ZAN SOKA A HAKA

Door queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. Meer

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 50

4.3K 229 9
Door queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )

















Page5⃣0⃣











Muryar Auntyn yara taji ta ƙara faɗin,

"Ai nifa ban yadda da bokannan ba, yace in suka ci sau ɗaya Abdallah sai yaji ya tsane Asmah ita ma haka, yadda ba abunda zai shiga tsakanin su balle a samu tsatson Abdallah, to ni dai sati nai ina zuba masu a abinci, amman ni ban ga sauyi daga yadda suke ba sam, in ma banda sabuwar shaƙuwa da suke ƙarawa, kwata kwata ma bai son yayi nisa da ita fa, dan ma na samu Abbansu cikin dabara nace ya riƙa tafiya da Abdallah kasuwa yana nunnu mai harkar kasuwanci ko zai fahimta, to shine ma fa suke ɗan rabuwa shi ɗinma da ƙyar Abbah ya shawo kanshi ya yadda zaina binsa".


Tai shiru jim kaɗan can kuma tace "haba Jummai na tabbatar sunci abincin nan, sai dai akwai ranar dana hango Asmah tana juye ma Uwar talle abinci a roba, ko da na tambaye uwar talle ce mun tayi kingi ne Asmah ta bata tace ta raba ma almajirai a hanya, shine na tambaye ta ko ta taɓa bata tace yau ne kawai tabata, ke na tabbata sunci abincin nan fa kullum sai na zuba shi kuma ita Asmah ba girki take yi ba balle ince ta girka ance ta huta na sati, kuma ai baza su zauna da yunwa ba ko?".


Can ta ƙara cewa "in ma wannan aikin bai ci ba, zamu koma wajen boka ne kawai ya bamu wanda za'a lalata mahaifar Asmah gaba ɗaya yadda baza ta taɓa haihuwa ba, in kuma har ta samu ciki to tabbas kawai mu kashe Abdallah da ita da abunda ke cikin nata *duk mukashesu*".

Wannan kalmar ta rinƙa yawo a ƙwaƙwalwar Asmah dake tsaya, amman bata jin kanta kamar mutum mutumin ta ce ke tsaya kwata kwata ta rasa mafarki take ko a zahiri take jin wannan mugunta da zaluncin da za'ayi masu su bayin Allah da basu san komai ba, leɓenta ta ciza taji zafi nan tasan tabbas a farke take, zahiri take ji ba mafarki take ba.



Can ta ƙara jiyo muryar na faɗin "ba wata matsala Jummai ai dane nake jin tsoro matsawar haka ta faru kawai *a kashe su*".


Asmah bata san sadda ta saki tray ɗin alabasa ba, ya faɗi yana sakin ƙara, muryar taji ana faɗin "waye nan!".


Da sauri Asmah ta duƙe tana toshe bakinta da ƙarfi kar kukan da yake ƙoƙarin kwace mata ya tona ta ji tai an maimaita, da sauri zuciyarta tace mata "duk abunda za kiyi kar ki yadda ta kama ki anan".


Hannu tasa tana kwashe alabasar da ta zubar da sauri sai da tabbatar ta kwashe komai ta ɗauki tray ɗin da sauri ta wuce part ɗinta Allah yaso cikin duhu ne ila da sai Auntyn yara ta ganta, tana shiga ta aje tray ɗin albasar ta kulle ƙofar ta jingina da ƙofar ta zame a hankali ta zauna tana maida numfashi, ji tai ana buga ƙofar sai da gabanta ya yanke ya faɗi, da sauri ta tura tray ɗin albasar ƙarƙashin kujera ta share hawayenta saɗaf saɗaf tayi ɗaki, sai da taji an ƙara buga kofar ta fito a hankali tana miƙa tana hamma kamar mai bacci tace "gani nan zuwa".


Buɗa ƙofar tai tana hamma, da sauri kuma tace "ahhh Auntyn yara sannun da zuwa ashe kune".

Auntyn yara ta kutso kai ciki tana faɗin "yanzu kika shigo?".

Asmah ta bata guri ta shiga, shiga tai tana ta kalle kalle, Asmah tace "Na ɗan jima da shigowa har na kwanta saboda kai na ciwo yake mun?".

"Kin jima da shigowa owk sai naji kamar Nihal tace kin shiga ba daɗewa  kin kawo abu ko?".

"Ay tun a na tada sallar magruba na shiga na kuma fita na dawo har na kwanta har ma na ɗan fara bacci".

"Owk amman baki ji ƙara ba tanan baya ba?".

"Gaskiya banji ba inaga kamar tsuntsye ne ko?".

"To bandai sani ba na dai ji karar kamar an fasa abu a ƙasa ta gefen window na".

"To ko dai za'a duba ne aga in akwai abunda aka fasa a wajen?".

"Ay to shikenan barshi na duba, sannu da ƙoƙari fa munga pancake bari muje muci, ohhh dakata ya ciwon kan naki?".

"Be daɗe da farawa ba amman nasha magani shine na kwanta".

"Kanki dai kaɗai ke ciwo ko bakya samun tashin zuciya ko, ko kina ammai?".

