Haleematu (3)

137 7 0
                                    

Na:Reedahmz
Page 3

Bayan Baba Laraba tagama radawa Inna Larai abinda yadace suyiwa marainiya baiwar Allah sai suka fashe da dariya dukkan su biyun ,ita kuwa tana durkushe bisa kafarta tana jiran a bata umarni taje tayi wanka da sallah don yau tagaji dayawa, Inna Larai tadubeta tace tashi ja'ira bakar munafuka kibar kallona kar intsiremiki idonan masu kama da na mujiya .. A hankali ta tashi ta nufi bayi tayi wanka hadi da alwala tadawo daki tadauko wasu kayanta tasa tayi sallah tazauna bisa sallayar tana mai zubar da hawaye tana kai kukanta wurin ubangiji akan wannan zalunci da ake mata cikin gidan mahaifinta Wanda duk tsanar mahaifiyarta yadawo kanta. Bayan tagama komi tajawo kwanon dake gefen kofa tabude taga tun tuwon jiya ne akasake ajiye mata shi kawai saiji tayi hawaye nabin Kumatunta tsabar bakin ciki tasa hannu ta share tahau ci da hakuri bayan tagama kuwa tashi tayi ta wanke kayanta kala hudu a cikin Daren ta shanya tazo ta kwanta bayan tayi sallama dasu Baba Laraba ta daga kanta sama tana kallon kwanon dakin tace yanzu da mahaifana suna Raye bazan sha wannan wahalar ba dubi dakin danake kwana kusada zaure bamai tunanin wani hali nake ciki ta matse hawayen dake kokarin zubowa tace Allah ka fitar dani daga wannan kangin bauta a haka bacci barawo yayi gaba da ita cikin baccin ne tayi mafarki da iyayenta suna cewa tayi hakuri firgigit tafarka tana hakki tashi tayi ta dauro alwala tafara nafiloli ....

Haleematu Where stories live. Discover now