Haleematu(35)

28 3 0
                                    

***Na: Reedahmz
*** 35

Yana fita yaje waje ya zauna yana kallon masu wucewa har aka kira sallah yamike yatafi massallaci suka hadu sukayi tareda Shamsu dayaje kasuwa ya siyowa Haleematu wasu abubuwa dabata dashi yabata a boye don gudun magana Mu'azzam zaune yace Dan uwa Allah yabamu ikon yin biyayya ga iyayen mu Amin Shamsu yace aigara kaima naka dasauki a yanzu yace hakane Amman kaima kayita addu'a da sallolin dare Allah zai kare yakawo maka sauki in sha Allah nagode sosai bro nan Rabi'a tashigo dauke da abincin su tace Ya Shamsu wai Mama kaje yace toh itakuwa tace Yaya ga list din dakace yakarba ya duba yace shikenan in sha Allah zansiya komi a can yadauki dubu ashirin yabata yace kiyiwasu hidimar ki in sha Allah kafin nadawo anjima zamu fita da Shamsu zantaho maki da waya ki rike mudinga magana ta rufe ido tana godiya yace tashi kije ta mike ya bita da kallo a zuciar shi yace zanyi hakane kawai saboda nasihar kawu Umar Amman Rabi'a bata cikin matan danikeso Allah kabani ikon kyautata mata Amin ya shafa Yace Haleematu ta amsa tazo yadauki dubu goma ya bata yace ta boye ko zatayi wani abu wataran..

Yanzu Yaya zakatafi yaushe zakadawo kasan fa su Amira maganar makaranta babu yace zandinga turowa Rabi'a ko Umar zasu na ciro maki in sha Allah tace shikenan yace Mama kiyi hakuri akan abinda yafaru wallahi gani Nike idan bani na auri Haleematu ba babu wanda zai rike Amana da Baba yabani tsakani da Allah Inna Larai tace eh sosai sarkin Masu Amana na duniya Baba Laraba tace Sayyadi Ashe kai shasha ne yanzu duk abinda muke hangowa ku baku hango bako uwar yarinyanan farin kafa gareta Amma ku bakwa gani Shamsu yace Aa Baba wannan canfi ne kawai irin na hausawa Inna Larai tace shikenan ai jiki magayi yace kiyi hakuri tace bakomi tashi kaje kuci abinci tunda tare zaku tafi goben yace in sha Allah Shamsu yakoma yatarar da Mu'azzam na waya yajira shi yagama sukaci abinci suka gama yace muje nan inaso insiya was Rabia karamar waya ok sukaje suka siyo sundawo yafita ya kirata Shamsu na daki yaji sakon text yaduba sai yaga transfer ne kuma zuwa osun yayi farin ciki sosai Mu'azzam nashigowa ya shaida mashi yatayashi murna.
Allah ya dare gari yawaye su Soja antafi akan Shamsu zaidawo nan da kwana biyu tunda report zaiyi yabar Haleematu da kunci donkuwa azaba daban daban Inna Larai tafara Mata harta kaiga makaranta kullum cikin makara toh ranan wata litinin Haleematu tana sauri suna da test ga tarin aiki da aka ajiye mata kawaii tafita ta tafi tace idan tadawo zatayi Ashe Inna Larai tacika fam Baba Laraba cewa take zatadawo tayi sallama tashigo Inna Larai tace ubanwa kikabarwa aiki yamiki banace karki sake fita batare da kingama aiki ba tace test muke dashi kuma zanyi latti Baba Laraba tace wazaki nunawa boko Inna Larai tarufeta da duka ta ko ina bugu takamata tahada da bango aikuwa nan take Haleematu tafadi a sume.

Haleematu Where stories live. Discover now