Haleematu (61)

44 2 0
                                    

***Na:Reedahmz***
**61**

Inna Larai zazzabi ne ya rufeta dawowarsu daga dinner Amira kuwa takira yayansu ta shaida mashi Komi yayi Farin ciki yace hakan yayi min wallahi Ummi ta huta Amira tace sosai Yaya nan sukayi sallama takoma daki tasamu innar tasu tasamu bacci tace Allah ya kawo sauki Amin.

Hamza da Mikel suka nufi masaukin su Hashim don ya gode Masu suna shiga sai kallon shi suke yayi murmushi yace miye haka kamar kunga sabon abu? Iliyas yace aidole amma Allah ya sanya alkhairi mutumina Sunusi yace Muna tayaka Farin ciki duk jikin su a sanyaye yace yagode sosai kuma dasafe akwai budan kai in sha Allah Mikel ya mika masu hannu suka gaisa sukayi sallama dasu suka barsu cikin jimami da mamaki.. Sagir yace Allah kenan Sunusi yace gaskiya yanada wayo da dabara.

Baba Laraba tayi zugum ita tarasa mike damunta ma hassada ce aa tausayin kanta take aa gatanan dai tasallah tace ohhhhhhh ku bari mukoma muyi shiri na mussaman Rabia tace Amma Inna tasallah bazaku hakura ba? Wannan ai ya ishemu darasi tasallah tace toh munji.

Husna tarasa yadda zatayi da kanta duk a rude take ganin asarar datayi tarike kanta gam Sholy tace kiyi addu'a..

Sofy haba Husna don Allah kisawa ranki salama mana Husna tace inason shi dayawa kwarjinin dayake dashi ne irin na Shamsu yasa nike sonshi sosai to koma miye yanzu yayi Aure kuma banga alamar Karin aure a tsarin shi ba.

Biki yayi biki angama lafiya andauki amarya ankaita gidanta maiji da lafiya wanda yasha narkakun kudi kowa yayi ta santi washegari yakama hanyar daya fito Imam ya sallami su Inna Larai da motar dazata kaisu Bauchi da kudi makudai da kayan abinci dana biki...

Ilyas dasauran abokan arziki suntafi da Mamakin Imam da irin tarin dukiyar gidansu ikon Allah kenan...

Haleematu tayi wanka tsaf tashirya cikin shiga ta alfarmar don jiran angon ta mai abin mamaki zuwa 8pm ya shigo yasameta shiru zaune yayi sallama da murmushi dauke a fuskar shi ya zauna yace Amarya bakya laifi murmushi kawai tayi, yace Ina me baki hakuri da abubuwan da kika gani na mamaki wanda bakiyi tsammani ba, dakuma yadda na boyemiki asalina. Nayi haka ne saboda dalilai guda uku wanda Zan fadamaki yanzu, "Nayi hakane saboda in samu soyayya ta gaskiya ba don dukiya ta kota mahiafina ba" Nayi hakane saboda antaba yaudara ta Allah ya fitar dani" Sannan Ankini saboda nace iyaye na bakowa bane Kuma aski nikeyi". Bayan da mahaifina danata Aminai ne Amman bata sani ba saboda ba anan nike ba bamu taba haduwa tunda ta girma sai lokacin da mahaifina yaturani nace karya fadawa Amininsa Babanta kenan saboda inason in mata wani gwaji toh kinji dalilai na dayasa naje na saje daku a Abu Zaria har Allah ya kawoki kamar wasa. Kema nafara har garinku unguwar naje nayi bincike akanki kuma anbani shaida mai kyau aka kuma fadamin irin wahala da kika ci a cikin gidan mahaifinki. Alhamdulillah nadau alkawari nabaki jindadi in sha Allah kisoni don Allah My wifey . Ajiyar Zucia Haleematu tasaki tace nagode Habibina Allah yabamu zaman lafiya medorewa Amin yace sannan yace to muje muyi alwala don gabatar da nafila ta godiya ga ubangiji ya bamu zuri'a dayyiba.

