ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 82

4K 293 57
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨














💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼
















🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan zaman lafiya da amana insha Allah🤜🏻🤛🏻))
















_Itz_queenbk @ insta gram_











Page 8⃣2⃣














Washegari da sassafe Abbah ya iso ya baro Auntyn Yara da wata ƴar uwarta budurwa me kimanin shekaru 18 a gida dan yanzu an sallamota daga asibiti ta warke garas sai tabunnan ciwon da taji, keken guragu aka bata yanzu dashi take tafiya, wannan budurwa mai suna Zeenah ita ke kula da ita ɗiyar ƙanwarta ce, yarinyar akwai mutunci da hazaƙa ita ke mata komai dan gane da jikinta, a inda mai aikinta ke sauran, yanzu Auntyn yara ta safko sosai barin ma da taji yadda Ladi tayi mutuwar wulaƙanci shi ne take tunanin fidda wannan muguntar a ranta tazo tai ta aikin tuba wajen ubangiji da waenda ta zalunta sai dai labari ya canja a lokacin da haihuwar ƴaƴan Abdallah ya iso kunnenta sai da tayi ƙaramin hauka tsabar baƙin ciki bugu da ƙari kuma Abdallah ya samu sauƙi.
(Ni ko a raina nace anya matar nan tana da alamar tuba a ranta kuwa muje zuwa muga ina ta dosa).




Bayan Abbah ya iso likitoci sun mai bayanin duk abunda ake ciki yayi murna sosai ta wani ɓangare kuma bai ji daɗi da Abdallah ya manta matarshi mutuniyar arziƙi ba, Allah sarki baiwar Allah dan ma Allah ya bata haƙuri da ya zata ji ga jego ga wahalar yara har biyu da ba babansu a kusa da zai na ɗebe mata kewa yana taya ta wahalar oh Allah me tsarin shi a sadda yaso akan ko me yaso, Allah kasa mana fahimta a zuciyoyinmu.


Ɗakin da Asmah ke ciki ya fara nufa yaga babies ɗin ya nata sa ma Asmah albarka yana ƙara yabawa da hankalin ƴarinyar, daga nan ya wuce ɗakin da aka kwantar da Abdallah cikin murna uba da ɗan suka tarbi juna suna masu matuƙar farin ciki.






Ƙarfe sha biyu dai dai aka ba Asmah sallama suka wuce gida wankan jego mai kyau Hajiya Zainab tayi mata ta shiryata tsab Ammie kuma tayi ma babies ɗin wanka aka feshesu da turaren yara mai sanyi, turaren wuta mai daɗi aka kunna a gidan ya hau fitar da ƙamshi mai daɗi ɗakin mai jego kuwa room heater aka kunna kasancewar weather su ta can ana wani muku mukun sanyi ne, kamar yadda al'adar su tacan ta tanadar, jama'an unguwa mata sukai ta shigowa nan sukai ta dafa abinci da kayan maƙulashe irin dai nasu kala kala, da suka gama suka gyara wajen tas sannan suka rinƙa fito da kyaututtuka kala kala suna ba Babies ɗin da uwar jegon, haka suke tarbar sabon jariri suyi mashi kyauta sannan suyi ma uwarshi abinci kala kala, kasancewar suna fita kullum shi yasa suka saba da mutan unguwar.


Washe gari aka sallamo Abdallah bayan an ɗora shi akan magunguna, suma nan suka yo gida koda ya tambayi wacece Asmah ce mai sukai ai beautynshi ce ta dawo nan suka bashi labarin yadda akai ta ɓace da kuma yadda Allah ya ƙara haɗa su da ita ba tare da sun sha wata wahala ba sai suka yanke mai sauran labarin saboda gargaɗin likita na cewa kar a sake a tuna mashi wani abu da ya faru da shi a baya domin zai ta ƙoƙarin tunowa ne wanda hakan hatsarin ne ga ƙwaƙwalwarshi, sun ƙara mashi da cewa Asmah tayi aure har ta haihu yanzu haka mijinta yayi wata tafiya mai tsawo ne, ya ji daɗi sosai da beautynshi ta bayyana gashi yanzu har tayi aure har Allah ya albarkace ta da ƴaƴa.





