ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

390K 23.8K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 56

5.1K 285 56
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨





💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼







🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )

















Page5⃣6⃣

*KADA KA FIDDA RAI DAGA RAHAMAR UBANGIJI.......*


"Nanawo? Nana? Nanar mu? wannan ai Halimatun muce da ɗiyarta wadda ita da babanta ba'a san ko suna da rai ko sun mutu ba tun faruwar rikicin Damaturu, to ya akai wannan hoton yazo nan Abdallah ko Asma'u waye a cikinsu danni nasan banda wannan hoton tabbas, kai bama Abdallah ke dashi ba, to na Asmah ne kenan kuma sunanta Asma'u kenan itace ɗiyar Halimatun mu data bata kenan, anya to taya hakan ya faru ko shiyasa nake ganin kamarsu kuma nake jin Asmah a jiki kamar ƴata ashe ko ƴata ɗince?" take ta tuna jiranta ake takaddun ta tattaro inda ta sake su ta ɗauki hoton ta fito, mutumin ta ba ya tafi.


Ta zauna tana ƙara nazarin wasu abubuwa wayatta ta jawo zata kira Halima amman sai ta maida har kuma zata kira Naty sai ta fasa tabi ra'ayin zuciyarta akan ta bari ta gaskatar da lamarin tukun, duk da wani ɓangare na zuciyarta na faɗa mata ai ba wani tabbaci da ya wuce wanda ta samu yanzu tunda suna yazo iri ɗaya ga kuma manyan shedu hoton da kamanni da ta daɗe tana maganar shiyasa da biki taso Nana taga amaryar dan tana ta bata labarin kamanninsu itama Nana taso ganin amaryar sai dai a ruɗe ta tafi, tashi tayi tana ta zirga zirga duk ta ƙagara Asmah ta dawo ji take kamar mafarki take bata so ta farka Asmah bata dawo ba taji gaskiyar lamarin.



Wani tunani ne ya faɗo mata rai da sauri ta jawo wayarta ta kira Na iraƙi tace mai yai sauri yaje ya ɗauko Asmah.





Asmah na zaune a tsakar gida bayan sun gama la'asar tana taya Aunty Nafi ɗaura tuwon dare sai wahalar tada wuta suke tana mutuwa saboda wani iska da ake tayi tun shigowar la'asar hadari ne ya taru cunkus a sama daga gani ruwa za'ayi kuma ruwan farko ba, su Asmah masu gona ana tajin daɗi ruwa yazo suna yi suna hirarsu sai suka ji sallama Asmah tasa mayafinta ta leƙa ai sai sukai kiciɓis da Na iraƙi, a ranta tace "to shi wannan ko bai ji lokacin da aka ce ya dawo bane?" katse mata tunani yayi da faɗin "ance na zo ɗaukar ki ne" bayan ya gaisheta.

Cewa tai "gani nan fitowa" ta juya kamar ta rusa kuka take ji.

"Ya naga kina bata rai me  ya faru? waye ne yai sallamar?".

"Wallahi Aunty Nafy Na iraƙi ne wai yazo ɗaukata tun yanzu" ta faɗa tana turo baki.

"To meye na ɓata rai Asmah ban sanki da haka ba, ina ma laifi ai mun gaisa ko gwanda ma da aka zo kina ganin yadda hadarin nan ya taru duk da na farko ne sai akasin tsammani amman da wuya ba'ayi ruwa ba yau duba da yadda hadarin ya taru ai gwanda ki koma ɗakin mijin ki Asma'u ya fiye maki alheri".

"Wayoo wallahi ni ban gaji da ganinku ba".

"Haba ƴar ɗiyata ba muna waya kullum ba kar ki damu sai wani lokacin kuma".

"To shikenan Aunty Nafy bari na ɗauko jaka ta".

"yauwa kayan na nan na haɗa maki cikin ƴar bakko a bayan ƙofa sai ki fito da su kar a manta".

