Haleematu (57)

37 1 0
                                    

***Na: Reedahmz
***57***

A garin Bauchi Haleematu ke kwance a dakinta dai na soro sai dai kunsan a gyara mata shi lokacin bikin Mu'azzam da Rabia Inna Larai ta kwada mata kira tamike dasauri don tasan bakowani kiran Inna Larai bane alkhairi, tana zuwa tace toh yanzu tunda kina gida ana hutu zaki cigaba da ayyukan gidanan Haleematu tace dama inason in sanar maki inason zanje Katsina nan da kwana biyu in sha Allah, caraf Baba laraba tace da izinin wa? Tace naku toh bazakije ba inji Inna Larai Haleematu tamike tace gaskiya yanzu bazaiyuba shekaru nawa kun hanani zuwa wurin dangin mahaifiyata kuma kun hanasu zuwa ganina  haba laifin menayi hakane dana hakura yanzu kam bazan iya ba, Rabia tamike Baba laraba tace aa zauna kinga lafiya bai isheki ba karkisa ja'iranan tamana asara....

Inna Larai tace lallai wuyanki ya isa yanka tace ko ina mukaje Inna inada gaskiya daidai shigowar Umar Inna Larai tasa kuka ni zaki zaga yau Ummi? Yace waye yazageki tace gata mara kunya yace mine ke Ummi yadaga hannu zai zabga mata mari kawai ta sunkuya yadagi jikin gini da hannun shi, tafice da gudu tadauki itace tace nagaji shekara ashirin da Yan kai ina bautuwa da cutuwa aikuwa yayo kanta da gudu yakai mata Mari itakuwa kafin yazo tashiga dakinta ta rufe takira wayar kawu Umar tace yazo gidansu babu lafiya takashe wayar, Umar kuwa sai dukan kofarta yake wai sai ya mata mugun duka.

Cikin haka kuwa saiga kawu Umar din yazo duk jikin su ya mutu yace ina Haleematu ya kwada mata kira tafito dasauri yakira kowa aka zauna, yace mike faruwa? Ke Haleematu kinkirani ta zayyana wa kawu Umar komi, yadubi Inna Larai yace ashe ke haryanzu duniya bata koya maki hankali ba? Kiji tsoron Allah wallahi don saiya tambayeki kaikuma katon namiji kashigo bakasan komi ba zaka hau kace zakayi dambe da Mace kabani kunya kekuma Laraba Allah wadaran wannan lalacewar taki da girman ki da saninki ake cutar da yarinya amma baki iya komi toh ku kwantar da hankalin ku yarinya takusa aure ta huta da jarabarku. Inna Larai tace Yaya wannan yarinyar munafuka ce yace rufemin baki tsit tayi don sun san halin shi, yace ke jeki hada kaya jibi saiki tafi Katsina din. Tace nagode kawu Allah ya kara girma Amin yadubesu yace idan natafi wani ya tanka maki ki sanar dani cikin bacin rai yafada.

Bayan Kwana biyu da faruwan haka bama maikulata ko abinci nema takeyi ta shirya tawuce Katsina bayan tayi sallama da kawu Umar yabata kudin shan ruwa a hanya dayake bata manta address din ba.

Mal Hamid sundawo garin Bauchi wurin kawu Umar akan batun sa rana yace basa bukatar Komi sai sadaki Mal Umar zaune yakira Amininsa guda biyu saikuma Malm Hamid da Liman. Kawu Umar yace toh yanzu zamu daura Aure fa don banason jinkirinan Liman yace hakan yayi kyau sosai kuwa... Aka daura Auren Haleematu da Hamza, sannan kawu Umar yakira Shamsu ya shaida mashi yadaurawa Ummi aure yanzu, gaban Shamsu yafadi yace amma kawu ita din tasani? Kawu Umar yace batasaniba saita dawo tukunan, bayan rakiyarsu Mal Hamid, kawu Umar yawuce wurin su Inna Larai yabata goron sure a hakan tabarshi a wurin tace taje takarata da talauci.

Mal Hamid yakira Hamza yace toh albishir dinka yace goro to yanzu dai muka daura maku Aure da Haleematu ihun farin ciki hamza yayi sannan Mal Hamid yace karka fadamata tukun in sha Allah zankiyaye sukayi sallama..

Hamza yakira mahaifiyar shi ya shaida mata tace Babana kenan ai mahaifinku yafadamin nayi farin ciki Yan uwanka ma sunyi farin ciki.

Yace nagode sosai Mama tace biki kuma in sha Allah sai a hankali yace a shirya komi a hankali saina shigo tasa mashi Albarka..

Haleematu tasamu kakaninta cikin koshin lafiya sunyi farin cikin ganinta sannan kawu Umar yakira tahadasu suka gaisa ya shaida masu yadaura mata aure za'a yi biki daga baya sukayi murna itama ya sanar da ita tadawo intayi kwana biyar tayi sallama dashi..

Mikewa tayi taje tayi sallah raka'a biyu tayi godiya wa Allah ta roki Allah zaman lafiya dakuma kariya sannan tadauki waya tayi text wa Hamza..

Assalamu Alaikum Habibinah mijinah abin kaunata nayi farin cikin wannan labari medadi dana samu Allah ya sanya mana Albarka cikin Auren mu Amin... ((Sultanatou Qalbee))

Zaune yake yana duba wani kaya dayasa akawo mashi yaji shigowar text yana budewa Kawai sai murmushi yaketayi Yana gama karantawa ya rungume wayar yace zanyi surprising dinki in sha Allah gobe da safe.

Alh mustapha Annur yace da Husna yasa Aurensu da Abdulhalim nan da sati biyu Masu zuwa tace toh mungode yace kuna fahimtar juna sosai ko? Tace eh Alhamdulillah yace to tashi kije Kituro mamar taki tace toh.. Bayan ta koma daki takira Sholy da Sofy tahada conference nan take shaida masu komi, Sholy tace kuma kundace fa Sofy tace Amman ina fata baya maki Wannan kamun kan nashi tace Ina aibazai fara bama, Sholy tace kinga wani hanin ko ba wancan sojan me shegen zafin kai ba. Husna tace har gobe ina son shi Sofy tace to saikitayi nikam sai anjima zamuzo gobe husna tace Allah ya kaimu tana dariya..

Na tambayi unguwar su cikin dabara Sagir kai dai yanzu tunda mun iso muje muci abinci koh? Sagir yace hakane suka nemi gidan abinci sukaci sannan sukayi sallah suka dauki hanyar zuwa gidansu Haleematu yadda Ilyas yafada mashi bayan sun shiga cikin unguwar basu ja ba suka samu gidan sukayi parking sun dan jima bakowa can saiga Inna Larai tafito tana dingisawa suka zo gareta suka durkusa suka yi gaisuwa nan tafara washe baki taga maiko, yace Baba tambaya muke gidan Mal Iro Katagum tace ahh yaro nan ne amma lafiya? Yace eh nazo wurin wata yarinya ne Haleematu nan Inna Larai tahada rai tace kaikuwa saurayi wannan yarinya data gama timbele a gari yanzu saboda abin kunya datayi aka daura mata aure a boye, Sagir yace anya itace kuwa? Tace itace kayi mamaki koh? Karkadamu zamu baka kanwarta what???

Haleematu Where stories live. Discover now