Haleematu (46)

38 2 2
                                    

***Na: Reedahmz
***46

Husna batasan lokacin da hawaye na takaici ya zubo akan fuskarta ba tsabar takaici Sholy ta amshi key din mota tace Sofy kuzo mutafi please kar a tsaya kallon mu suka ja hannun husna zuwa mota basu tsaya ko Ina ba sai gidan dasuke ta ajiye jakarta ta rike kanta gam Sholy da Sofy sukace don Allah karkidamu kanki wai shin shine da namiji guda daya ne dazaki daga hankali inagashi garin bin shi ji wani wulakantaki da yayi Husna tadago takalle su tace nayi nadamar yi mashi magana yau aiko baisan niba yakamata ya mutuntani hmmm..

Haleematu zaune Ilyas kecewa gaskiya wancan lecturer din ya iya bayani yadda mutum zai fahimta sosai Hashim yace sosaima ni ai kamar kar yafita Haleematu tadubesu tana murmushi kawai Hamza yace kinji mutanen naki ko sai santi suke kamar abinci duka suka kwashe da daria sallamar white ce katse su duka suka amsa ta gaishesu Ummi har kinfito kenan tace nafito white tundazu tazo gefen Ummi tazauna Ummi tace Guys ga neighbor dina Sara White sukace welcome to the club tace thank you Sara ga course mate dina Hamza, Ilyas and Hashim tace nice meeting you guys sukace welcome White

Mu'azzam ne suke waya da Shamsu Shine yake cewa waini yaya joint ne Shamsu yace naje nahadu da wancan yarinyar mai shegen rawar Kai Mu'azzam yafashe da dariya Wai Husna baiwar Allah babu ruwanta toh ya kukayi? Shamsu yace nayi mata warning wai inbata number nace takama kanta kamar mata masu class wannan rashin class ne Mu'azzam yace baka kyauta ba kaduba yadda ta ajiye komi ta tunkare ka fa Shamsu yace toh shine nifa nayiwa tufkar hanci yawwa Mu'azzam dai shiru yayi sannan yace nikam Miyasa zaka fasa Auren Ummi toh koma miye yanzu inason sanin dalilin kin Auren Ummi Shamsu yace nifa bansaniba amma jinake bata cikin raina Kawai bansonta da Aure. Mu'azzam yace toh lallai kana bukatar addu'a mai karfi, don ni idan ba don uwata tayi saurin sara baki to da Babu makawa zanyi.... Shamsu yace hakane Amman mubarwa Allah Komi, kasan rayuwa zabin Allah shine zabin gaske, don Haka Komi yayi farko yanada karshe, Allah ya bamu jarabawa dazamu iya Ameen inji Mu'azzam amma gaskiya a bawa Husna hakuri , Shamsu yace wai wannan wani irin iskanci ne duk abinda banaso naga alama kanaso, murmushi Mu'azzam yyi, yace toh zan maka rakiya idan zakaje kaji aboki....

Haleematu Where stories live. Discover now