"To".

Har bakin mota Aunty Nafy ta rako su tana ɗaga ma Asmah hannu sai da ta ga ɓillewar motarsu tai saurin shiga gida ganin yadda ƙasa ke shiga idanunta ga yadda iske ke kwaso yaye yaye.

Suna isowa gida part ɗin Ammie tayi direct sai dai yadda ta ga Ammie duk taji tsoro zuciyarta ta fara faɗin to meke faruwa? me ke faruwa dani? me yake shirin samuna? ta kauda tunanin da insha Allah ko ma meye alkhairi ne.

Ta ƙarasa ciki da sallama, Ammie ta amsa tana koƙarin kauda damuwar dake fuskarta, murmushi tayi tace "Asma'u kin dawo ko? sai ki kaga an ɗauko ki tun yanzu ko?".

Asmah ma tayi dariya cikin ƙoƙarin ɓoye tsoron da ke fuskarta cewa tayi "ba komai Ammie ai mun gaggaisa ga kuma hadari ya taso ai gwanda da na dawo ma".

"Yauwa ƴal albarka shigo ki zauna dama ina so na tattauna wani muhinmin abu dake", ta faɗa tana kamo hanun Asmah suka zauna suna facing juna.

Asmah ta yaye gyalenta da jakka ta aje gefe guda tana maida dubanta ga Ammie dan ji meye mahinmin abun.


Ammie tayi gyaran murya tace "dama tunani nayi naga ban sanki ba sosai ina nufin ban san rayuwarki ta da ba shiyasa naji ina kwaɗayin insa ya rayuwarki tada kike ina ne ƙauyenku ma? ina iyayenki suke kuma? in ke marainiya ce to taya akai suka mutu? ciwo sukai? ko ɓata sukai? ina dai san na san duk abunda kika sani game dake da fatan zaki faɗa mun komai?".

Asmah ko da taji tambayar bazata duk sai taji gabanta na faɗi tunaninta ɗaya to me ya faru, wata zuciyar tace mata to me ya faru kuwa dan kawai tana san ta san labarinki, to amma mai yasa abun ya zo kwatsam dole akwai wata a ƙasa, ita dama ta daɗe tana mamakin yadda akai su Ammie basu tambayeta ba, cikin ƙoƙarin kauda tunaninta tayi murmushi tace "Ammie ai bazan taɓa ɓoye maki komai ba insha Allah zan gaya maki duk abunda na sani game dani kamar yadda kika buƙata yanzu kuma".

"To ina ji ƴa ta".

Nan Asmah ta feɗe mata biri tun daga kai har wutsiya na game da labarinta tas ba abun da ta ɓoye mata, sai dai tun da ta fara bata labarin hatsarin da ya faru da ita da iyayenta taga hawayen Ammie sun ƙaru sai data gama tas sannan tayi shiru ita ma tana share hawayen tuna rayuwarta ta da.

Gani tayi Ammie ta faɗi a wajen tayi sujjada sannan ta ɗago ta koma inda take zaune hawaye na ƙara bin kuncinta ta kasa magana mamaki da dana sani take, tana mamakin yadda akai Asmah ta zama ɗiyar Nana da suke ta nema shekaru da yawa da suka wuce da kuma yadda akai duk tsawon zamanta a gidan nan basu gane ba sannan tana dana sanin rashin tambayar Asmah tarihinta da bata yi ba tun farko, nan ta cigaba da kuka itako Asmah ganin kukan na Ammie yayi yawa har ya wuce misali ya sata share mata hawaye tana faɗin,

"Ya haƙuri Ammie dan Allah ki daina kuka komai ai ya riga ya wuce ya zama labari da tarihi dan Allah ki bar kuka".

