ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 67

3.1K 234 24
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨


💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼


🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))




_Itz_queenbk @ insta gram_









__STAY AWAY FROM HURTING OTHERS,  THE HURT YOU CAUSED AND THE PAIN IS INFLICTED AND WILL COME BACK TO HARM YOU IN A DIFFERENT WAY......._
             *QUEEN BK*











PAGE6⃣7⃣











Mamaki ne ya kama Asmah jin muryar namiji ce ke sallamar dan ba kasafai take bak'i maza ba Abdallah ma ba wai ya cika kawo mata abokanshi bane kuma ko da bakʼi maza yʼan uwa sun sun zo sai dai a kirata b'angaren Ammie ko Abbah.




Kashe gas d'in tayi kasancewar ta kammala girkin, ta coridor d'in da zai sada ta da d'akinta tabi ta yadda wanda ke falo bazai ga gintanyar mutum ba, mayafi ta d'auko ta yafa sannan ta wuce falo, Abdallah ne da Mahmud zaune Abdallah rik'e da remote a hannunshi yana so ya kamo masu tashar k'wallo dan wani match zasu kallah shi kuma Mahmud ya dage yana ta bashi dariya yana ta k'yak'yatawa.



Da fara'a a fuskarta ta shigo da Abdallah suka fara had'a ido da sauri Abdallah ya had'e dariyar shi tare da shan kunu yana kawar da kanshi daga gareta, tas akan idon Mahmud bin Abdallah kawai yayi da kallo cike da tsantsan mamaki duk da dama ya d'an lura akwai abunda ke faruwa tsakaninsu tun zuwanshi dan Abdallah ya canja halayenshi towards ita Asman sam baya maganarta kamar yadda ya saba kuma bai so yaji ana maganartan, kuma bai cika zama a gidanba hasalima tun da yazo yake ma Abdallah mitar suzo b'angarenshi amman yak'i yadda sai yau, yau d'in ma wayau ya mai sannan ya yadda,  shi dai abun mamaki yake bashi dan bai tab'a kawo hakan a ranshi ba amman yaci alwashin koma meye a tsakanin nasu zai daidaita shi da yardar Allah, Amsah ce ta katse mashi tunani da fadin,


"Haba ya Mahmud ai ni nayi fushi dakai sai yau kaga damar shigowa nan tun zuwanka, sai dai mu hadu a waje ko a bangaren Ammie ko?".




"Haba sis wallahi ba haka bane kin dai san halin mutumin naki ko? To sai yau ya gayyaceni shiyasa" ya fad'a yana satar kallon Abdallah, shiko gogan kamar ma ba ya falon dan hankalinshi kacokan nakan wasan kwallan kafar da ake nunawa a gidan talabijin.





"To shikenan ya mahmud kun tashi lafiya?".



"Lafiya k'alau ya jarabawa kun gama Waec ko? ".



"Eh, jarabawa Alhamdullilah".



"To Allah ya taimaka yabada sa'a, wai shin dakata ma tun kafin mu shigo nake jin k'anshin dad'i mun shigo falon kamshi yana nema ya cika mana ciki, da fatan da rabona dai a ciki"




"Aikuwa ya Mahmud dambune na girka maku" ta fad'a tana duban Abdallah dan tasan yana san dambu kamar tasan ko za'a rina tana fad'ar dambu ya juyo ya kureta da ido yana had'iye miyau can kuma ya kauda kai yaa had'e fuska kamar bashi ba, ita abun ma dariya yabata ta dai hadiye gudun kar ta b'allo ruwa.



Ya Mahmud ya amshe da fadin "yauwa kaji bayani nan a zubo mana shi nan" shima ya fad'a yana kallon Abdallah.





Kitchen ta koma ta jera duk abunda ta dafa kan tray sannan ta koma falo saman tebur d'in da ke tsakiyar falon ta dire a hankali, plate biyu ta jawo ta zuzzuba had'ad'en dambunta da sai fitar da daddad'an kamshi yake, duk ta lura da yadda Abdallah ya zuba mata ido a wayance, plate d'aya ta tura gaban Mahmud tare da cemai ''bisimillah'' yana kai loma d'aya yace,

"Uhm uhuh tab cancad'i amman ko duk wanda bai ci dambun nan ba an bar shi a baya".



Ya fad'a yana kallon Abdallah da ya kura mashi ido yana had'e miyau, da sauri ya tab'e baki yana jan siririn tsaki, zamewa yai akan kujera da yake zaune ya kwantar da kanshi tare da lumshe idanu kamar mai bacci amman idon shi nakan lomomin da Mahmud ke sawa a baki yana zuba santi.