"A'a Aunty kai na kurum ke ciwo".

"To da sauƙi Allah ya sauwaƙa, ina Abdallan?".

"Baya nan ya fita masallaci".

"To baku samun wata matsala tsakaninku dai ko naga bai cika zama gida ba yanzu lafiya dai ko".

"Aunty lafiya, ni bansan me na mashi ba kawai dai naga ya dena zama a gida".

Sai da wani murmushi ya suɓuce ma Aunty wanda Asmah ta lura dashi infact dama dan ita ta faɗa hakan, taɓe baki tai tace "Allah ya kyauta ni dai na tafi".

Sai da ta ƙara bin falon da kallo sannan ta tafi tana gyara zaninta, Asmah na ganin tafiyarta ta tura ƙofa ta zame bayan ƙofar ta zauna a hankali tace,

"Auntyn yara? Boka? A kashe su gaba ɗaya? da bakinta take faɗin tana zuwa wajen boka, wallahi duk girman da nake bata yau kaf ya zube ba shakka biri yayi kama da mutum, ni dama a raina haka kawai Auntyn yara bata kwanta mun bansan me yasa ba to yau na gano dalili, naji da kunnena me san rabani da masoyana da kuma rayuwata gaba ɗaya, wato a kasheni da ya Abdallah da ɗan da ko cikina ma bai shiga ba, a lalata mun mahaifa? kai haba ba zaiyu ba wannan tasuniya ce yadda nake son ƴaƴa shima ya Abdallah yake son ƴaƴa ace baza mu samu ba,  na kasa haɗa komai me hakan yake nufi?, dama can Aunty ta saba haka ne? ay ta saba saboda tace a dane take jin tsoro, wato yanzu bata jin tsoro imaninta ya gushe har zata iya hallaka rai ukku har kabari, lallai Aunty mugun iri ce wannan shine perfect example ɗin sumumi kasau macijin sari ka noƙe" take Asmah taji "maganin ya Abdallah" yayi mata ringing a ƙwaƙwalwa, fashe wa tayi da kuka.

Cikin kuka take cewa "ba tantama maganin nan ma a wajen bokan ta amso shi dan baya kama da wani maganin gargajiya, ni ta mayar ma maganin gargajiyar, shi yasa duk ta wani dage sai na riƙa bashi akai akai kuma tace kar na faɗa ma kowa, ohhhh ni Asmah na cuci mijina da hannuna, Ya Abdallah wannan itace cutarwa da kake gaya mun kar na maka? inalillahi? yau na haɗa ɗayan mafarkinka ya Abdallah, na gane saƙon dake ciki, na gano ya Abdallah sai dai a lokacin dana gano lokaci ya ƙure domin na rigada nayi maka cutarwa da kake gudun in maka, ya Allah me na aikata da hannuna? yau na shiga uku na? ashe muna tare da makishiyar mu amman bamu sani ba? ashe haka Auntyn yara take? to tsaya ƴaƴanta sun ko san abunda take aikatawa? a'a basu sani ba gaskiya, to su Ammie fa? ko suma ta taɓa cutar su basu sani ba? to tsaya ko dai Ya Abdallah yasan abunda take ne? in ba haka ba mai yasa ya hana mu cin abincin da take aiko mana dashi, kai amman Allah mun gode maka daba mu ci abincin nan ba data gama damu, Allah na gode maka da ka tsaremu ya Allah ka cigaba da tsare mu da dukkan masu so su cutar damu".


Da sauri ta zabura ta tashi tace "wa zan fara faɗa mawa? Mimi? a'a Ammie, kai Abbah kawai, dan bazata cigaba da cutar da mutane ba, yau kowa yasan halinta".


Har ta kama ƙofa zata buɗe sai taji zuciyar ta na mata gargaɗi da "Asmah me kike shirin aikata wa ne? ki natsu mana kar kiyi abunda daga baya zaki zo kina da nasani dan ƙeya ce, gwanda ki hango gaba me zai faru kamin ki aiwatar da abunda kike niya".

A fili tace "kuma fa haka ne, yanzu idan naje na faɗa masu wannan maganar kara zube, ba yadda za suyi su yadda dani domin su a ganinsu sun san wacece Auntyn yara kuma sun san abunda zata iya da wanda baza ta iya ba, baza su yadda dani ba saboda basu taɓa kawowa a ransu Aunty zata iya aikata kallar wannan ɗanyen aikin kamar yadda ban taɓa kawo wa a raina ba, a ƙarshe tsana kawai zan jawo ma kai na, sannan Aunty Nafy ta ƙara ƙaimi wajen cutar damu tunda taga an yadda da ita, kenan faɗan zai koma gaba da gaba ni da ita kenan kuma ni ba me bin baya na, gwanda in mata kwantar ɓauna yadda zan gama da ita lokaci guda ba tare da wata matsala ba, ita tana can tana saita muguntar ta ni kuma daga gefe ina wargaza mata sha'ani, to amman taya zan iya yin hakan? taya zan iya sanin mugayen ƙulle ƙullen ɗa take yadda zan mata harin ba zata? taya?".