Bayan sun huta sosai Abdallah yace ma Mahmud ya raka shi shopping wani ƙaton mall suka je nan Abdallah ya shiga jidar kayan sawa da mayuka da turarurruka kallar wanda yake amfani dasu da, sai da suka zagaye gari sosai sannan suka dawo gida a gajiye.







*********



Abdallah ne zaune a masaukinsu kwance yake kan gado yayi fulo da hannayenshi a yayinda Mahmud ke gefen shi suna waya da Miemie, abubuwa ne da yawa ke yawo a zuciyar shi labarin Asmah da Mahmud ya bashi yake ta ƙara bita a ranshi, ji yai kamar an tsikare shi zumbur ya tashi da hannu Mahmud ke mai nuni da "lafiya?" cewa yai "ina zuwa" sannan ya fita falon gida yana fita yaci karo da Ammie zata wuce kitchen riƙe da robar wankan baby a hannunta da sauri ya ƙarasa gareta tare da miƙo hannu zai karɓi robar yana faɗin "sannu Ammie" janyewa tayi tace "yauwa Abdallah" sai da ta aje robar sannan ta dube shi ta cigaba "shin kaje kayi ma ƙanwarka barka kuwa? Abdallah wai ko ka manta Asmah ne?".



Sosa ƙeya yayi yace "a'a Ammie ban manta da beauty ba, tun da na dawo ban ganta bane shi yasa ban mata barka ba".


"Ɗama ina zaka ganta kai baka neme ta ba?".

"To Ammie na ɗauki laifina ayi haƙuri, tana ina ne?".

Da hannu ta nuna ɗakin da Asmah ke ciki tana faɗin "ka shiga wancan ɗakin".


"Ammie in shiga ciki".

"Eh" kawai tace mashi ta wuce ta cigaba da sabgarta.




Tsayawa yai yana ta mamakin wai ya shiga ɗakin da Asmah take ba ita ya kamata ta fito su gaisa ba basai ya shiga har ɗakin ba tunda dai ita matar wani ce, amman ko ma meye dai ai Ammie ta fishi sannin haka ɗin dan haka ya yanke shawarar zuwa, hanyar ɗakin ya nufa yana tafiya a hankali sai da yaje gab da bakin ƙofar yayi sallama.




Asmah na zaune akan gado riƙe da hussaina tana feeding ɗinta a yayinda hassana ke kwance gefenta tana ta wutsul wutsul ita ma tana neman abinci, sanye take da wata doguwar riga baby pink colour daga kasan rigar tayi faɗi sosai sai gaban rigar zip ne rigace dai irin ta indiyawa mai kyau sai baƙin turban mai kyau a kanta tayi ɓul ɓul tayi kyau sosai, ji tai wata sanyayyar murya na faɗin "Assalamu alaikum" daga bakin ƙofa kuma kamar tasan muryar jin muryar namiji ce da sauri ta zare husainah daga gareta tana jan zip ɗin rigarta take ko husaina ta fara tsala kuka an cireta bata ƙoshi ba nan ta shiga rirrigata tana amsa sallamar kamin tai wani yunƙuri taji wani turare mai sanyin ƙamshi ya daki hancinta, ɗagowar da zatai ta hango Abdallah sanye cikin baƙin wando da farar riga sai zuba ƙamshi yake yana sakin mata murmushin nan nashi mai tsada, da sauri ta sadda kanta ƙasa dan gani tai yayi mata kwarjini da yawa ga wata sabuwar kunyar shi da ta ɗarsu a zuciyarta ko me yasa?, ƙarasowa yayi ya zauna gefen gadon ɗan nesa da ita da sauri tace,

"Ina wuni".