Ji tai Ammie ta jawo ta ta rungume ta tana faɗin "dama naji a jikina ke jini na ce, ashe na kusa ma ke ƴa ta ce Asmah, no wonder nake ganin halayenki ɗaya da jinin mu Asmah, ni yayar mahaifiyarki ce kuma kamar uwa a gareki". da sauri Asmah ta ɗago cikin mamaki da rashin fahimtar abunda Ammie ke faɗa mata tace,

"Ummata? kin santa ne? dan Allah taya kika san Ummata? ya kuke da ita? tana ina yanzu? tana raye? ko ta mutu kamar Abbah na? Ammie dan Allah kice kisan Ummata dagaske ne ba mafarki nake ba yau na haɗu da wanda yasan Ummata, amman Ammie ya akai kika san ummata?" a kiɗime take jero ma Ammie tambayoyin tana rirriƙe mata hannu tana sakin kuka.

Hannu Ammie tasa tana share mata hawaye tana faɗin "Ay tabbas ba mafarki kike ba na san Ummanki, farin sani ma kuwa".

"Ammie dan Allah a ina kika san Ummata, bayan ban taɓa gaya maki ita ba sai yau?".

Ammie tasa hannu ta jawo hoton da ta aje saƙon kujera lokacin da Asmah ta shigo, ta miƙa mata tana faɗin "ta wannan hoton na san ke ɗiyar Halimatu ce, Halima kuma ƙanwa tace mu biyu ne mata a wajen mahaifiyar mu, Naty kakar kice Asmah kece ɗiyar da muka daɗe muna nemanku ke da babanki wanda har mun fidda ran kuna raye" Asmah da sauri ta karɓa hoton tana dubawa tabbas hoton tane to ya akai yazo hannun Ammie?.

Ammie kamar tasan me take kintsawa a ranta dan haka nan ta kwashe kaf ta faɗa mata yadda akai ta ga hoton da taje ɗauko takardu wanda shine silar aikawa a ɗauko ki dan hankalina ya kasa kwanciya na ƙagara in ji zahirin batun ba shi yasa na aika aka ɗauko ki.

Asmah kam ko da jin haka sai ta ƙara shiga ruɗu tana ganin abun kamar ɗaya daga cikin mafarkanta ne zata tashi ne kawai ta tsinkayi mafarki tayi, tasan tabas in dai ba mafarki take ba to abunda Ammie ta faɗa ba shakku a ciki gaskiyane, da suri ta rungume Ammie tana faɗin,

"Na gode Allah da ya cika mun wannan buƙatar da na daɗe ina roƙan sa shi yasa aka ce *LA TAQNAƊU MIN RAHAMATILLAH* kada ka taɓa cire rai daga rahamar ubangiji, ashe ina zaune da yayar mahaifiyata wadda take itama uwa a gareni ban sani ba, ba mamaki nake jin sonku a zuciyata yafi komai yawa, Ammie yanzu ina Ummata take dan Allah kice mun tana da rai, Ammie kice mun zan iya ganinta ita ma ta ganni, in gana da Ummata" ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka, ita ma Ammie cikin kukan take shafa bayan Asmah tana faɗin,

"Ki kwanatr da hankali ƴata ki daina kuka Allah ya amsa addu'arki, mahaifiyar ki tana raye kuma cikin ƙoshin lafiya, a halin yanzu ba abunda idanta ke marari kallar ta ganki ke da mahaifinki koda ko gawar ku ce dan yafiye mata akan rashin ganinku gaɓa ɗaya".



"Allah sarki Ummata ashe zamu gana Allahna kai ne abun godiya Ammie dan Allah ki kaini naga ummana".

"Kar ki damu Asma'u zaki ganta very soon amman bazai yu ba yanzu saboda a yanzu haka tana indiya tana jarabawa amman ta kusa dawowa".

"Ammie dan Allah ba yadda za'ayi ko muryarta ne inji bazan iya bacci ba in bamu gaisa da ita ba".

