ZAN SOKA A HAKA

Oleh queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. Lebih Banyak

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 41
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 47

4.9K 253 22
Oleh queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana insha Allah🤜🤛 )

















*MY WATTPAD READERS THIS PAGE IS YOURS, ILSVM GUYS, I LOVE YOUR COMMENTS, DO COUNTINUE VOTING THANKS TO ALL THOSE WHO VOTED FOR MY STORY IT REALLY MEANS ALOT MAY ALLAH SWT BLESS U ABUNDANTLY, ONE LOVE, ALLAH HAFEEZ TO YOU ALL. 🥰😍❤💋💕💝💘💖💞 .*







Page4⃣7⃣



*WAJEN MU'AMULAR KA DA IYAYENKA, DANGINKA, ƘAWAYENKA, ABOKANKA, IYALANKA KADA KAYI YAUDARA DAYI MASU ƘARYA KA SANI ZA'A YI HISABI A TSAKANINKU.........*
QUEENBK.












Sai da ta ɗaura kallabinta sannan ta buɗe ƙofa, Mimi ta gani tsaye da basket da sauri ta jawo ta ciki tana rungume ta tace "ayyah sisto nayi missing ɗinki".



Mimi tai dariya tace "wai ya na ganki garas ai ni nasha baza ki iya tashi da safen nan ba".

"Saboda mi?".

"Bansani ba, ai da ninan gashi nazo yi".

Asmah ta kwashe da dariya tace "wallahi Mimi duk kin canza Zarah ta shafa maki virus ɗinta".

Mini tai dariya tace "wooo ina ni ina kamo Zarah, ai yau ban baki labari tunda asuba ta kirani wai na shirya naje na taimaka maki tasan kina cikin yanayi, nace ohh Zarah ke da abun ma kika kwana a ranki".

"kai Zarah batada dama, wallahi har nayi missing ɗinta".


" Hmmmm ai ni da ƙyar nayi bacci jiya dan ma su Zaitoon na nan in suka tafi yake nan".

"Allah sarki sis sai ki dawo nan da kwana".

Harara Mimi ta watsa mata tace "tarewa nan kawai zanyi, ke tsaya ma kinga yadda kika fito amarya sak kuwa wallahi kayan sun amshe ki".



Asmah ta juya idanu tana jujjuyawa tana faɗin "dan Allah sis?".


"Wai ke ina ya Abdallah ko har kin fara ɓoye shine?".

"Sosai me za'a fasa mutuwa ko hisabi?".


"Ba ko ɗaya, uhmm bari in gudu Ammie tace kar na daɗe ga abincin naku nan".

"Allah sarki Amnie ki gaishe mun ita kam mu iso, yanzu za muzo gaisheta, kice mun gode".

"Zan gaya mata amman abincin Auntyn yara ta maku, dan tace ma Ammie ita zatayi".


"To mun gode sosai".



Mimi na fita Abdallah ya fito daga ɗakin shi da hannu yama Asmah alamar waye, tace "mimi ce ta shigo ta kawo mana breakfast amman har ta fita".



Buɗa kulolin ta shiga yi farfesun nama ne sai kunun gyada da fanke, cewa tayi "ya Abdallah kazo muci" ta faɗa tana fiddo mai kujera ɗaya daga cikin na diny ɗin, zuwa yai ya zauna ita kuma ta ɗauko plate da cup ta shiga zuba mashi, tace yaci har ya ɗaga cup sai kuma ya aje, da sauri Asmah tace "lafiya".



Cewa yayi "ban iya cin wannan".

"Saboda mi?"

"Baya ƙamshi kallar naki, ni naki nake so".

cewa tai "ya Abdallah ya za ayi da wannan, ka daure muci da rana sai nama girki kaji".

Kaɗa kai yayi yace "bazan ciba, ni dai kije kimun naki".

Asmah dama tasan hali tace "to" cike da tunanin ko ita mai ma zata haɗa mai, bama tasan da meye da meye a kitchen ɗin ba, rufe kulolin tayi ta nufa kitchen tana buɗe buɗe, taga komai na abinci an tanadar dashi, da sauri ta fera plantain tasa a cikin frying machine ta soya masu ƙwai sai ta haɗa masu quaker oaths, ta gama jera komai ta kai mashi saman diny, ta jawo kujera kusa dashi ta zauna, kular farfesun ta jawo zata ci aman sai gani tayi Abdallah ya janye hadda cup ɗin da ta zuba kunun gyaɗar
cewa tayi,




"Ya Abdallah wai me ya faru ne".

