ZAN SOKA A HAKA

Od queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. Více

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 62

4.3K 274 12
Od queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨









💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
*_NA_*
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *_QUEEN BK_* 👸🏼










🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* 📝
((Gidan   zaman  lafiya  da amana    insha    Allah🤜🏻🤛🏻))

















Page 62









Can ma cikin gida ba labarin dake zagayawa bayada na Asmah da Abdallan kowa kuwa ba ƙaramin mamaki da al'ajabi abun yake bashi ba, haka taron ya sheda jama'a wanda ya haɗa da waenda suka zo taya murna da ƴan gulma da tsegumi da masu yamaɗiɗi da magana cikin gari, anci an sha kalar wacce rai ke so, Mai martaba da kansa yayi addu'a sosai bayan saukar ƙur'ani da akai, haka aka rinƙa kwantar da shanaye da raguna nama kam sai kaci ka tafi dashi, Asmah kam ranar taga dangi kamar zasu fashe dan har mutan Katsina ƴan uwan mahaifinta haka suma sukayo taron dangi dan zuwa ganin ƴa da kuma ƴar uwartasu wacce take ɗiya ɗaya tilo gun Muhammad itako a ranar bata san adadin kyautar data samu ba, haka taro ya watse cikin farin ciki da kewar juna tsakanin ƴan uwan kowa sai sam barka yake.






Bayan kwana uku gidan shiru kamar ba shi bane a ciki da mutane cundum ba, dan duk an watse hatta su Aunty Urwa duk an tafi su Ammie ne kawai suka rage dan su Auntyn yara ma da suka zo tare da Abbah tuni sun juya, Su Yabi kam da Aunty Nafi basu daɗe da juyawa bama dan kwanansu huɗu alheri kam ba kallar wanda basu sha ba da kuma zasu tafi goma sha tara ta arziƙi su Naty da Mai martaba suka ƙara haɗa masu haka suka tafi suna santi da sam barka, cikin kwanakin nan kuwa Asmah kwata kwata taƙi yadda su haɗa hanya da Abdallah dan da ta ganshi zille mashi take dan tasan tas zai kunyata ta a bainar nasi, duk kuwa da lura da tai dashi kan yana matuƙar son ya ganta amman sam bata bashi dama ba kullum ko da dare yayi zata shige cikin ƴan uwa ta shaƙi baccinta ashe bata san hakannan da tayi ba ƙaramin cima Abdallah tuwo yake a ƙwarya ba wannan kenan.






Washegari da sassafe su Ammie suka wuce Kano ya rage daga Abdallah sai Asmah sai ko mutan gida, ranar Abdallah wuni yayi a sashen Naty amman sam bai kula Asmah ba ko kaɗan dan shi ya ɗau fushin abunda tai masa ɓangaren Asmah kam abun har tsoro ya fara bata dan da fari tasha wasa yake mata amman ganin yayi kicin kicin da rai ya shareta dan ko magana tayi baya amsa mata kuma Ummah a lure take dasu tun safiyar yau ɗin.





Misalin ƙarfe 8:20 Asmah ce zaune kan sallaya tana lazumi bayan tagama sallar isha'i ta kuma bi da nafilfilin data saba bayan ta shafa addu'ane ta taso cikin murmushi tana duban Ummanta dake ta gyara masu kayan cikin akwatinsu a wardrove ɗinta dan gefe ɗaya ta ware masu ƙarasowa tayi wajenta tana faɗin "sannu Ummata amman ba nace ki bari zanyi aikin ba bana so inga kina wahala Ummah ki bari na ida dan Allah" ta faɗa tana karɓe kayan dake hannun Ummah.