"Ba wai naƙi bane Asmah sai dai yanzu in har tasan kina nan to hankalinta bazai kwanta ba, gobe da safe zaki ganta, kuma kinga suna jarabawa ne hasali ma da ƙyar aka shawo kanta ta yadda tai karatun domin rashinku ya zame mata wani babban giɓi a rayuwa a sanadiyar haka ma yanzu haka ma tana da ciwon zuciya, domin bayan faruwar abun da akai ta bincike kuma ba'a ganku ba baku ba labarinku ta shiga wani mawuyacin hali duk ta koma abun tausayi domin lokacin ma fita hayyacinta tayi gaɓa ɗaya ta koma kamar wata zararra an daɗe kan a shawo hankalinta, da addu'a dai da temakon Allah dai yasa bayan shekara ɗaya da abun ta ɗan dawo da natsuwarta ta cigaba da fauwala ma Allah komai amman duk da haka in ta tuno ba ƙaramin tashin hankali take shiga ga ciwon ta ya tashi dan ma likotoci sunce ta daina ɗaga hankalinta sosai shine ma su mama(Naty) da Abbah(sarki) suke ɗan kwantar mata da hankali, bayan shekara shida da faruwar hakan maza sun ta zuwa neman auren Nana amman ta tubure sam ita tananan da auren Muhammad Maska a kanta kuma zaku dawo gareta, duk da malamai sun gaya mata da aure ya akai shekara huɗu ba abunda ya shiga tsakani miji da mata ko cummunicating basa yi a tsakanin su to wannan aure ya mutu, Amman Nana sam taƙi bawa kowa fuska duk kuwa da yadda Abbah da mama suke matsanta mata akan tayi auren amman taƙi, ganin in ma suka kawo mata maganar auren ƙaramin hauka take tada masu ga kuma ciwonta shi yasa ma suka daina mata maganar sai dai a bita da addu'a, Mai babban ɗaki ma ita kanta ba yadda batai da Nana ba dole ita ma ta haƙura ta ƙyaleta domin taga abun ya girmeta, to ganin zaman kaɗaincin da take a gida yayi yawa shi yasa ma su Abbah suka ɓillo da maganar karatu amman shima bata yadda ba ta gwammace tai ta zama a ɗaki tana tunani wata sa'in hadda kuka duk tabi ta lallace ta ƙanjame gashi kullum likitoci cikin ƙara gargaɗi suke ma su Abbah akan ta fidda damuwarta to amman ta kasa, abunda ya ƙara dagula mata lissafi kuma shine hatsarin da Abdallah ya samu domin tayi matuƙar shaƙuwa da Abdallah sosai suna san junansu fiye da yadda bakya zato tun yana ƙarami, itama lokacin bata wuce shera takwas ba sun shaƙu sosai har yazo Abdallah in dai yana hannun Nana bai yadda da kowa ciki kuwa harda ni, to wannan abun da ya faru da Abdallah ba ƙaramin maida ta baya yayi ba dan da har an samu ta ɗan fara sakewa amman hakan na faruwa sai ta ƙara shiga wani halin lokacin abun sai yafi lalacewa yazo ma bata cin abinci har sai da aka kwantar da ita asibiti kuma Nan ulcer tazo tana wahalar da ita, ta daɗe a asibiti har aka sallamota  ta dawo gida ta cigaba da jinya tsawon wata huɗu ta murmure sosai aka samu sauyi cikin sabbin halayenta da take tun faruwar abun sosai dan zata zauna suyi hira da mutan gida har ayi dariya da ita zatai komai normal duk da abun na nuƙurƙusarta can ƙasan zuciyarta, dama tun tana asibiti tuni Abbah yasa ammanta cukun cukun samun gurbin karatu a ƙasar Indiya sai ta riƙa zama a gidan ƙanwar Mama (Naty), tunda ita acan take zaune da mijinta da ƴaƴanta, abunda yasa sukai haka kuwa dan doctor yace a daina barinta cikin kaɗaici shi yasa kawai suka yanke wannan hukuncin, koda suka sanar mata akan batun da tace bata so sai da sukai mata nasiha sosai bata ƙara masu musu ba ta amince, to shine take indiya a yanzu gidan Aunty Maimunatu (ƙanwar Naty) take karatunta inda take karantar likitan zuciya a Dr.Khan medico university yanzu tana shekararta ta biyu kenan dan sun gama wannan jarabawar za su shiga aji uku".