Gani tayi yayi kicin kicin da rai, har ta manta wannan yanayin nasa, ƙasa kasa tai da murya tace "dan Allah ya Abdallana me ya faru? me kake so ne? zan maka ko meye bana son ganin ka cikin wannan yanayin wallahi".


"Asmah kar kici abincinnan, ni dai na gaya maki tunda bazan ci ba kema baza kici ba?" .

Cikin mamaki take kallonsa ko mai yasa duk ya canza mata lokaci guda, cikin sanyin murya tace "haba ya Abdallah to shikenan nabi umarninka bazanci ba, sai kalar naka zanci dan Allah ka maida wuƙar, ka manta ni babynka ce".


Kallo kawai ya bita dashi, Asmah ganin haka yasa ta ɗauki fork ta sa a plate ɗin shi ta fara ci, sai lokacin taga yayi murmushi, tace "yauwa baby na ko kaifa", wage idanu yayi yace da gaske ni babynki ne, ɗaga mashi kai tayi, murmushi taga yayi aranta tace "ashe haka yake sunan shine ban faɗa masa", ta ɗebo ta bashi shima ya ɗeɓo ya bata haka suka ci har suka ƙoshi.



Suna gamawa ta kwashe kayan duk ta kai kicin, ta dawo tace "babyna muje ka canza kaya muje mu gaida su Ammie".

"Meye laifin wannan?" ya faɗa tare da taɓa jallabiyar dake jikinshi.

"Basu da laifi, sai dai babyna yafi yin kyau in yasa manyan kaya".

"Dagaske? to muje ki samun".

Kamo hannunshi tayi suka shiga ɗaki, data duba wadrove ɗin wanda suka fara catching eyes ɗinta ta jawo, wata bugaggar shadda ce light purple tasha aiki captan ce, a ranta tace "anko" ta gama fesa mashi turaransa fogg a jikin kaya, ta taimaka mashi yasa, ta kawo hular da zatai matching ta aza mai bisa kai tace "masha Allah babyna kayi kyau" ta faɗa tana kaishi saitin madubi, taɓe baki yayi yace "ai kin fini kyau".



Dariya Asmah tayi tace "a'a ka fini kyau".

Zama yayi bisa gado ya buga ƙafa yace "wallahi bazan yadda ba kin fi ni kyau".


Ganin in batai wasa ba yanzu sai ta birkitasa tai sauri tace "to na yarda, amman ai kana da kyau" ta faɗa tana janyo hannunsa tace "muje mu gaida su Ammie kaga har 11 ta wuce" ɗauko mayafi tayi ta yana a kanta suka fita, part ɗin Ammie suka fara zuwa nan suka tarar da Abbah zaune shida Ammie suna ta magana cikin farin ciki, Asmah taja Abdallah suka fita bata so ta katse su, part ɗin Auntyn yara suka shiga suka tarar da ita a falo, tana ganinsu tace,

"Ga amarya ga ango, to ku har kun fara fita tun yanzu ko amarcin baku gama ciba?" Asmah murmushi kawai tai cike da kunya, nan suka zauna a ƙasa suka gaisheta.




Ta amsa tana faɗin "kun dai yi kalaci ko, kunci abincin ko?", tun kan Asmah ta ɓuda baki ta amsa taji Abdallah yace,

"Ay munci" da mamki ta kalle shi, sai dai tai shiru tunda mijinta ne ba yadda zatai ta ƙaryata shi, kuma ma da gaskiyar shi ko ba daɗi suka ce basu ci ba tasan Aunty Yara zata ji ba daɗi.


Aunty nafi ta washe baki tace "a to ai yafi, yadai maku daɗi ko?".

Asmah tace "ay yayi daɗi sosai".

"To ko na karo maku ne?" ta faɗa tana niyar tashi, da sauri Asmah tace,

"A'a Aunty mun ƙoshi wallahi"

"To ai shikenan da rana ma kar kiyi girki ni zan maku har sati ɗaya daga nan sai ki fara girkin ki, zuwa lokacin ai kin huta".

