ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 54

4.9K 272 17
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨







💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼











🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )




















Page5⃣4⃣






Sai wajen sha ɗaya da mintoci suka tashi Abdallah ne ya fara buɗa idanunshi tsayawa yayi yana kallon fuskarta yana murmushi ji yayi jikinta zafi rau, hannu yasa yana zana mata fuska jin lumfashinta yayi yana fita iskar mai zafi gashi sai zufa take, a hankali yace "beauty mai ya faru naji jikinki yayi zafi".




Bata bashi amsa ba amman tana jinshi dan tun lokacin da ya fara zana mata fuska ta tashi, hanunshi ya sa cikin rigarta yaji wuyanta da ƙirjinta duk zafi rau, cewa yayi "wayyo beauty baki da lafiya wallahi jikinki zafi kamar fa ruwan zafi".




A hankali ta buɗa idanunta tana jin jikinta duk ba daɗi ga wani azababben ciwon kai da ya addabeta, ruɗewa yayi gaba ɗaya ganin yadda duk ta faɗa lokaci guda da sauri ya tashi yace "beauty ina zuwa" sannan ya fice.






A falo sukai kiciɓis da Ammie dake shigowa da sallamarta yana ganinta ya isa gareta yace "Ammie kizo kiga beauty bata da lafiya fa" Ammie murmushi tai kawai jin yadda ya ƙara canja ma matar tashi suna, ganin ya ƙura mata idanu yana son yaji tayi magana yasa tace,



"To muje na gani", ta faɗa tare da wucewa ɗakin yana binta a baya.




"Inalillahi Asmah jikinki da zafi masassar kike ne? akwai ciwon kai?".





Ɗaga kai tayi Ammie ta ƙara cewa "kuma kinsha maganinnan dana kawo maki ɗazu".






Ta ƙara ɗaga mata kai, take Ammie ta fiddo wayarta ta kira Dr. Aisha dama kallar wannan case ɗin ita suke kira bayan Dr. Aisha ta tabbatar ma Ammie akan zata taho yanzu ta kashe wayar ta dubi Asmah tace "yo bama kici abinci ba ko naga kalacin dana ba uwar talle ta kawo maku yana nan bisa tebur ko taɓa shi bakuyi ba".







Asmah tace "Ay", komawa Ammie tai falon ta zubo farfesun ƴan ciki da chips da wainar ƙwai sai tea mai kauri data haɗa mata ta dawo ta zaunar da ita zata fara bata, Asmah tace "Ammie bari naje nayi brush".


"Zaki iya ko?" murmushi Asmah tayi tana jin daɗin yadda Ammie ke kulawa da ita, tace "zan iya Ammie".



Da ƙyar ta faɗa toilet tai brush duk jikinta a mace yake bayan ta fito ta zauna bisa gado Ammie ta fara miƙo mata abinci da sauri Asmah tace "zan iya ci da kaina Ammie".




Abdallah dake gefe yana ta binsu da kallo tun ɗazu da sauri yace "Ammie kawo na bata".




"To imaza gashi ni bari naje kafin Dr. ta iso dan baƙi na baro a falo" ta faɗa tana miƙa ma Abdallah plate ɗin tana tafiya bayan ta mata addu'ar samun sauƙi.





Abdallah ya dawo kusa da ita ya zauna ya shiga bata abincin yana hura mata da bakinshi, duk sai taji ya bata tausayi yadda duk ya tada hankalinshi akan ciwonta duk ya marairaice kamar ya cire mata ciwon yake ji, tana iya hango hawaye kwance a ƙwayar idonshi, gashi ya dage so kawai yake taci abincin shi bai ma damu da cikinsa ba sai ya tabbatar ya hura mai zafin sosai yadda bazai ƙona ta ba, fuskar shi ta kamo suka haɗa ido cewa tai "baby na ya akai? me aka maka? me kake so?".






Gani tayi hawayen sun ida gangarowa, cikin kuka yace "so nake ki warke", hannu tasa tana share mashi hawayen fuskar shi cikin ƙarfin hali tace "to bari kuka babyna na warke kaji imaza ka daina kukan".




