Haleematu (65)

26 1 0
                                    

**Na: Reedahmz**
**Haleematu 65**

Yace Kai Abdul wannan kallo haka yayi dariya yace Maigida aidole saboda irin Wannan kudi da aka narkar mikel yace toh ai wannan bakomai bane cikin dukiyar Alh Inna yace yawwa ai nan ne gidansu abokina dakuke kama da Matarshi Abdul yace ai har na Matsu in shiga don ganin ikon Allah mikel yaja hannun shi sukayi sallama cikin falon Imam yace ikon Allah kawai don wani mugun kama dayagani na Matarshi a tareda Abdul yayi matukar bashi mamaki yace Mikel ku zauna barin kira Haleematu tazo taga ikon Allah dasauri yashige daki yasameta tana Shirin fitowa..

Yace hummmmm fito kiga ikon Allah tace sun shigo kenan yace eh toh muje suka fita yana gaba tana binshi a baya suka shigo falon zumbur Abdul ya mike gami da bude baki yace what! Itakuwa kasa daga kafarta tayi saboda tsananin ganin kamarta da wannan bawan Allah, Mikel yace kaga yanzu ma sunfi kama dana gansu tare Ikon Allah Kowa yazauna sannan aka gaisa  cike da mamaki. Imam yace Amma don Allah kai dan wani gari ne? Abdul yace Bauchi, eh Haleematu tace nima ai yar Bauchi ce Mikel yace kaji wani abin sukayi ta mamaki hakanan dai.

Bayan sunci abinci suka mata gaisuwa suka wuce family house sukayi gaisuwa nan ma sukayi ta mamaki Alh yace kai dan waye a Bauchi? Yace Alh Mustapha Annur yace aa ikon Allah kodai kaine Yaron dayake bani labari kullum Abdulhalim yace eh nine nayi mamaki dabaka gane fuskata ba ai Alh Inna yace kayi hakuri yaro kasan sha'anin girma sukayi daria yace yanzu kana ina? Yace Ina Katsina ina Alh Inna yace Mika'ilu kuna tare kenan? Yace eh baba Allah ya taimaka Amin Alh Inna yatashi yafita Nadiya Allah Allah take suke kebe da sahibinta.

Rabi'a suna tana jimamin irin warning dasuka dingayiwa Inna Larai randa sukace karta fita takiji Umar yace ai shikenan Allah ya jikan Inna kam yanzu gashi Haleematu ma tana hutawa, Amira tace uhmmm rayuwa kenan. Sai Rabi'a tace Baba Laraba tunda wannan gida an rabashi tuntuni inaso kidawo gidana da zama Mana? Baba Laraba tace eh kinkawo shawara gida dai na Umar,Amira da Haleematu ne duk dai daki daya shine mallakin mahaifiyar ku Kinga kenan keda Shamsu ma kunada kaso aciki Amman tunda karshen wata Zasu zo saimuyi zama dasu ko? Sukace hakan za'ayi.

Alh Inna yakira wayar Alh mustapha suka gaisa yace yau dai nasha kunya fa Alh mustapha yace aa name kenan? Alh Inna yace ai yaron wurinka yazo Amman nakasa gane shi fa saida ya fahimtar dani Alh mustapha yace wani yaron wai? Alh Inna yace aa Abdulhalim mana, Alh mustapha yace don Allah yana gidanka yanzu haka? Sosaima cewar Alh Inna, Don Allah ka rike manshi ina zuwa Alh Inna yace lfy Amma ko? Alh mustapha yace lfy Amma yafi watanni da barin gida ban san dalili ba don ko wayarshi bata Shiga. Alh Inna yace toh shikenan saikazo din.

Abdulhalim yakoma gidan Hamza don jiran Mikel ya gama hira da Nadiya. Yana kokarin fita suka ci karo da Sorayah tadago ta kalle shi Kawai tace ikon Allah! Shikuma yace kiyi hakuri don Allah ina dan sauri ne tace no bakomai ita mamakin ta kawai kamar dasukeyi da Matan yayanta tagani daya daure mata kai. shikuwa birgeshi tayi matuka don tana da kyau murmushi kawai yakeyi har ya isa gidan.

Alh mustapha ya shaidawa Hajia samun lbrn ganin Abdulhalim gabanta ya Fadi tadai matse ta nuna farin cikin fuska kawai yace Jos zamuje yau in sha Allah karya sake bacewa murmushi kawai tayi tace saika ce wani yaro? Husna dake jinsu takada kai Kawai yanzu tasan ya mata nisa dole ta hakura dashi it's nata kaddara da haka yazo, zata nemi soyayya ta Shamsu kawai tunda Mu'azzam ya tabbatar mata baya dating kowa kuma zai taimaka Mata sosai...

Alh Inna yasake Kiran Alh mustapha yace kasan Allah suna kana da Matar Imam Ikon Allah gamu fa yanzu zamu fito

Cikin abinda baifi awa biyu ba suka iso Jos bayan sun zauna Alh Inna yatura akira Abdulhalim bayan ankira duk suka shigo da Imam din da Mikel sai Haleematu. Abdulhalim na ganin Alh mustapha da Matarshi sai Husna ya zaro ido!!!

Haleematu Where stories live. Discover now