"To mun gode Aunty amman da kin barshi wallahi kar mu wahalar dake, girkin ai ba wahala zan iya".

"A'a kul kar naji kin sake faɗin haka, ai dole na maku" su Nihal da yasmeen duk sun fito sun gaisa, sannan suka fita suka koma part ɗin Ammie, har ƙasa Asmah ta gaida su kanta na ƙasa.


Ammie tace "a'aha suwa nake gani haka, kune tunda safe nan?".

Asmah tai murmushi tace "ina kwana Abbah, ina kwana Ammie".


Abbah yace "lafiya lau ɗiyata ya kuke ya kuka tashi, fatan dai ba wata matsala ko?".

"Ay Abbah ba wata matsala na gode da duk abunda kukai mun ubangiji Allah ya biyaku ya saka maku da gidan aljanna".



"Ameen amman kar na kara jin godiyar nan a bakinki".

"To Abbah bazan kuma ba".

Ammie tace "to mu dai mun yafe gaisuwar nan har ta sati ku huta abunku, amman ace daga aure yau da sassafe kuma kun fito, a'a kuyi zaman ku dan Allah mu dai mun yafe gaisuwar nan".



"A'a Ammie dan Allah ya zamu ƙi gaisheku, ba wani abu wallahi dan kawai muzo mu gaishe ku mu samu albarka sai kuma ku hana mu".

Abbah yace "kar ku damu ai albarkar mu kullum tana tare da ku, kibi yadda tace ai ba na har abada bane na lokaci ne".

Ammie kam cikin faɗa faɗa tai magana dan Asmah tasan da gaske take, cewa tayi "kar ki ƙara cewa komai ki yadda kawai in ba haka ba za muyi fushi daku".


"A'a Ammie dan Allah kar kuce haka ai mu bama son fushinku ko kaɗan hakan na iya sa Allah ma yayi fushi damu, dan Allah Ammie kar kuyi fushi damu zamu bi umarninku, ku gafarcemu".



Ammie da Abbah duka sukai dariya, Ammie tace "bama fushi daku kuma ba za mu taɓa fushi daku ba, Allah yasa maku albarka ya baku ƴaƴa na gari daza su maku biyayya kuma".

Abbah yace "Ameen ameen".

Abdallah ko da tunda ya shigo ya isa wajen Abbanshi ya kama mai hannu yana gaisar dashi, jin abunda Ammie tace ya kalli Abbah yace "dagaske muma zamu haifa yara".

Abbah yace "ay da yawa kana so ko?".

"Eh mana ina so, to taya zamu haifa yaran?".

Da sauri Asmah tace "Bari na shiga wajen su Aunty shaila" ta fice da sauri kamin Abdallah ya gama kunyatata.


Ɗakinsu Mimi ta wuce nan ta tarar su Auntƴ Shaila da Aunty urwa nata shirin tafiya, tana shiga su Zaitoon suka taso suka tare ta suna faɗin "Aunty Asmah ina kwana, ina kika je tun da safe muna ta nemanki bamu ganki ba kuma ma Aunty Mimi tace kina gidanki kuma ma mun ce takaimu gidanki taƙi kaimu".

Allah sarki Asmah Allah ya zuba mata son yaran nan barin ma yadda suke sonta, ƙaɗa kai tayi ta kakkamosu tace "ayyah boibies ɗina Aunty Mimi bata kyauta ba da bata kawo man kuba nayi missing ɗinku" ta faɗa tana rungumesu.

Su Nabila Fatima dasu Maheer da Aswad sune manya ƴaƴan Aunty Urwa, dan haka su suna daga gefe suma suna ta watso ma Asmah tambayoyi, Minal ce karama a cikinsu ta kalla Asmah tace "to anti Acma yanju ce ki kaimu gidanci ko".

Asmah tai dariya tace "yanzu kuwa sannan ta juya wajen su Aunty Urwa da suke ta masu dariya tace "ohhh ni na tasa yara sai surutu muke na manta bamu gaisa ba" suka sa mata dariya suna faɗin "ai ke da Mimi ban san wand ayafi wani son yara ba, kema yanzu ai zaki ta zubo naki kin huta".