Haka suka riƙa cin abincin yana bata tana bashi har suka ƙoshi, ƙara taba jikinta yayi yaji zafi yace "beauty ina zuwa", ya fita da ido ta bishi tana jingina bayanta jikin gado, sallamar Dr. Aisha taji da Ammie suka shigo cikin ɗakin nan Dr. aisha ta shiga dubata wata allura tai mata sannan ta rubuta wasu magunguna Ammie ta ɗauki takadar dan taba da a siyo ta fita bayan Dr. Aisha ta gama mata bayanin ciwon Asmah.



Dr. Aisha ta kalla Asmah tace "kar ki damu zazzaɓin zai sauka ciwon kan ma zai tafi in kika samu hutu kuma kika sha magungunan da za a kawo maki sai dai if possible kar ki bari mai gidanki ya kusance ki nan kusa saboda kinji raunuka sosai a ƙalla kwana biyar in zai yu ma sati dan kisamu ki warware kafin lokacin insha Allah wannan allurar da na maki da magungunan zasu sa raunukan su warke da wuri in har ba'a fama su ba".





"To na gode Doctor insha Allah za'a kiyaye".






Abdallah ne ya shigo riƙe da roba a hanunshi, kallon shi Doctor tayi dan dama tasan shi tace "Abdallah me zakai da wannan ruwan?".





Sai da ya aje robar a ƙasa sannan yace "wanka zan ma beauty ita ma haka ta mun da banda lafiya ai".




"wanka?" gani tayi yasa ƙaramin towel a ciki ya matse yana ƙoƙarin goge ma Asmah goshi nan ta gane me yake nufi da wankan da yace murmushi tayi dan taga ana samun improvrment sosai a wajenshi fiye da yadda ta san shi a da cewa tai "to hakan na da kyau sosai ka cigaba, to Asmah Allah ya ƙara sauƙi ni zan wuce" ta faɗa maganar ta ta ƙarshe tana kallon Asmah.




"To mun gode Doctor" shima Abdallah ya maimaita abunda Asmah tace.





Doctor Aisha na fita Uwar talle ta shigo sai da tayi ma Asmah ya jiki kana ta miƙa mata magungunan da Ammie tace ta bata sannan ta fita, Asmah tasha maganain kamar yadda aka rubuta, nan Abdallah ya cigaba da matso tsumman yana goge mata fuska gani tayi yana ƙoƙarin cire mata riga da sauri ta riƙe tana faɗin,




"Ka barshi kaji zan samu sauƙi" turo baki yayi ya maƙe kafaɗa yana faɗin "a'a ya bazan bari ba ɗin nima ba haka kike mun ba inbanda lafiya".






Haka ya zare rigarta ya goge mata wuya zuwa ƙirjinta sai da ya taɓa yaji zafin ya ragu sai yazo ya mata wani tofin add'ua kamar yadda take mashi sannan ya zare rigar shi ya kwanta ya rungumeta yana faɗin "beauty kiyi bacci kinji kina tashi zazzaɓin zai sauka".




Dariya tai tana tuna duk yadda take mashi ne, haka sukai bacci, Asmah daɗinta ɗaƴa Auntyn yara bata nan ake wannan dramar ta tafi asibiti.


Sai da aka kira la'asar suka tashi, ba laifi Asmah ta ɗan ji ƙarfin jikinta sosai, tasa Abdallah tayi bayi ta koya mashi yadda zai yi wankan tsarki bayan ya tsabtace jikinshi suka ɗauro alwallah suka fito suka tada sallah Asmah taja sallar kamar yadda suka saba.






🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚🦚





*BAYAN KWANA BIYU*





Abbah yayo kiran Asmah tana isa falon shi ta tarar da Lawyern Abbah da archtect da waenda zata ba kwangila haka suka zauna suna tattaunawa inda Abbah yaji Asmah ba tayi dai dai ba sai ya gyara mata yanzu an riga an samo waenda zasu yi aikin a gonar har sun fara gyara gona kasancewar damina ta matso, iri kuma duk an siya an aje duk yadda abun zai tafi da kuma yadda za'a shigo da engines ɗin duk ba abunda basu tattauna ba sai dai fatan alkhairi a sana'ar Asmah.