Ita ko Asmah murmusawa tayi tana k'ara mika ma Khaleel milk shake mai sanyi da ta zuba a kofi d'auka yayi yasha ai shiru kuke ji nan ya dukufa aikin zira ma ciki dan ya manta ma dasu a fallon dan dama sun d'ebo yunwa shida Abdallan, a hankali ta tashi ta jawo k'aramin table din dake tsakanin kujeru ta ajeshi gaban Abdallah kasancewar babban tebur d'in yafi kusa da Khaleel shi Abdallah ba zai iya cin abincin kan table d'in ba face ya takura da yake falon ba laifi akwai girma, nashi plate d'in da ta zuba mashi ta d'ora kan tebur d'in tare da milk shake d'in shima sai da ta kalleshi har yanzu idonshi na kan Khaleel dake ta zuba lomominshi hankalinshi kwance😀 sai dai in baka luraba bazaka fahimce idanun Abdallan abude suke ba dan ya kwanta sosai ne kan kujerar sai ya kwantar ta kansa ya lumshe ido Yana ta kallon bakin khaleel, dariya taso k'wace ma Asmah da k'yar ta danne gudun kar ta taso zaune tsaye, a sanyaye tace



"Bisimillah ya Abdallah ga naka".







Ta fad'a tana k'ara tura masa plate d'in kusa dashi, sai dai ko motsawa bai ba, taga kuma yadda ya kalla plate dʼin ya d'auke kai, har kusan minti biyar bai ma yi alamun motsawa ba, har tana niyar tashi sai Kuma wata zuciyar tace bari dai ta zauna taga k'arshen wannan dramar.





Tas Khaleel ya cinye har ta k'ara mai sai da yaji yayi nat sannan ya sarara ya d'auki tissue yana goge baki fad'i yake,


"Kai wannan danbu haka ai duk wanda bai ci ba an barshi baya wallahi" ya fada yana satar kallon Abdallah, toshe kunne Abdallah yayi Yana fadin "oho ni dai banji ba" can kuma kamar an tsikareshi ya tashi zaune ya d'auki spoon ya d'ebo ya Kai dai dai bakinshi sai ya tsaya yana ta kallon dambun, su dai da ido suke ta bin shi wata k'ara yayi wadda ta haddasa ma Asmah durk'ushewa daga tsugunnen da take, jefar da spoon d'in yayi tare da fatali ta plate din gabanshi ya fadi kasa Yana fashewa bugun bakinshi ya shigayi Yana fad'in "Wallahi banci ba kar ki soya ni Allah banci ba" take zuciyar Asmah tai wani waje duk da abubuwan sun zo mata a baibai tana bukʼatar ta zauna tayi warwara dan fahimtar sakʼon da zuciyarta ke son isar mata, ita dai tasan tabas banza bata kai zomo kasuwa.





A fusace ya tashi yayi kan Asmah ya dʼaga kʼafa zai yi ball da ita da sauri Khaleel ya rikʼo hannunshi Yana fadʼin "miye haka Abdallah?" wani huci ya saki Yana fisge hanunshi daga rikʼon da Khaleel dʼin ya masa ya wuce dʼakin shi Yana bugo kʼofar da masifar kʼarfi, ai Asmah tuni ta rikice ai bata san sadda wani marayan kuka ya subʼuce mata a ranta take jinjina eh lallai abun ya girmama ita dai tun saninta da Abdallah bata taba ganin wannan yanayin nashi ba har kuwa lokacin da basa shiri tuni zuciyarta ta cunkushe da tunani kala kala ganin ta kasa warware dʼaya tuni ta kʼara kʼaimi akan kukan da take rairawa dan ita shaf tama manta ta Khaleel a falon.




Dafe kanshi yayi yana jin kukanta har zuciyarshi dan ta matukʼar bashi tausayi dama haka Abdallan ke mata ne?, shi yama rasa yadda zai fara lallashinta, a hankali yayi gyaran murya wanda yadʼan fargar da Asmah da zamanshi a wajen dan haka ta tsagaita kukan duk da ta kasa hadʼiye shi gaba dʼaya, sai da ya shafa goshinsa da tafin hannunshi kana cikin sigar lallashi yace,


"Sis dan Allah kiyi hakʼuri kiyi shiru muyi magana".