Ƙara fashewa tai da kuka tace "Ya Allah ka kawo mun mafita, ya Allah kada ka basu damar cutar damu ko misƙala zarra, ya Allah ka kare mu da karewarka mai girma".


Jingina tayi a bango tana wani kuka mai tsuma zuciya, yanzu ta ƙara yadda ya Abdallah ƙaddarar tane, kuma ta ɗaukar ma kanta alƙawarin koman rintsi koman wuya tana tare da shi, za suyi yaƙi tare su ci nasara tare, za suyi ɗariya tare su kuma yi kuka tare, zasu zauna da juna koman wuya har abada.



Ji tai an ƙwanƙwaso ƙofa zuciyarta sai da ta yanke ta faɗi, cikin fargaba ta buɗe ƙofar idonta yaci karo da masoyinta, da gudu ta ƙarasa ta rungume shi da ƙarfi har tasa yana taku ɗaya baya, riƙo ta yayi suka shigo cikin gida sai da ya kulle ƙofa da ƙyar ya ɗago fuskarta dan ta maƙalƙale shi, ganin yadda idanunta suka canza kala suka kumbura cikin tashin hankali yace,



"Inalillahi Asmah! me yake faruwane bana ce ki daina kuka ba nace ki daina zubar mun da hawayenki, waye ya taɓa ki? ki faɗa mun na maki alƙawarin bazai kwana lafiya ba" ga mamakinta gani tayi hawaye ya fara sintiri a fuskar shi, zamewa yayi ƙasa cikin kuka yace "meye dalilin kukanki?".


Ita ma zamowa tayi ta zauna kusa dashi tace "yayana dan Allah ka yafe mun, na maka wani babban laifi amman a rashin sani dan Allah ka gafarceni na cutar dakai amman na maka alƙawari in the future hakan bazai sake faruwa ba, duk abunda yazo ni zan fara tantance ingancinsa kafin na aminta na baka shi, in cutarwa ne ni zai fara samu kuma ba zai zo gare kaba, zan tsare ka da kariyar Allah, zan iya fansa rayuwarka da rai na yayana, zan iya mutuwa dan ka rayu".

"In kika faɗa haka kin yi rashin adalci ƙanwata, zan rayu dake zan mutu dake, sai kina raye zan rayu in ko kin mutu Abdallah ma ya mutu" ya faɗa yana girgiza kai wasu sabbin hawaye suna bin kuncinsa.



Asmah batasan sadda ta tallafo shi ta jefa mashi bakinta cikin nashi ba, yau ko sai da ta nuna mashi tsantsan so da ƙauna da zuciya da gangar jikinta ke mai, wanda kalamai basa iya furtawa".



Duk ta gama susuta Abdallah ya gama sakin layi, sai da suka gaji sannan Abdallah ya jawo ta ya rungumeta, sun ɗauki mintuna shiru kowa da tunani kala kala a zuciyarsa can Asmah tace,


"Baby na ka faɗa mun duk abunda ka sani domin in samu damar kare ka da izinin Allah, domin zamu gudu tare ne mu tsira tare".

"Meye na sani?" ya faɗa yana ƙara cusa kanshi a wuyanta.

"Me yasa ka hana mu cin abincinnan?".

"Saboda ni girkin ki kaɗai zan iya ci ya gamsar dani".

Ƙara rungumoshi tayi tace "na gode babyna kar kaci abincin kowa sai nawa kaji?".

"Naki kaɗai nake iya ci".

"Na gode sosai, ina sonka baby na".

"Nafi sonki".

"Bawani na fika".

"Za mu gani to".

"To shikenan" ta faɗa tare da sakinshi tana kallonshi ido cikin ido can tace "babyna kana mafarkina? kana ganina a mafarkinka?".



Ɗaga mata kai yayi alamun "eh" cewa tayi "me kake gani a mafarkenka duka ka bani labari kaji".


Sosa kai yayi yace "na manta duka wallahi".

"Daga yau in kayi mafarki kana tashi kaban labari kaji babyna".

Ɗaga mata kai yayi, tace "promise" ta faɗa tana dunƙule hannu tana miƙa mai, shima dunƙule wa yayi ya buga mata yace "yah promise".






A/N


Whoaaaashhh na gaji wallahi sai gobe, take care❣💋.

Nyt.

Fiamanillah
👸🏼QUEENBK👸🏼

Ga verder met lezen

Dit interesseert je vast

3.9K 187 11
Labarin wata ba fulatanar budurwa mai suna FANTA! Da matashin saurayin ta MAHBUB dan birni😉 Written by MISS XOXO and NAFEE ANKA😍 (2016...)
32.5K 2.3K 21
Ta zaci gamo tayi da aljani ashe ba aljani bane mutum ne kamar ita , soyayya ce kawai tsakanin su
1.5K 168 22
saukakekken hanyar shiga,Amma naiman hanyar fita it will be diely.......WHEN IN NO WAY OUT
7.6K 310 36
labari mai matukar ban tausayi, son zuciya, soyaaya mai zafi da shiga rai, hadi da nadama.....