Samun kanshi yayi da kasa daina kallonta ko me yasa?, ɗaga gira yayi yace "lafiya lau ya kike barka an samu ƙaruwa".


Ɗago da idanunta tayi tana dubanshi take idanunsu suka sarƙe cikin na juna, da ƙyar ta gano muryarta wajen faɗin "lafiya lau".


"Allah ya raya mana ya ɗayyaba".


Maganar ta mata suga sosai barin ma da taji yace "Allah ya raya mana" ma'ana su cewa tai "Ameen".




Miƙo hannusa yayi ya ɗauki Hassana dake gefenta wacce ta saki kuka ɗorata yai akan kafaɗar shi yana ɗan jijjigata aiko sai tai shiru tai lamo sakkota yai yana binta da kallo farat ɗaya yaji san yarinyar na shigar shi har ɓargo, ita ko bin shi kawai take da kallo, me yasa ne take ganin kamar ba Abdallah da ta sani ba? gaba ɗaya ji take kamar yau suka fara haɗuwa duk ya canza mata gaba ɗaya duk kamaninshi sun soma sauyawa kwarjininshi har cika mata ido yake uwa uba natsuwar da ke tattare dashi dan komai a natse yake yinsa har maganar shi ma ɗai ɗai take fita sai kace ba Abdallah da take koya ma magana ba, lallai lafiya uwar jiki babu mai fushi dake ubangiji Allah ya ƙare mu da lafiya mai ɗorewa.




Ɗagowa yayi suka haɗa ido da sauri ta sauke kanta dan ya kamata tana kallonshi cewa yayi "wai ƙanwata yana ga kina ɗari ɗari da nine? ko duk lafin da na maki ne baki yafe ba? Allah a lokacin ban gane ki bane amman yanzu ai na tuna na gane ki, ki yi haƙuri pls nasan ba daɗi, nasan kin sanni sosai da naji ance da banda lafiya har gidan mu kin zauna na kuma ji duk yadda abubuwa suka faru na game da dawowarki gida na kuma yi farin ciki sosai, kuma Allah ya jiƙan mahaifinki da rahama nasan lokacin da muka rabu dake kina ƴar ƙarama sosai dan haka ba lallai bane ki iya tunani ba, a lokacin munyi sabo dake sosai dan haka yanzu bana san wannan ɗari ɗarin da kike dani ki saki jikinki dani nifa yayanki ne, ke kuma ƙanwa kike a waje na kamar Miemie".






"Hmmm ya Abdallah kenan akwai abubuwa da yawa da zuciyata ke muradin faɗa maka sai dai kash a wannan lokacin kayi nisa dani, zan adana su har tsawon lokacin da zaka dawo gareni, a hankali a hankali sai na rufe gaf ɗin dake tsakanina dakai na mallake ka a karo na biyu a rayuwata wanda har abada ba zaka taɓa gudu na ba, bazan karaya ba saboda hakan ba halin jarumai bane hakan ba halin matan kirki bane yin fatali da mijinsu a kowane yanayi, haƙiƙa kuma so, yarda da amana basu ce haka ba dan haka zan sa ma zuciyata haƙuri da dangana domin shi mai haƙuri yakan dafa dutse har yasha romonsa, ai ita gobe daɗi na da ita saurin zuwa gareta, na yadda na amince ni ƙanwa ce a gareka har zuwa tsawon lokacin da zaka daina ganina a matsayin ƙawa kawai a wajenka" ta faɗa a ranta a fili kuma tai murmushi tace,




"Ayyah ya Abdallah ba komai wallahi ƴa wuce banji komai ba kawai dai ina taya ka murnar samun lafiya ne naji daɗi sosai".






Murmushi yayi har haƙoranshi na bayyana haƙiƙa yaji daɗin kalamanta cewa yayi "nima naji daɗin ƙara haɗuwa dake a rayuwata sosai beauty, haka nake kiranki da kina ƙarama in kin mun izini zan cigaba da kiranki da haka ma yanzu".



Murmushi tayi tana ɗaga mai kai alamu "eh".