Yau ne Aunty Nafy zata zo dan haka Asmah tun safe ake ta shirye shirye murna wajenta kau kar ku tona, wata lafiyayyar waina da sinasir tayi sai miyar gyaɗa da taji ganda da naman sa, sai wani kunun aya da tayi mai ɗankaren daɗi, bayan ta gama gyara gidan duk ta turare shi tayi wanka ta caɓa adonta cikin wata super da ta sha ɗinki plane zani da riga da tasha parten work da stones tayi kyau sosai ɗan kwalin ta ture a ga tsiyar, kula ta ɗauka ta ɗibar masu Ammie wainan yau har Abbah daban ta ɗiba mai, sashen Auntyn yara ta fara shiga ta kaimata ta ƙara mata ya jiki da yake yau ɗin ta dawo daga asibitin Abujan da taje, bayan nan ta bada aka miƙa ma Abbah sai ta wuce sashen Ammie.





A falo ta iske su zaune da Abdallah, da sallam ta shiga sai data aje kular a gaban Ammie sannan suka gaisa duk da ta lura tun shigowarta Abdallah ya bita da wani kallo wanda ita kaɗai ta san sirrin abunta, ɗan kallan inda yake tayi tace "sannu da hutawa yaya", sai da yayi murmushi sannan yace "beauty kinyi kyau sosai" yana ƙara kallonta, da sauri ta maida dubanta ga Ammie tace "Ammie ya masu jiki?".





"Da sauƙi Asma'u kin shiga kun gaisa ko?".



"Ay Ammie Allah dai ya ƙara sauƙi".



"Ke to to ai na manta ashe yau ne Nafisa zata zo ko?".

"Eh".

"Shiyasa na ganki sai ɗauki kike, tab wallahi duk na shafa'a kinsan jikin tsufa".



Asmah tai dariya tace "laaa Ammie baki wani tsufa ba".



"Bari faɗi Asma'u wane kallar ban tsufa ba, mutum na da jikoki rututu ai saura kaɗan ma in fara ganin ƴaƴan jikoki kuma dan ko yanzun Nabilar Urwa SS1 zata shiga dan kusan sa'oi ne da Mimi, Mimi bata girme mata da yawa ba".




Nan dai suka cigaba da hira can Ammie tace "uhmm kar ki mun wayau bari nima na tashi na shirya ma tarbar muhummiyar baƙuwata".




Asmah tai murmushi tace "Ammie muje na taya ki".



"Da dai kinje kin ba mijinki wainar nan yaci ni kar ya cinye mun tawa" ta faɗa tana kallon Abdallah da ya zuba waina biyu yana ci.





Bayan Asmah ta koma part ɗinta ta shiga kallo wani indiyan film ta sa mai kyau tana yi tana kallon agogo taga har 12 amman bata ji sallamar Aunty Nafy ba, ba'a daɗe ba Abdallah ya shigo yana turo baki, tarbo shi tayi tace "babyna ya akai?".




Shigewa yayi jikinta yace "ba Ammie bace taƙi taban waina naci wai sai inzo wajen beautyta taban".




Asamh tai dariya ta ɗago kanshi tana lakuce mashi hanci tace "to dama taya zaka cinye ma Ammie nata bayan ga naka yana zaman jiranka" ta faɗa tare da jan hannunshi zuwa tebur nan ta zuba mai tana bashi da hannunta shi kuma yana amsa yabawa da kwalliyarta.





Bayan ya gama tayi mashi shigar masallaci ta fita tana raka shi har bakin ƙofa kamar yadda ta saba, bayan ya tafi ta ƙara gyara ko ina ta jawo wayarta da niyar kiran Aunty Nafy taji ko lafiya jin su shiru, sai tajiyo muryarta tana sallama ai da gudu taje ta rungumosu su ukku ne da ita da Yabi sai ko Aunty.




Yabi tace "Maza ki karyani ki ma mijina asara".


Asmah ta ƙyalƙyale da dariya tace "dama me ya rage".

"To bari in juya tunda baki son gani na" ta faɗa tare da juyawa za tai hanyar waje.