Jin hakan bata San sadda ta hadʼiye kukan ba tana share kʼwalla da habʼar gyalenta ba, kanta na kʼasa tana wasa da yʼan yatsunta yadda tayi ne ya sa shi gane cewa ta natsu ne dan jjin me zai fadʼa matana, sai da ya kʼara gyara murya sannan ya cigaba,



"Kusan a tare aka haife mu da Abdallah sai dai shi yabani wata dʼaya da yan kwanaki, mahaifiyata yayar mahaifin Abdallah ne hakan yasa muke cousins dani dashi, lokacin da aka tashi yayen mu duk Inno ce ta karbi yayenmu wadda ita kakace a gare mu kuma a halin yanzu ta rasu".

Da sauri Asmah tace "ubangiji Allah ya jikʼanta da rahama" tana kʼara maida kanta kan zoben hannunta wanda Abdallah ne ya bata tana jujjuyashi a yatsanta.


Sai da ya jinjina kai sannan yace "ameen summa ameen" ya cigaba Yana me kʼara gyara zamansa "a wannan lokaci duk da kasancewar mu yara kʼanana ne amman ba kʼaramin shakʼuwa bace ta shiga tsakani da Abdallah, to kullum muna tare muci tare ayi mana wanka tare mu kwanta tare mu tashi tare muyi wasa tare, daga baya ma sai muka tsiri wani abu yadda kasan tagwaye in wannan na kuka sai dʼayan ya dʼauka sai su Inno sun lallashe mu gaba dʼaya sai in duka mun yadda muyi shiru sannan muke shiru, a wajen su Inno ko sun ji dadʼin yadda muke San junanmu danshi papi (kakanmu) har Hassan da hussaini yake kiranmu, sai da muka kwasa shekara dʼaya cif a gidan kakanninmu a lokacin Kuma mun kʼara wayau sosai Dan mun cika shekara uku a duniya duk wani shakʼuwa ta kʼaru sam ba'a jin fadʼan mu, labari ya canja ne lokacin da iyayenmu suka zo dʼaukar mu anan muka tubure mu sam ba musan da wannan maganar ba, ba wanda zai rabamu duk da su Inno sun so a bar masu mu kawai su cigaba da rikʼa mu ba musan dai me ya faru ba sai momma (Aunty Uwani mahaifiyar Mahmud) ta kwashe mu muka wace katsina gidanmu, watanmu biyu Kuma cif a kazo aka tafi da Abdallah lokacin munsha kuka da zazzabi, iyayenmu suka shiga lallashi bayan dʼan wani lokaci Kuma muka ware, daga nan muka shiga makaranta sai lokacin hutu Abdallah kanzo gidanmu koni naje, tunda Kuma aka haifi Miemie labari ya canja dan duk hutu ina nan dan tunda na kʼyallara ido na ganta naji ina matukʼar san babyn a lokacin iyayenmu sun sha ko danni kadʼai ne a gida banda kʼani ko kʼanwa saboda ni kadʼai Allah yaba ma iyayena sai suke zaton ko wannan kadʼaicin ne yasa nake son baby Miemie, abu yakai ko Abdallah baya nan in dai Miemie na nan zan zauna a gidan nan bani da wata damuwa dan lokuta da dama zan zo shikuma yace dole sai Damaturu zashi wajen ki, in akai kʼokʼarin fahimtar dashi nazo amman sai yikʼi ganewa dole suke barin shi dan Abdallah jarababbe ne in ya nace sai yayi abu to dole abarsa, sai suke barinshi ganin nima dʼin bana ta tashi a haka rayuwa tai ta gungurawa har yazo lokacin da kuka bace dake da Abbanki hakan ba kʼaramin tashin hankali bane ga dukan yan uwa barin ma a wajen Ummanki da Abdallah, ganin an rasa gane kan Abdallah dan dama asali shi ba mai magana bane sosai amman alokacin abun ya koma sai sdai kuyi ta kurame dashi daga uhm sai a'a, ko a makaranta ya kasa wani hobʼbʼasa akasin da da yake ja gaba Kuma sahun farko, ganin damuwar tana so ta masa yawa gashi yaro yasa iyayenmu yanke hukunci hada mu su tura mu karatu London wajen kʼanwarsu dake aure a can (Aunty Mami) dan a lokacin yafi sakewa dani, a lokacin Kuma duk muna da