Haleematu (44)

31 4 1
                                    

***Na: Reedahmz
***44

ZARIA

Haleematu cikin garin Zaria tanata dube dube tadauki kayan ta sai cikin school takira Shamsu yace yana zuwa kusan mintuna 20 min ya iso suka shiga sukayi komi tare suka kamalla yamata nasiha tace tagode ya hadata dawani abokin shi idan tanada bukatar wani abu suka fito Shamsu yace Inane gidan dakace zata zauna suka fita ya nuna masu shima gidan dalibai ne wanda basa son hostel ciki da a falo ne matsakai ci da toilet dakuma kicin dinta dan daidai itama ya birgeta shamsu yace katifa fa yace akwai mai kawowa zansa yakawo Shamsu ya bada kudi sannan yabata kudi dazata karasa siyayya yace zai wuce tayi karatu ta kuma kiyaye kanta tayi mashi Allah ya tsare yawuce sukayi sallama tadawo ta fitar da wasu kayanta tagyara wurin tsaf saiga katifa ankawo mata tasaka Mai zanin gado tazauna tabuga tagumi tace Allah ya sa nazo cikin nasara Amin ta rufe dakin tamike saboda gajiya cikin bacci takeji kamar ana knocking kofarta tabude ido dakyar saboda bacci waye saitaji muryar mace tabude saita ga wata siririya haka tace sannu da zuwa sunana Sara White nima cikin gidan nike hope zamuyi mutunci Halimatu tace in sha Allah..

Bauchi
Inna Larai tace tasallah kinsan shirina na gaba kuwa sonake a mallakewa Rabi'a Mu'azzam sosai fa sai yadda tayi dashi don uwarshi zata iya hanashi shiyasa kinganni nikadai tasallah tace nadauka zama zakiyi ai bazaki mike tsaye ba har garin kallon ruwa kwado yamiki kafa Inna Larai tace kada kidamu ina shiri tadauka banda wayo ne insa a raba dan nawa da farin ciki ma balle nata tasallah tace toh kibari karshen sati mukoma in sha Allah zaifi sauki Inna Larai tace toh shikenan Allah ya kaimu kafin ma nasamu wasu karin canji tace hakane sukayi sallama takoma gida

OSUN
Husna abin duniya ya isheta gabadaya batada wani tunani saina Shamsu kuma batada phone number dinshi gashi bata ganinsu duka wurin cin abinci Sofy tace don Allah kisawa ranki sauki wai miye haka ne sokike ki kashe kanki toh wallahi zankira Ummah a waya infadamata Husna tace bazaki gane ba kokadan Sholy tace duk da haka kicire damuwar da namiji a ranki don Wallahi zakisamu matsala gagarumi mara yankewa nidai kibi komai a sannu inhar mallakinkine zaki sameshi cikin ruwan sanyi inkuma bahaka ba duk dabarar ki bazaki sameshi ba Husna tace nagode matuka da kulawar ku gareni Nagode..


Haleematu Where stories live. Discover now