"A'a ɗiyata ki barshi bani nace na hutar dake ba, oya no more words jeki falo ki fara cin abunci gani nan isowa" ta faɗa tana maida abunda Asmah ta karba hannunta, da sauri Asmah ta riƙe mata hannu sai da ta  marairaice kana tace,



"Ummah dan Allah ki barni nayi albarkarki nake son insamu" shafa mata kumatu tayi tare da faɗin,

"Yauwa ƴar kirki Allah ya maki albarka i maza ki gama ni bari na gyara wannan jibgin kayan da aka babbaku" ta faɗa tana komawa side ɗin ɗakin da aka tara alherun da Asmah da Abdallan suka sassamu ɗin, Naty ce ta shigo ɗakin tare suka gyara kayan da Ummah duk wasu envelop na kuɗi suka ware su guri guda dangin su kaya ma haka suka kimtsa su cikin wani jibgegen akwati sai sauran ƙwarerayi, nono, manja da man gyaɗa da suka rage suka ajesu store kamin su Asmah su tashi tafiya duk kuwa da mafi yawan kayan sun jibga ma Ammie ta wuce dasu, bayan sun kammala ne suka isa falo nan suka iske har baba gaje (babbar kuyanagar Naty) ta jera masu dinner ɗinsu, Naty ta jawo ƙwaryar fura zata fara damu dan ita ta bada izinin kar ariƙa dama mata fura ta fi son ta dama da kanta, da sauri Asmah ta karɓe tana faɗin ta barta zatayi, Naty tai murmushi tana faɗin "oh ni wannan kishiyar tawa bata so taga ina motsa jikina anya kuwa ko dai zagon ƙasa kikai mun bansani ba kin ƙwace fada kin banni da ɓara ayaba?"duka suka sa dariya Asmah tace,



"Nifa tsohuwar nan ba gane maki nake ba yau kice mun kishiya gobe in abun ya kaɗo maki kice mun ƴar jikalle to ni ki zaɓa ɗaya a ciki dan insan wani babi nake a kuma wace kusurwar kika ajeni".



Dariya Naty tai tana faɗin "yau ina ganin walele giɓin takwaru ai gaba ɗaya na haɗa na baki sadda kishin ya motso kishiya kike sadda kuma tsokanar ta taso jikalleta kike".



Kafin Asmah tai magana sukaji sallamar Abdallah bayan ya shigo, da hannu Ummah ta nuna mai kusa da Asmah tana faɗin "Habibi zo ka zauna nan inji damuwarka kwana biyu ban gamsu da yana yinka ba".




Ƙarasowa yayi ya zauna inda ta nuna masan gaf da Asmah, a hankali ta ɗago idanunta cikin son su haɗa ido caraf kuwa idanunsu ya sarƙe cikin na juna sun ɗauki tsawon sakonni biyar suna kallon juna kafin Abdallah ya yanke kallon ta hanyar kawar da kansa gefe yana kallon Ummah hannunta ya kamo yana faɗin "habibty yunwa nake ji" kan tayi wani yunƙuri har Naty ta miƙo masa plate ɗin da ta gama jera masa kalaluwan abincin nan ya shiga ci ko sake waigen Asmah baiba, itako Asmah sake da baki take kallonsa da ƙyar dai ta saki ranta ta koma kan damun furarta cike da tunani kala kala bayan ta gama ne ta jawo ƙaramar ƙwarya ta zuba masa tare da tura masa furar gabansa tana faɗin "ya Abdallah ga furarka" in ƙwaryar data aje ta tanka to tabbas Abdallah ma ya tanka duk kuwa ba wanda ya lura da hakan sai Ummah itace ma ta ƙara matsar mai da ƙwaryar tana faɗin "Habibi kasha furar mana" sai lokacin ya kalli furar tare da faɗin "to" a taƙaice.



Haka suka ci abinci jefi jefi Naty na magana Asmah na amsa mata duk da gefe ɗaya na zuciyarta na kan sauyin  lamarin Abdallah, lokacin da taga ya fara shan fura ba ƙaramin daɗi ta tsinta kanta daji ba har rasa dalilin hakan tayi.




