Haleematu (54)

36 1 2
                                    

***Na: Reedahmz
**54**

Abdulhalim gaban Alh mustapha Annur yace Baba gani dazu nashigo mufida tace kana nema na yace inaso muyi wata magana mai muhimmanci ne kabani kunnuwanka da natsuwar ka, yace in sha Allah Baba...

Alh mustapha yace sonake in hadaku Aure da Husna dasauri ya kalli Alh mustapha yakoma ya sunkuyar dakai yace to Baba Ina godiya sosai..

Alh mustapha yace idan kuma akwai wacce Kakeso kada ka boye ka sanar dani kaji yace Babu ma Baba Alh mustapha yace toh shikenan Allah ya maku Albarka Amin cewar Abdulhalim yamike zuwa dakin shi da tunani mai tarin yawa..

Rabia da Amira sai Umar sunata yiwa mahaifiyar su Sannu Shamsu yashigo ya zauna yace Sannu Mama Yajikin naki tace dasauki sosai dazu kawunku yazo kun hadu? Yace eh munhadu kan maganar Ummi ce nayi bincike amma wai aski yakeyi fah, tace to shine me Ina ruwanka? Yace gaskiya naso ace tasamu me babban sana'a a hannu amma bakomai tunda yanada hankali ai shikenan Alhamdulillah! Inna Larai tace to sannu Ubanta  yace yi hakuri yanzu ga wannan kici saita sake tana murmushi... Ya mike yafita

Amira tace namata murna gaskiya tunda Yaya yaki Auren ta aigashi Allah ya kawo mata wani Rabia tace me askin ? Amira tace eh indai da rufin asiri ba laifi Umar yace amma dai gaskiya data samu wanda yafishi ai me sana'a ta aski zata tsinana masu? Amira tace dare daya Allah kanyi bature Inna Larai tace shegiya kodai ta shanye min ke ne kike kareta haka.

Haleematu kwance sai taga kira tadaga Mu'azzam ne tace aa Yaya Kwana biyu ya aiki Alhamdulillah ya masu jiki tace Alhamdulillah, yace Kwana biyu ya school din tace lafiya lau.. nakira inmiki murna gameda wani abu danaji za'a turo, tayi murmushi tace nagode Yaya Allah ya bar zumunci Amin.

Hamza yatafi mangu ya sanar da Yayan Baban shi game da Aure dayake so yayi kuma ance yatura Malam Hamid yace a Ina ne? Hamza yace Bauchi ne toh Masha Allah cewar Malam Hamid in sha Allah zamuje da liman koh yaushe suke so a zo? Yace yayanta yace nan da kwana biyar toh Allah ya yarda Amin Hamza yatafi..

Sunusi capacity yace Hashim Yarinyar fa tahadu ga kamun Kai  shiyasa Nikeso ai, abokin Sunusi Sagir yace batadace da dan iska irinka ba kuwa Sunusi yayi dariya yace inji ubanwa? Ai idan da kudi shikenan wai ko kamanta waye Babana?

Sagir yace ban manta ba amma dai shikenan.. Ilyas yace Sunusi yarinya dakake magana akanta anbiya sadakinta fa Aure kawai yarage, Sunusi yace dawa? Hashim yace Hamza Barber, Sunusi yace kutttttttttttttt! Sai dai idan kudi basa aiki Hashim Abokina babu abinda zaka iya kawai kayi hakuri Sagir yace kaga ba'a nema akan nema, Sunusi yamike ya Shiga motarshi da gudu.

Shamsu yace Ummi ya maganar danace kifadawa wancan yaron? Tace nafada in sha Allah nan da kwana 5 zasu zo kafin katafi. Yace ok toh yayi ya tamke fuskar shi sosai baisan dalilin jin haushin zuwan Hamza da mutanen su...

Abdulhalim gaban Husna yace kiyi hakuri bansan yazamu fuskanci wannan sabuwar alaka ba Wanda yazo mana daga sama. Tace Bro bakomai duk wanda yayi biyayya zaiga dakyau in sha Allah Inayi Mana fatan alkhairi in sha Allah, yayi murmushi yace toh Allah ya tabbatar mana da hakan Amin sukayi hira kadan yace zaifita zuwa cikin gari ta rakashi jikin mota yatafi tana kallon shi yafice.

Inna Larai da Baba laraba suke tattauna maganar Ummi suna dariya wai ai hakan shine daidai da ita. Inna Larai tace toh dama koda Mai kudi yazo wazai barta ta aura, ai ba ita Babu jindadi.. yadda tazo a wahala haka zatakoma Rabi dake tsaye tace aikoni naga mai maiko saina shiga na fita nan suka gama shirya mugunta son ransu sunata dariya abu yayi..

Nadia sunyi shopping tsaf Kamar yadda Imam ya bukata suka koma gida niki niki Saif kecewa ohhhhhhh ai wannan watan Yaya yadawo daga Lagos Dubai zamu tafi yawon bude ido 😄 Sorayah tace Ina har honeymoon zamu bishi Zayd yace ehem ehem kamar kinmanta waye Ya Imam? Nadia tace kugama duk indai guy dinan ne akwai ra'ayi yanzu yace ehh yanzu yajuya zuwa aa nidai fatana yasa yarinyar dazai aura ta rikeshi Amana sukace Amin...

Hamza cikin shagon askin shi wayar shi tayi kara yaga Haleematu ce, yabar Komi ya zauna ta gaishe shi yace yaushe zaki dawo tayi murmushi tace ohh jia fa nataho.. yace gani nike kamar shekara, tasake yin murmushi sannan tace Habibi yasu Mama da fam yace kowa Alhamdulillah kuma kowa yanaso yasan Habibty..tace a basu hakuri soon in sha Allah yayi dariya sannan yace miyasa brother dinki baya ko murmushi, amma kinga daya hadani da kawu naji dadi.. Haleematu tace sai hakuri haka yake zaku saba a hankali, yace shikenan Allah ya sa baki bukatar Komi ko? Tace Babu sukayi sallama yakoma bakin sana'ar shi da farin cikin jin masoyiyar shi.

A kwana a tashi Babu wuya wurin Allah Rana bata karya yau ankawo tambayar Haleematu kuma kawu Umar yabasu sunyi farin ciki matuka sannan yace subashi wata guda kafin asa date. Suka Amince da haka aka rakosu suka tafi.. Shamsu fushi yake yana cika yana batsewa yarasa mike tokareshi da kaunar Haleematu gabadaya wunin ranan yakasa sukuni har Haleematu tasame shi tace Yaya baka da lafiya ne? Gobe zankoma school Yaya.. kawai ya fashe da kuka yace inasonki Ummi aikuwa caraf a kunnen Inna Larai da sandarta tace mekace??? Duk suka waigo baki daya don ganin ina take..

Haleematu Where stories live. Discover now