"Ok now tell me your story, a ina kike zaune yanzu ma'ana wane gari kike aure? ina mijinki yake?".





Tambayar tazo ma Asmah a bazata kuma tayi mata tsauri da yawa rasa me zata ce mashi tayi tsintar kanta tayi da faɗin "Bo..borno ne mu...muke zauna" ta faɗa cikin in ina da alama Abdallah bai lura da hakan ba dan wata tambayar ya ƙara jeho mata "wane mataki kike a karatu yanzu?".




Ammie ce ta shigo riƙe da ruwan wankan babies ɗin a hannunta ta daɗe a bakin ƙofa tana jin tattaunawarsu ganin Abdallah ya cika Asmah da tambayoyin da tasan zasu ma Asmah zafi kuma zata sha wuya wajen amsa su dan tasan Abdallah sarai da tambayoyinshi, shi yasa tana shigowa tace,




"Asmah tashi kije Dada na nemanki a ɗakinta na kai maki kunun dana dama can ki tabbatar kinsha".



Wata ajiyar zuciya Asmah ta saki tana jin daɗin shigowar Ammie da bata san yadda zatai da Abdallah da tambayoyinshi da bata san iya faɗin su ba da sauri tace "to Ammie" ta tashi tana miƙa mata Husaina dake hannunta ta fita ko kallonshi bata sake yi ba shiko kafaɗa ya ɗaga sama yana juyowa ga Ammie da ta fara ma babyn hannunta wanka ta hannunshi ya ƙara kallo sannan yace,




"Ammie ina son yaran nan sosai".




"Ai na sani" da mamaki yake kallonta cewa yayi "Ammie ya akai kika sani?".



Ɗagowa tai tana kallonshi sai yanzu ta tuna abunda tace murmushi tayi ta cigaba "ya za ai uba yace baya son ƴaƴanshi Abdallah? saboda nasan ba zaka ƙi ƴaƴanka ba shiyasa nace haka" shi kam kan shi ya kulle he just continue staring at her blankly, nisa wa tayi ta cigaba "Asmah ƙanwarka ce kai kuma yayanta ne dan haka ƴaƴanta ƴayanka ne kaima ƴaƴanka nata ne".






"Ohhh na gane, eh haka ne" ya faɗa yana kaɗa kai.










Haka Abdallah ya zauna a ɗakin ya kasa fita saboda twins, da aka gama masu wanka ma tasa su yayi a gaba suna bacci yana ta kallonsu ya rasa gane wane irin so ne yake ma yaran har cewa yayi suna na kama da shi, Ummah dai dariya kawai take mashi da ya tasa ta gaba da tambayoyinsa.






Can da yanma suka fita waje dan yo tsaraba Asmah kawai suka baro gida sai Dada, itama sunce ta rubuta abunda take so su sayo mata ta rubuta duk abunda take so harda tsarabar da zata ba su Zarah da Miemie, wani ƙaton shopping mall suka fara zuwa komai akwai, Abdallah ya tsinci kanshi da jidar ma twins kayan sawa kala kala ganin haka su kuma su Ammie suka shiga ɗaukar ma Asmah abubuwan da zata buƙata dan wanda ta rubuta duk kusan waenda zatai tsaraba ne.









Washegari da sassafe jirginsu ya ɗaga zuwa gida Nigeria sun taho da Bahijjah kasancewar sunyi hutu a inda su Dada kuma sai ana gobe suna zasu iso.














Fiamanillah♥









👸Queen bk...........

Continue Reading

You'll Also Like

134K 8.7K 55
Kallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi
3.1K 389 31
Fyaɗe aka yi miki. Shi ne abinda zuciyarta ke ƙara nanatawa. Ban san waye ba, ban kuma san dalilinsa na aikata haka a gareni ba, ni a sanina bani...
118K 5.1K 63
Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni h...
53.5K 1.9K 12
Just walk in and read, I promise u are going to be mesmerize with the emotional love story embedded in this novel.