Albarka kam Haleematu tasha shi wurin mijinta saboda samunta da yayi a cikakken budurwa yayi godiya wa Allah da mace tagari kafin sufito har ankawo masu breakfast daga main house bayan sunyi wanka tashafa humra shima yafito sanye da kananan kaya ya riko hannun ta zuwa dinning area tanata sunkuyar dakai yace toh zaki daina wannan kunyar kokuma mu maimaita abin jia yanzu dasauri ta dago tace am sorry hubby ya fashe da dariya suka zauna suna hira suna karyawa yace sutashi suje cikin gida wurin iyayen shi da Yan uwa tagansu tace toh yadauki waya yakira Hajia ya gaisheta yace suna zuwa yanzu sungode da break tayi dariya tace Allah ya maku Albarka Amin.

Tasa leshi dinki yakarbi jikinta shikuma jamfa yasa suka kama hanyar gida tunda babu nisa suka isa yarike hannunta sukayi sallama da gudu Nadiya ta fito ta bata hug Hajia Sumayya tace saketa karki yar da ita takoma hannunta suka karaso tazauna bisa carpet ta durkusa ta gaida Hajia Sumayya shima Imam yayi gaisuwa yakoma gefenta yazauna Alh Inna yayi sallama cikin falon yazauna yace abude taro da addu'a akayi sannan yayi masu nasiha yace da Haleematu tadauki gidan shi tamkar nasu tayi godiya Hajia Sumayya tace idan kinada matsala ki fadamana in sha Allah kinji tayi godiya akace za'ayi introduction kowa yana nan. Imam yace do I have to introduce everyone? Kamata yayi kufada da kanku ai Sorayah tace Ehem Brooo ya kalleta yace what? Tace no nothing your wife looks take away dariya duka sukayi.. Imam yace wannan itace Nadiya diya ta biyu a gidanan Next is Saifullah ,Soray aka fashe da dariya don shi yasamata sunan haka hattah Alh Inna idan yaso nishadi sai yace Soray sai Ramadan, Zaid, Khalid, Marwan and last born Fauza. Masha Allah tace cikin murmushi Hajia Sumayya tace kisaki jikinki don Allah tace toh Mama in sha Allah Nadiya da Sorayah suka caja daki don hira kadan.

Husna kuka take wurin Mahaifiyar ta tana bata hakuri Hajia tace Asmau kishare hawayenki Dole ki auri Imam idan ina raye Husna tace nagode uwata.

Inna Larai ta zube saboda hassada daya tsaya mata a rai ga bakin cikin ace Haleematu ce a cikin gidan Baba Laraba tace nikam na saduda wallahi Rabia tace Ina tare dake Baba Inna Larai tace ai saina hana yarinyar nan zaman jindadi Baba laraba tace Larai na haneki da shiga hurumin ubangiji Inna Larai tace Ina ruwanki? Tunda bakiyi ai shikenan zaki sha mamaki! Rabi'a tace wallahi gaskiya take fadamiki Inna Larai ta dubi Rabia tace buhun ubanki shashasha kawai, nan suka barmata dakin duk yadda sukayi Umar yanaji yashigo yace Wallah Inna kiji tsoron Allah kibar Ummi ta huta a gidanta azabar ya isa haka tace dashi fita a dakina yamike yayi tafiyar shi wurin abokan shi kawai

Washegari Inna Larai da tasallah suka kimtsa don zuwa wurin matsafi wanda suke kira da mallam Rabi'a tace Inna kifita hanyar tasallah babu inda zata kaiki sai tashar wahala inna Larai tace idan kikasake tsoma bakinki cikin lamarina zakiyi mamaki sosai tafice tana dingisawa a hankali zuwa gidan tasallah abinta.

Sun kama hanya sukaje yabasu magani yace aje a tona kasan murhu a binne duk inda take zaman gidan miji zai gagareta tadauko kudi ta ajiye suka fito don dawowa cikin gari sunzo dab titi kawai sai ga Mai tirela sukuma sun sa Kai baiyi wata wata yabi kansu duka!!!

Haleematu Where stories live. Discover now