Tana gamawa ta wuce ɗaki dan ta gaji da halin ko in kulan da Abdallah ke nuna mata, wayarta ta jawo ta hau whatsapp ta fara chatting da su Zarah da Mimi domin group ɗaya suka buɗe ma kansu me taken "The best three ever" nan taga har sun tutturo mata note ɗin da akayiyyi makaranta kamar yadda suka saba sannan taga lesson teacher ɗinta ta turo mata Assignment ɗinda zatai yau itama ɗin kamar yadda suka saba, sai da suka sha surutunsu sosai da su Zarah tare da labarin makarnata kana Asmah ta sauka nan ko ta ɗauko litittafanta sai da ta gama Assignment ɗin har ta fara kwakwafar note ɗin taji an turo ƙofar an shigo Umma ce lokacin har goma tayi fira ta ƙare kenan, murmushi tayi tace "barkadai ummata".






Da murmushi ta iso gareta tana shafa kanta bayan ta zauna tace "me ɗiyar tawa take karatu ake tayi?".


"Eh Ummah ban ma fara ba tukun note nake kwafa".

"To madallah Allah ya taimaka yanzu dai ba wannan ba ki bari gobe kya ƙarasa maza tashi kije kiyo wanka" ta faɗa tana rufe mata littafi tana gyara mata su saman bedside.

"Toh Ummah" ta faɗa
bayan ta ɗaura towel nan ta shige bayi, da murmushi kawai Ummah ta bita, bayan ta fito ne Ummah tace ta shafa mai da hoda sai ta ɗan zizara kwalli, haka Asmah tayi duk da tana mamakin mai yasa Umman nata tasa ta yin hakan sai dai bata mata gardama ba duk tayi, wata ɗoguwar rigar bacci har ƙasasai dai sharara ce peach colour Umma ta bata tace ta saka da kanta ta gyara mata gashi ta sharce shi tas ta ɗaure mata shi a ƙasa ta nannaɗe yadda zata ji daɗin bacci kallanta tai ta cikin madubi tace "masha Allah ɗiyata kinyi kyau ina zuwa" ta faɗa tare da fita ɗakin, Naty ta shigo cikin shirin baccinta kai dubanta tai wajen Asmah tana faɗin "ke ƴannan yau bamu gayyar kwananki anan maza ki wuce ɗakin mijinki in banda shaƙiyancin yarorin zamani har yaushe zaka bar mijin ka shi kaɗai bayan kuna tare".



Asmah ta marairaice fuska kamar zatai kuka sai yanzu ta gane shirin da Ummah ke mata, Naty ta cigaba " kar kiyi wani kalar tausayi gwara ma ki tashi ki tafi tun muna mu biyu" ta faɗa tana rashewa saman gado tana mimmiƙe jiki, Ummah ce ta shigo riƙe da wata ƙaramar kwalbar turare sai da ta feshe Asmah tas dashi turaran ko ba ƙaramin daɗi gare shi ba har Naty sai da tai maganar daddaɗan ƙamshin ita kanta Asmah ba ƙaramin burge ta yayi ba, Ummah ta zira mata wata doguwar hijabi tace "tashi maza ki wuce ɗakin mijinki" ba yacce Asmah ta iya dole ta tashi tana masu sai da safe.




Har bakin ƙofar sashen Naty Ummah ta rakata tana faɗin " kar inji kar in gani mijinki ya ƙara fushi dake kuma kiyi duk yadda zakiyi kiga kin kawar da fushin da yake dake a yanzu, Allah ya maki albarka jeki".



"To Ummah sai da safe".

Hannu kawai Ummah ta ɗaga mata tare da turo ƙofar, Asmah tsaye tayi tana mamakin ya akai Ummah tasan da fushin da Abdallah keyi da ita take wata zuciyar ke cemata "yadda yake shareki a gaban kowa akasin yadda yake maki a da kina tsammanin bazata fahimce komai ba game da haka?" iska ta furzar daga bakinta tana shafa goshinta a ranta take faɗin "ohh ni Asmau wallahi dama su Ummah sun barni na cigaba da kwana dasu danni kunya zan riƙa ji wallah".




