Haleematu (9)

111 11 0
                                    

**Na:Reedahmz
**Page 9

Haleematu Yarinyace yar shekara shabiyar da haihuwa an haifeta ne a garin a bauchi katagum mahaifinta malam Ibrahim Umar Wanda ake kira da iro katagum dan kasuwa ne a cikin garin bauchi wato a cikin kasuwar muda lawal yana sana'ar sai da kayan gwari yana samu dai dai gwargwado yadda iyalansa basa kukan yunwa Malam Iro su hudu mahaifinsu ya haifa da mahaifiyarsu maza uku Mace daya dama matarshi kenan baita ba auren wata ba Umar ne Babba sai iro sai maryam wato baba laraba sai autansu usman Baban su malam iro wato malam umar yanada kani Malam Sani Wanda shikuma yaransa biyu mata Shema'u da Alawiyya itace Inna larai wato itace aka hadata aure da yayanta iro Kafin auran Alawiyya da iro alawiyya ta taba auran wani yarasu yayanta biyu dashi malam habu wato Shamsuddeen da kanwarshi Rabi'a Bayan auranta da malam iro rikon yaranta yadawo hannun mijinta kuma yayanta malam iro saboda yanuwan malam habu marigayi mijinta basu da karfi. Bayan Auran Alawiyya da Malam Iro Bai dade ba Allah yabata haihuwan da namiji Akasamishi Umar sunan mahaifin malam iro kenan Umar yanada shekara biyu malam iro yahadu da mahaifiyar haleematu wato Aminatu Wanda ita bahaushiyace yar katsinawa Allah yahada jininsu suka kulla soyayya harta kai ga aure haka Inna larai dataji labari tadaga hankalinta sosai don batason kishiya shikuma malam iro yace ba fashi sai yayi bawanda ya goyi bayan haukarta sai baba laraba hatta yayar inna larai wato shema'u bata yarda ta goyi bayanta ba iyayen malam iro suka amince yayi auranshi mahaifin Inna larai wato malam sani shi yakarbawa malamute iro auran akayi bidiri aka gama antaho da amarya daga katsina zuwa bauchi lafiya washegari baki suka koma suka bar amarya da angonta nima nace barin barsu su huta.

Haleematu Where stories live. Discover now