aikinsan ba'a rasa nono a ruga Sofy yace kodai daren jiya ne tace shiyasa nikeson ki saboda daukar saiti Sholy ...

Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.

HUSNA MUSTAPHA ANNUR

Haleematu tadawo gida tasamu kaya jibge wai Inna Larai ta ajiye mata don wanki bayan ga Umar yana nan tace Inna banda lfy inajin zazzabi tace banson munafurci tace wallahi shikenan takyaleta tace ai gobe ma rana ce Haleematu tawuce kicin tadauko kwanon abinci ta taga kamar na yaro tace humm watarana sai labari gashi an hanata zuwa katsina taci Tasha ruwa ga kudi da Yaya yabata Amma ba damar kashewa gudun halinsu Inna Larai da Baba Laraba Amira tace gaskiya jamb Alhamdulillah yayi sauki Rabi'a tace zamuci in sha Allah Umar yace muyi addu'a dai Ummi tace nikam bansamu nagama page din English nakarshe bama lokaci yayi sai Rabi'a tace sakacin ne tace aiki natsaya yasa nayi latti Umar yace toh miyasa baki bari ba sai kindawo tace saboda Inna tace saina gama Amira tace cab aini saina dawo inyi Inna Larai tace toh karata kika kawo wurinsu kenan tace aa hira kawai mukeyi toh duk ku watse suka tashi takoma daki wurin Baba Laraba tace Nifa ko gaskiya zanje wurin tasallah takaini wurin wannan malamin nata don ni gaskiya haryanzu banason auren Shamsu da yarinyanan Baba Laraba tace ai nadauka dama kinyi sanyi ne tace ina mafita kawai nike nema Baba Laraba tace kawo kunnenki kiji abinda za'a yi.......

Haleematu Where stories live. Discover now