Ai da sauri Asmah ta tarota tana faɗin "haba yabi ai bama faɗa kinsani, dawo da Allah".



Dukansu suka kwashe da dariya yabi tace "ni bazan dawo ba sai in kin bani na sosa baki" ta faɗa tana girgiza.




Nan ma dariyar sukai Asmah tace "kar ki damu yabi ai har na sosa haƙori akwai" ta kalle Aunty Nafy tace "ai da har zan kira ku naji shiru".



Yabi tace "ai tun ɗazu muka shigo Hajiya ce ta tsare mu, nan ta cika mana gaba da miya kala kala tace wayau zata maki ta cika mana ciki kan muzo wajenki".




Asmah tai dariya Yabi ta cigaba "shiyasa naci kaɗan saboda in cinye naki duka ki rasa na ba ma mai gidan".





Nan dai Asmah ma ta cika masu gaba da beta sai farincikin zuwansu take duk sun lura da haka dan sai tambayoyi yaushe gamo take masu kuma sun yaba da komai da suka tarar a gidan barin ma tsabtar Asmah haka suka kwashi gara sukai sallah suka sha hira barin ma da Yabi dan ita ce bakinta bai mutuwa to kuma sun haɗu da Asmah, sun ma ɗanyi hira da Aunty Nafy akan sana'ar da ta fara ita ma Auntyn Nafyn ta gaya mata sana'ar da ta ke son ta buɗe da kuɗin, nan Asmah ta shiga bata shawara.






Sai da akai la'asar sannan suka ce zasu tafi nan Asmah ta marairaice tace su kwana, Yabi tace "ke ƴannan rufa mana asiri mu mutu a ɗaka maza su kaimu kawai sai muzo riɗau riɗau muce mun zo kwana kuma wai ana gari ɗaya a'a ke dai ki zauna gidan mijinki ki ta biyayya sai kuma wani jiƙon ko kinzo"



Nan suka ƙara mata ƴan nasihohi a haka bata so ba ta raka su, sai da suka ƙara shiga wajen mai jiki kana suka shiga wajen Ammie dan dama da suka shigo sun gaisa da Abbah, haka Ammie ta cika su da goma sha tara ta arziƙi kamar yadda Asmah ta cika su dashi, sai da suka raka su har bakin gate sannan suka juyo Asmah cike da kyewar su.







Tana komawa ta iske Abdallah a ɗakinshi dan dama ya dawo da suka gaisa ne ya shige ɗaki zaunawa tayi inda yake kwance yana tattaɓa wayar shi, cakulkulo tayi mashi tana zare wayar dariya ya shiga yi ba ƙaƙƙautawa yana lumshe ido, jawo ta yayi jikinshi yana matseta cewa yayi,




"Beauty dan Allah muyi wasan nan ba zan ƙara ji maki ciwo ba".


"Ya haƙuri baby kaga ban gama warkewa ba ko baka son na warke ne?".


"Uhmn uhmn dan Allah beauty niko? niko? to mu ɓata ma".

"A'a baza mu taɓa ɓatawa ba baby" ya buɗa baki ne zai yi magana Asmah ta jefa bakinta cikin nashi nan ta shiga faranta mai ba tare da an kai ga babban ba.









A/N



kuyi haƙuri da wannan da ƙyar na maku typing dan yau a gajiye nake, love y'all😍❤💋bed well.

Continue Reading

You'll Also Like

53.5K 1.9K 12
Just walk in and read, I promise u are going to be mesmerize with the emotional love story embedded in this novel.
3.1K 389 31
Fyaɗe aka yi miki. Shi ne abinda zuciyarta ke ƙara nanatawa. Ban san waye ba, ban kuma san dalilinsa na aikata haka a gareni ba, ni a sanina bani...
8.7K 386 23
A story about Love,Hypcrisy, betrayal, sacrifice and sorrow, Is all about two kingdoms who are families but unknown to them,and they all wish one day...
12.3K 1K 56
Shin abinda nayi zan samu sassaucin allah kuwa bare na iyayena,wanda sun yi alkwarin duk wanda yayi mua'amala dani bashi basu. Taya zan tunkaresu bar...