Asmah ta sunne kai cikin kunya, nan ta gaida su bayan sun gama gaggaisawa Aunty Urwa tace "Amarya da wannan sammako haka, mu dai mun yafe aje a kular mana da yayanmu".

Asmah tace "ayyah Aunty Urawa ai tarevmuka fito dashi".

Suka yi dariya su duka Asmah ta ƙara cewa "Aunty Urwa ya naga kuna ta shiri ba dai yau zaku mana tawaye ba".


"Aiko yau zamu tafi ana sallar azahar".

"Kai wayyo Allah mu dai bamu gaji da ganinku ba".

"Ai muma bamu gaji ba wallahi, to ya muka iya kinga monday yara makarnta gashi nima ina da shara'a ranar monday kuma ban shirya ma zaman ba, kinga ko dole komawa sai anyi hutu kuma".


Da sauri Minal tace "ni dai Aunty ulwa momy tace da jetoon kawai jata, aini a gidan anty acma jata banni ko?" ta faɗa tana kallon Shaila tana ɗaga gira.


Shaila tace "zama ki bar mafarkinkine yarinya".

Asmah tace "Ah ah wai Aunty Shaila har dake wai duk yau zaku tafi, ai nasha ku ba yau ba".

"Ai dole mu tafi saboda ba hutu ake ba".

Ita ko Minal jin abinda momynta tace ta fashe da kuka tana faɗin "ni bajan biku ba, ni ce kun banni nan gulin Dada (Ammie kenan da yake haka jikokin ke kiranta) kullum inje gidan anty acma ta bani shokulat".

Asmah tace "yauwa ƴar gidana aban munke, to maza daina kuka in kina so abarki" ta faɗa tana share mata hawaye.

Aunty Urwa ce ta jawota ganin taƙi shiru tace "ishiru kinji Minal ɗita ki bari ayi hutu sai kice Momy ta kawo ki, kinga makaranta za'a saki, ko baki so kina zuwa skull kamar Zaitoon kinga Zaitoon big girl ce saboda tana zuwa makaranta, kema in kika je za ki zama big girl" da ƙyar dai suka samu sukai convincing ɗinta sannan ta dena kuka.




Mimi ce ta fito daga bayi ɗaure da towel ta fito tana faɗin "waya taɓa mun Minal ɗita nake jiyo kukanta?" ki ciɓis tai da ganin Asmah can ta washe baki cikin zolaya tace "ah ah ha amare ne a gidan namu to barkanku da zuwa, ina kika baro mana babban yaya?".




Ammie ce ta shigo tace "Asmah maza jeki gida Abdallah na jiranki har ya tafi".


"To Ammie".

Ammie ta ƙarasa gurinsu Urwa suna magana, Asmah ta kalli Mimi tace "to ƴar ƙanwa ina nan ina sauraranji sai kin kawo mani ziyara kema".



Mimi tai dariya tace "Ashe wata zatai jiran gawar shanu".




Haka ta tattara yaran suka tafi part ɗinta, ko da ta shiga bata ga Abdallah ba ganin duk inda tabi suke binta tace "ku zazzauna a nan bari na kunna maku tom & jerry, dukansu suka ce eh suna so, ta kunna masu tace bari na ɗauko maku chocolate ta tafi ɗaki ta ɗauko masu cheasy da dai sauransu ta babbasu suna ta murna suna kallonsu.

Asmah ta wuce ɗakin Abdallah zaune yake bisa gado rike da wayar shi sai tsaki yake, ƙarasawa tai inda yake ta zauna tace "ya Abdallah ashe ka dawo?".

Ko kallonta bai ba, hannunshi ta riƙe tace "ya Abdallah me nai maka" yanzu bata san me yasa ba kwata kwata bata son ɓacin ransa ko kaɗan duk sai taji itama ran ta ya ɓaci.


Kallonta yayi yace "bake bace kika gudu ina ta nemaki ba, ba kin mun alƙwari bazaki gudu kibarni ba".



Abun yaso ya bata dariya sai dai tasan in tayi dariya ta kara jagwale abun kenan, cikin murya mai sanyi tace,

"Haba babyna ina zan iya guduwa in barka ni kaina bazan samu natsuwa da kwanciyar hankali ba matsawar baka tare dani, ba guduwa nai ba ina gurin su Aunty Urwa ne".