A hankali kuma ta fidda tunanin komai a ranta ta fara takawa zuwa ɗakinsa, can bayan ɓangaren Mai martaba ne wani babban ɗaki guda ɗaya a wajen, tana isowa bakin ɗakin ta sauke ajiyar zuciya ta tura ƙofar a hankali ta shiga tare da sallama.




Zaune yake bisa gado yana ta latsa wayar sa, ɗagowa yayi don ganin waye ya shigo karaf suka haɗa idanu da sauri Asmah ta sakar masa murmushi, da sauri ya taso kamar zai rungumeta sai kuma taga ya juya tare da komawa inda yake yana cigaba da abunda yake abaun ma dariya ya bata cikin dariya ta isa inda yake tare da zama kan bedside ɗin kusa da shi yadda zasu fuskanci juna da kyau a hankali ta kama cinyar hannunsa tana kwantar da kanta saman kafaɗar shi sannan tace "haba babyna mai na maka ne zaka ɗau fushi dani kuma kasan bana iya jurar fushinka gareni koda ko na sakon ɗaya ne mijina abun alfahari na ka taimaka ka faɗa mun laifina gareka ko zanyi gaggawar roƙar yafiya daga gare ka tare da making sure ban ƙara kwatanta kalarsa ba ko da wasa kaji mijina?" ta faɗa tana zare wayar hannun sa ganin bama sauraronta yake ba, kawar da hannunsa yayi daga gareta tare da tashi  yana shigewa bayi Asmah kam tace eh lallai abun ya girmama tana ji ya gama wanka ya fito yai shirinsa ko kallonta bai ba ya ƙara hayewa gado ya juya mata baya wato tayi da bayansa ko?  ganin da tayi itama inba shareshi tayi ba ba zasu shirya ba dan sarai ta san halin Abdallah kamar yunwar cikinta tasan in eh ne to tabbas eh ne haka ma in a'a ne to ba sauyi ta san ko ba daɗe ko ba jima sai ya dawo mata sai dai tana fatan ya dawo matan da wuri dan itama bata iya jurar fushinsa da rashinsa a kusa da ita sam, taɓe jajayen lips ɗinta tayi ƙasa ƙasa take faɗin "uhhmmmn wahalar da rai fushi da maƙoci zama kayi ka gama ka dawo saiti" toilet ta shiga ta cire bra ɗinta dan ba ta iya kwana da ita sannan ta dawo ta kashe wutar ta kwanta ɗayan ɓarayin tana kallon shi da yake ɓarayinta yake kallo yadda ya rufe idanunshi ba ƙaramin burgeta yayi ba yadda gashin idanunshi sukai zara zara gana yalwataccen  girarshi kam kamar an zana ba abunda yafi tafiya da hankalinta sai sajenshi da ya kwanta luf luf a gefen fuskarsa, Allah na gode maka da kasa na zaɓi Ya Abdallah a matsayin mijina da nasan zan dauwama cikin ƙunci da nadama haɗeda da nasanin rashin sa har abada oh ni Asmah ina zan kai ɗumbin so da ƙaunar da ya Abdallah ya nuna mun tun ban san meye duniya ba ban san meke mun ciwo ba, tashi tai zaune ta warware gashinta dan ya takura mata dan tafi gane ta sake shi in zata kwanta tuni ko ya sauko mata har ƙugunta hannu tasa ta maida shi baya tana maƙala wanda ke damun fuskarta a bayan kunne sannan ta koma ta kwanta matsowa tayi daf da shi har suna shaƙar lumfashin juna cikin wata siririyar murya kamar mai raɗa tace "ya Abdallah na fa kasa bacci" a hankali ya saki wani nishi kamar mai bacci haɗe da juya mata baya wato karma nayi baccin kenan yake nufi shiba damuwarsa bace ko? tambayar da Asmah kema zuciyarta kenan, a haka tai ta juye juye tana girgiza kai dan ta kasa bacci, can har bacci ya ɗan fara fizgarta taji haske ya gauraye ɗakin buɗa ido tayi tana kallon Abdallah dake tsaye hannunshi kan switch ɗin wutan, cikin mamaki ta tsaya tana kallonshi gani tayi ya fara takowa yana zuwa saitinta sai da yazo gaf da gaton taji yace "Beauty zo nan" ya faɗa ya na nuna mata kusa dashi, da hannu tai masa alamar "meye?" ganin ya ƙare ɗaure fuska sam ba wasa a tattare da fuskar tasa yasata tashi tana turo baki ta isa wajenshi, kama cinyar hannunta yayi yana matso da ita daf dashi har tana jin bugun zuciyarshi idanunta ya tsaya dai dai faffaɗar kafaɗarsa dan ya fita tsawo, hannunsa ya ƙara sawa ya kamo haɓarta tuni idanunsu suka sarƙe cikin na juna sun ɗauki tsawon sokon goma suna kallon juna kafin Abdallah yasa hannunshi cikin gashinta tattaro shi ya shiga yi duk da ya kasa kamawa sai zame masa yake dan gashinta ga tsawo ga yawa ga kuma santsi da ƙyar ya iya tattara shi tsakiya yana naɗewa duk da ya bar jelolin gashin da yawa suna reto, cikin zuciyarta take cewa to meye na kama mun gashi mai ruwansa dashi kuma, kamar ya shiga zuciyarta kuwa ji tai yana faɗin "gashinki ya hana mun bacci sai shiga mun baki yake yana lulluɓe mun fuska " take ta tuno juye juyen da tai tayi yana gamawa ta taɓa inda ya ƙulle mata shi a tsakiya taɓe baki tayi tare da komawa tana kwanciya kan gado ta side ɗin damarta ta kwanta wanda hakan na nufin ta bashi baya shima kashe wuta yayi yai kwanciyarsa tuni bacci ya sure Asmah, ita ta fara tashi da Asuba amman sai gani tai Abdallah duk ya maƙalƙale ta dan ƙafar shi ɗaya na tsakankanin ƙafafunta kanshi kuma nakan ƙirjinta a yayin da hanunshi ɗaya ya zagaye  ƙugunta sosai tayi mamakin yadda suka koma haka, murmushi kawai tayi dan tasan rigimar Abdallah ce kawai ta motsa na fushin da ya ɗauka da ita, sai da ta sumbace goshinsa sannan ta janyesa daga jikinta ahankali ta faɗa bayi sai da tai wanka sannan ta ɗoro alwala ta fito har suka kusa cin karo da Abdallah zai shiga bayin, bashi waje tayi ya wuce sai da ta gama kimtsawa har tasa kaya sannan aka tada sallah nan ta jona sallar dan masallacin dake  cikin gidan ana jin komai tas, koda ta gama bata koma bacci ba sai tai ta hailala dan koyi da Annabi Muhammad (SAW).