Asmah kam da tunda Ammie ta fara magana take sharɓar kuka ta ƙara fashewa da wani kukan tana tsananin tausayin Ummanta yanzu take ganin ashe ita bata sha wata wahala ba dan nata duk nafila ne akan wuyar da Ummanta tasha, Ammie taƙara jawota ta rungumeta tana faɗin,



"Yi shuru Asmah haka Allah ya tsaro mana kuma mun gode mashi, ba wai na hana ki gaisawa da Nana bane dan wani abu ba sai dan kinga in har taji yanzu  bazata kwantar da hankalinta ba me yuwa ma ba zatai jarabawar ba, shiyasa nace sauran kaɗan ta gama ki haƙura zuwa ɗan lokacin nima wallahi ba wanda ya kaini son ku haɗun sai d......".



Da sauri Asmah ta katseta da faɗin "wallahi na fahimta Ammie mu bari har tagama ɗin Allah ya kaimu lokacin ya bata sa'a".

"Ameen bari ma na kirata naji yaushe zata gama" Ammie ta faɗa tare da janyo wayarta tana latsa nambobin Nana a wayar sannan tasa ta a loudspeaker, ringing biyu aka ɗaga daga ɗayanɓangaren aka fara magana, "hello Adda kwana da yawa baki kirani ba ko har kin manta da ƴar ƙanwar taki ne?" ta faɗa tana dariya.

Ammie cikin saita muryarta tace "haba ina na isa na manta Nanawo kwana biyu ina ta kiranki baya shiga kinsa sai sa'a ake samunku, to ya jarabawa".

"Jarabawa Alhamdullilahi Adda barka da dare ya kuke ina habibina (Abdallah yake cema haka) da matar sa duk dai suna lafiya ko ai ina nan zuwa inga matar habiby duk inajin na ƙagara in ganta wallahi haka nan sai in zauna in ta tunanin matar shi na rasa dalili wallahi, duk ya suke a gaida man su insha Allah first thing in na dawo zan zo na gansu, ai shi kam Habiby na kusan kullum sai munyi waya dashi sai da duk sadda za muyi sai yace baya kusa da matar ko ya fita ko tana bayi".

"Allah sarki kun dai kusa gama jarabawar ko?".

"Ay Addah mun kusa da yake jarabawar kashi kashi ce yanzu wanda muke saura sati biyu mu gama ta sai a bamu hutun sati biyu kuma sannan mu koma mu dasa wata".

"To Allah dai ya taimaka, amman zaki dawo hutun sati biyun ko?".

"Ai da gudu ma addah duk ma na ƙagara wallahi nayi kewar ku da yawa".

"To shiken Nana Allah ya nuna mana lokacin ki maza ki dawo dan zan maki wani albishir da zai saki farin ciki har ƙarshen rayuwarki abunda baki taɓa zato ba baki taɓa tsamani ba, abunda kika fidda rai a samun shi, abu mai mahinmaanci da kika ɓatar da daɗewa ashe yana gidan mu ƙarƙashin kulawar mu amman ban sani ba sai yau na gano".