shekara sha dʼaya Kuma dai dai da zamu shiga jss 1 kenan haka muka koma can da karatu da zama ma, har lokacin bai manta dake ba dan in kaji ya zauna yana zara magana to akan beauty ne duk da lokacin ya dʼan sake sosai ya dawo dai dai, kullum burinshi ya gama karatu ya koma niger yaga beautynshi dan a kullum Aunty Mamy ce mashi take ai kina Nigeria kina jiransa amman bazai iya ganinki ba sai ya gama karatu lokacin ya kʼara girma ita ma beauty ta girma sai ya sata a motar da yake kira ta beauty ya tukʼaki, ba kʼaramin dadʼi labarin yake sanya shi ba, a hankali yana girma da wayo duk ya fahimce labarin kʼanzon kurege ne ake shirya masa, a hankali kuma abun ya fara fita a ransa ya daina nuna damuwa ta zahiri sai dai ina da yakʼinin a kwai ta badʼini, a haka muka cigaba da maida hankalinmu a karatu har Allah yasa muka kammala secoundary school, lokacin da muka dawo gida cike da murna ko da na tarar da Mimi  ta girma sosai dan lokacin tana primary 2 nan tsohuwar zuma ta taso naji ina matukʼar kʼaunarta har kʼokʼon zuciyata duk da daga farko ban san me zuciyata take ji akanta ba dan nasha yan uwantaka ne kawai sai daga baya na gane zallar kʼauna nake mata kuma ina sonta ne da aure, ban fadʼa ma kowa ba na cigaba da rainan sonta a zuciyata duk da ita kanta uwar gayyan bata san wainar da nake toyawa a zuciyata ba, ra'ayin mu dʼaya da Abdallah wajen karantar sojan ruwa duk da anso Abdallah ya karanta Architecture ganin ya iya zane sosai Kuma yana son zanen amman yace sam shi sojan ruwa yake so haka mu ka tafi karatu tare muka Kuma gama tare, bʼangaren ni da Mimi kuwa ganin ta girma sosai zata iya dʼaukar duk wata magana da zan gaya mata dan haka na warware mata adanannen sirrin dake zuciyata, ban sha wata wahala ba na sami tata zuciyar ko dan hadda yarinta a lokacin ban dai sani ba, sai dai muka bar ma zuciyoyin mu sirrin soyayyarmu ba wanda muka sanar Abdallah ma da kanshi ya dʼagomu, bayan kammala karatun mu Abbah ya dage akan sai mun fiddo da mata munyi aure a cewar shi mun girma har zamu gandʼame ba muyi aure ba, Niko lokacin na kasa shaida ma kowa tsakaninmu da Miemie ganin har yanzu yarinya ce dan lokacin ta shiga js2 bʼangaren Abdallah Kuma bama a magana danshi kwata kwata baya kula mata ko kadʼan, haka Abbah yasha surutu har ya gaji ba wanda ya fidda mata cikin ni da Abdallah duk da jari da filaye da yawa da Abbah ya bar bamu mu juya dan mu rike iyalinmu in munyi auren, a haka har posting dʼin mu na farko ya fito nan Abbah ya dage da cewa muna dawowa daga posting ba sauran dʼaga kʼafa mu fiddo da mata ko shi da kansa zai fidda mana ya mana aure dukkanmu muna cikin tension barin ma ga Abdallah dan mun san Abbah dagaske yake, har gwanda ni azatona inna fadʼa masu wacce nake so may be zasu iya daga mun leg har zuwa Miemie ta gama school, bʼangaren Abdallah kam sosai ya tada hankalinshi dan acewarsa mutum ba wani girma ba amman ace sai yayi aure dole niko dariya kawai nake, bayan mun tafi ne dukkan kʼaddara ta riga fata hatsarin Abdallah ya bijuro bayan mun dawo Kuma hankali a tashe ba'a kʼara bi takan zancen ba, bayan an dadʼe kuma Abbah ya sarara mun dan na lura kamar ya fuskanci akwai wani abu a tsakanina da Miemie duk da bai tunkaren da batun ba shiyasa bani da tabbas ko ya sani, to kinga duk kusan rayuwar Abdallah tare mukayi ko?".