Koda gari ya waye bayan ta shiga ɓangaren Naty sai tai ta ɗari ɗari sai da Ummah ta mata tatas tana faɗin ai ita ba sirikarta bace mahaifiyarta ce sannan ta saki jiki tana ba Ummah haƙuri, haka rayuwa ta cigaba da gungura masu cikin farin ciki duk kuwa da Abdallah bai sauko daga dokin fushinsa ba ita kuma ta tattara shi ta aje shi gefe guda dan itama lokacin bata jin daɗin jikinta tana ta fama da ciwon kai ƴan kwana biyun nan kuma bata faɗa ma kowa ba sai ta samu tasha Paracetamol take jin daidai, daɗinta ɗaya da ta samu Abdallah ya dai na nuna mata halin ko in kulan da yake mata a gaban mutane sai sun kyeɓe ya nuna bai son zancen ba, shiyasa ma Ummah bata fahimci komai ba dangane da hakan.





Fiamanillah

👸🏼 *QUEEN BK* ...✏

Pokračovat ve čtení

Mohlo by se ti líbit

84.3K 5K 58
Dr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a h...
544K 1.3K 2
A story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......
181K 17K 79
"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane k...
134K 8.7K 55
Kallon kitse ba litaffina bane na marubuciyar nan ne Halima Abdullahi k/mashi