Cikin sanyi murya tace "kai Addah kar kisa in sauka a kano fa, me ye wannan abun ai ni yanzu ba abunda zan gano ya sani farin ciki har ƙarshen rayuwata ba kallar Asma'u da Abbanta" muryarta ta ƙara raunana, itako Asmah ga farin cikin jin muryar mahaifiyarta ga na abunda ta faɗa yanzu, take kuka yazo mata tasa hannu ta toshe bakinta ba abunda take tausaya wa Ummanta kallar ji da zatai Abbanta ya rasu, mijinta ya rasu, "wayooo Allah Ummana Allah ya sauƙaƙa maki" ta faɗa a ranta, can ta ƙara jiyo muryar Ummanta tana faɗin "wannan albishir ɗin kaɗai zai sani farin ciki har ƙarshen rayuwata Adda amman koma wane albishir ne zaki mun naji ina farin ciki da shi kuma na ƙagara naji ko na gani".


Ammie ta share hawaye tace "Nana kar ki damu komai na Allah ne, amman ina mai tabbatar maki wannan albishirin zai saki farin ciki har ƙarshen rayuwarki Nana, sai kin dawo zan faɗa maki".

"Na gode Addah wallahi har kinsa inajin kamar in yo tsalle in ganni a gabanki, duk na matsu na dawo".

"Kar ki damu ke dai ki dage ma karatunki sati biyu ai kamar gobe ne".

"Kai Adda kin sani ina zullumi wane kamar gobe kwana sha huɗu fa?".

"Ai kin mayi ƙoƙari Nana ke da ƙawa zucin gida ai ban taɓa tunanin zaki iya barin ƙasar nan gaba ɗaya ba, ke da ko kwana ɗaya kikai a wani wajen da ba gida ba sai kinyi zazzaɓi".

"Uhmm wallahi Addah biyayyar iyaye nake".

"To Allah ya baki ladar".

"Ameen Adda da kema ai kina yi".

Bayan sun kashe wayar nan Asmah ta saki wani kuka me tsuma zuciyar mai sauraro, kuka take cike da farin ciki da kuma tausayin mahaifiyarta ita ko Ammie na ta aikin rarrashi, yanzu ta gano Abdallah yawan wayar da suke da wata yana ce mata habibty ashe Ummanta ce, tana jinsu suna waya tun kan suyi aure da lokacin bata damu ba amman bayan sun yi aure kwata kwata bata son taji suna waya duk da ta lura habibtyn bawai budurwarashi bace amman ta lura suna matuƙar son juna shiyasa take kishin ko wace, shi yasa ma wani lokacin in ya dawo ya ce mata habibtynshi na gaishe ta ko ta kanshi bata bi wani lokacin ma suna zaune zata kira shi ita kuma kishi bai barinta ta zauna wajen sai ta shige bayi ta kulle kanta tana jin haushi duk da kullum hirarsu bai wuce ya kake ya kike, da surutai dai rabi shirmen Abdallah, ashe to wannan habibtyn mahaifiyarta ce bata sani ba, taya zatai kishi da mahaifiyarta, ina ma ta yadda sun gaisa ko sau ɗaya ne, kai rashin sani yafi dare duhu, tunani ne barka tai a ƙwaƙwalwarta muryar Abdallah suka ji ya shigo yana dariya yana tsalle yana faɗin "Wayoo! wayoo Allah daɗi ku zo ku gani yayyafi ake a waje wallahi daɗi iskar ruwa fa za'ayi yau, wayoo daɗi".







👸🏼QUEEN BK👸🏼

Continue Reading

You'll Also Like

117K 5.1K 63
Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni h...
12.8K 332 10
NEW COVER ART IS INSPIRED BY THE OLD COVER BY @Somniphobie SOME CHARACTERS ARE FROM THE MUSIC FREAKS MADE BY ROSY CLOZY ON YOUTUBE ❤️ This story is...
256K 18.6K 22
Avantika Aadish Rajawat Aadi, with his fiery nature, adds intensity and excitement to their relationship, igniting a spark in Avni. Avni, like the ca...
6.6M 96.7K 67
Kylie Braun, 16, the daughter of Scott Braun or as some of you may know him as Scooter Braun, never liked the annoying, self centered, jerky supersta...