Dʼaga masa Kai tayi tana share kʼwallan dake zuba a kumatunta, jinjina Kai yayi sannan ya cigaba "to kinga ba wanda zai fadʼi maki halayen Abdallah sama dani ina da yakʼinin yadda nasan Abdallah ko su Ammie da Abbah bazasu fadʼi wani halayen nasa ba" nan ma dʼaga masa kai tayi tana cigaba da zirarar da kʼwallan da ta rasa dalilinsu, wata ajiyar zuciya yayi ya cigaba da fadʼin "asalin halayen Abdallah, Abdallah mutum ne natsatstse Wanda sai an tona sosai kan a samu natsatstse irinsa, kamili ne ajin farko Sam bayada shiga harkar da bata shafeshi ba, a bʼangaren surutu kuma mutum ne da magana bata cika damunshi ba dan sai kai magana gomo bai ansa dʼaya ba ko yai ta binka da kadʼa kai, yana da sarauta a jinin jikinshi dan ya fusgo dangin Ammie ne sosai dan in yana wani abun sai kasha shene yarima mai jiran gado, yana da tsantsan addini Kuma sam baya kula mata yana da hankali da zurfin tunani uwa uba  kʼokʼari da fasahar da Allah ya zuba masa a kʼwakʼwalwa duk wannan kadʼanne daga cikin halayen Abdallah na ainihi, sai dai tun bayan hatsarinsa ya koma yin abu kamar yaro yata zara magana kamar yara, in kin tambaye sa bai san jiya ba baisan yau ba baisan gobe ba balle Kuma ina ya dosa rayuwarshi kawai kara zube take, Yana matukʼar tsoro kamar dai yaro wata sa'in ma yafi yara dan kome kika tsoratashi akai shikenan ya zauna sam bayada tunanin manya da zai iya banbance hanya mai kyau da akasinta ba, a duk turbar da kika dʼorashi akai dai dai ne agunshi, shi yasa za'a iya saurin cutarsa, a halin yanzu in bai budʼe baki yayi magana ba kaganshi daga zaune sai ka rantse mutum ne mai cikakken hankali sai dai in yayi magana kaji ko ya aikata wani abun sai kuma in cinwonsa ne ya tashe wanda yake hadʼewa da zuciya dan a zahiri Abdallah mutum ne mai zuciya da naci akan abunda ya kʼwallafawa ransa abubuwa da yawa dangane da halayensa na yanzu ba sai na fadʼa maki ba dan nasan ma zaki fini sani akan wannan, ba komai bane dalilin da yasa na dauko maki wannnan labari ba illa iyaka saboda dalilai biyu na farko ina son ki kʼara sanin waye mijinki Kuma ki kʼara hakʼuri da juriyar zama dashi dan nasan no condition is parmanent da yardar Allah wannan abu duk sai ya zama tarihi na biyu Kuma akwai wani babban nadʼi cikin lauje dangane da wannan ciwon nashi, ina ga Allah ne ya kawo warwarar sirrin nan dan ya kawo karshen wahalar da bawan Allah nan yake sha, akwai wani aiki da nake son muyi mai matukar tsauri gaske dan haka ina so ki zama jaruma Kuma ki adana jarumtar ki dan shirin shiga filin daga, akwai abunda nake so mu tattauna dake da yawa Kuma mahummi amman kafin nan ina so na baki wani assignment ina so ki sama Auntyn yara ido sosai daga nan har zuwa kafin in tafi zamu zauna dan in warware maki komai yadda zaki gane, sai dai akwai  sharadʼi biyu akan wannan aikin da na baki na farko bana son tambaya na biyu Kuma ya zamana sirri a tsakaninmu kar ki fadʼa ma kowa daga ni sai ke dole sai mun bi wannan ka'idojin in har muna son mukai ga gacci ...............



*A/N*

To msu karatu.......
Me kuke tunanin yake ran Mahmud?
Me yasani?
Wani aiki ne mai tsauri da Khaleel yake son suyi shida Asmah?
Meye dalilin Mahmud nasa Asmah lura da Auntyn yara?.

Well amsoshinku ku bi yoni mu cigaba da gashi suya sai ran sallah🤩🤩...



Love y'all💋💋❤.

Fiamanillah
👸🏻Queenbk....

Continue Reading

You'll Also Like

340K 17.4K 79
"You have a single bullet in your guns, you can kill the person in front of you or shoot the person aiming at you, it's your choice." When top female...
1.5K 168 22
saukakekken hanyar shiga,Amma naiman hanyar fita it will be diely.......WHEN IN NO WAY OUT
3.9K 187 11
Labarin wata ba fulatanar budurwa mai suna FANTA! Da matashin saurayin ta MAHBUB dan birni😉 Written by MISS XOXO and NAFEE ANKA😍 (2016...)
84.3K 5K 58
Dr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a h...