Haleematu (22)

52 5 0
                                    

** Na: Reedahmz
**Page 22

Rabi'a tacika tayi fam da ita haka tagama sauran wanke wanke da kuma wanke bayi saida Yayan su ya tabbatar tagama sannan yafita Inna Larai tace rabu da ita ai zata dawo gidan tasameni yau.

Sallama sukaji inna larai tace muryan wa nikeji Yaya yashigo da fara'arshi yace nine inna yaushe a gari yace dazu toh ya mutan gidan naku yace kowa lafiya Baba Laraba tafito tace Aa Yaya manya sannu dazuwa yayi murmushi ya durkusa a kasa yace mama Ina kwana tace lafiya dan albarka ya garin yarbawa yace Alhamdulillah

Yaya kamar yadda kukaji shine babban da ga Baba Laraba su biyu ta haifa da kanwarshi kafin Mahaifinsu ya mutu suna cemishi Yaya ne saboda Sunan malam iro yaci wato Ibrahim a waje da wurin aiki duk mu'azzam suke kiranshi kanwarshi kuwa Zainab shi kusan sa'a ne ga Shamsu itakuwa Zainab sa'ar Haleematu tana zama wurin Yayan Babansu shikuma tare suka samu aikin soja da shamsu Amman shi Air force ne.

Dasauri aka kawomishi koko da kosai yace wallahi nayi rashin irin wannan abubuwa sukayi dariya Rabi'a tafito tana yauki kamar kubewa tace Yaya barka da isowa yace manya barka yana sameku tace Alhamdulillah ya Osun yace Alhamdulillah can yace nikam Ina Sadiya don shi haka yake cewa Halima suka ce ta tafi makaranta yace Allah sarki kukam kun gama koh tace eh result muke jira shin Ina kuka cike a jamb dinku ne tace ehh first choice dai Nasa ATBU sai na biyu nasa UDUS yace wani course tace ATBU nacike Biochemistry UDUS kuma Microbiology yace Good

Baba Laraba da Inna Larai suna tattaunawa nikam sai inga kamar Yaya yanason Rabi'a cewar Baba Laraba Inna Larai tace aikuwa da anyi tuwo na mai na Amman kyalesu intayi tsami zamuji aida kuwa munkara karfin zumunci.

Haleematu Nơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