Dariya yayi sosai dama tasan za'a rina dan yana son sunan da ta kira shi dashi, jawo ta yayi ya rungumeta tace "to babyna kace ka yafe mun mana".


Ɗago kanta yayi yana kallonta cikin ido sannan ya ɗaga mata kai alamun "eh" tace "na gode", hancinsa yasa kan nata yana gogawa a hankali yana murmushi, Minal ce ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin "Anty acma ga maman mu cunjo" ai tuni Asmah ta zare jikinta daga gare shi tace "to Minal muje ko".


Ta kama hannunta suka fita Abdallah ma ya rufa masu baya, nan suka masu sallama akan za su tafi, sannan suka fita Abdallah ma ya bisu, har Asmah ta ɗauko mayafi zata raka su suka ce a'a ta barshi, sannan ta koma, gurin da yaran suka ɓata da cheasy ta share ta goge ta ƙara sa turaren wuta cikin electric burner ta kunna tuni gidan ya ƙara baɗewa da ƙamshi.


Sallar azahar ta gabatar sannan ta nufi kitchen dan gwara ta ɗaura ma babynta abinci dan tasan baze ci abinci ba inba natan ba, da sauri ta gurza Kwakwa, ta dafa mashi coconut rice da miyar dakali da taji kayan lambu, sai ta haɗa coconut and milk shake tasa a fridge, gani tayi biyu da rabi tayi kuma har yanzu Abdallah be dawo ba, ta wuce ɗakinta ta sheƙa wanka da haɗaɗɗen sabulun da Ammie ta bata, bayan ta gama ta fito ta cakuɗe jikinta da mayuka da turarurruka ko wane lungu da saƙo, ɗaya daga cikin dogayen rigunan ta zaro wata mai ɗan karen kyau baƙa ce sai dai taji adon duwatsu tun daga sama har kasa ta zura ta, kwalliya sosai tayi tasa dip red jambaki bayan tayi linen da black gazar sai taɗan murje shi kaɗan tayi matuƙar kyau, ta gama sharce gashinta kenan ta ɗauko ribon zata kama sai taji an turo ƙofa Abdallah ne ya shigo, tsayawa yai ya kafa mata idanu cewa tai,

"Sannu da zuwa ya Abdallah, kayi sallah ko?" ta faɗa tana ƙoƙarin tattara gashita guri guda.



"Munje masallaci da Abbah" kawai ya faɗa yana takowa zuwa gareta, sai da yaje gaf da ita kamar zai shige mata yasa hannu ya cire ribon ɗin da ta nannaɗe gashinta dashi, take gashi ya sakko ya bazu har gadan bayanta, da hannu ɗaya ya rungumo ta ɗayan kuma yasa yana janye mata gashin da ya rufe mata fuska yana maƙala shi bayan kunnenta shafa gashin yake yana shin shinawa can hanci shi ya kai kan wuyanta wani fitinannan ƙamshi yaji daya rikita shi hanci shi yai ta gogawa a wuyanta zuwa bayan wuyanta yana ɗage gashinta, duk yadda Asmah ta so ta hana Abdallah ta kasa, ta rasa me yasa take kasa hana shi a duk lokacin da ya raɓe ta, rinannun idanunshi ya ɗago yana kallonta, sai wani lumshe ido yake kamar yadda ita ma haka nata idanun sukai, tana iya karanta tsantsan ƙauna daga ƙwayar idanunshi, a hankali ya kawo bakinshi dai dai nata, da sauri Asmah ta janye saboda yadda take jin jikinta na kyarma ga yadda Abdallah duk ya rikice da ƙamshinta, duk ya susutata.


Zama yai kan gado dan duk ba ƙarfi a jikinshi, ita kuma Asmah ta jingina da bango da ƙyar ta saisaita lumfashinta, kama gashinta ta ƙarayi ta ɗaura kallabin rigar tace "ya Abdallah muje muci abinci kar ya huce".


Suna fitowa falo suka ji ana ta buga ƙofa, Asmah ta buɗe Nihal ce ta kawo masu abinci, ta iske ta har ta aje tana shirin juyawa ashe ta daɗe tana ƙonƙwasa masu.





Fiamanillah
Queen bk👸🏼

Lanjutkan Membaca

Kamu Akan Menyukai Ini

118K 5.1K 63
Labari ne mai ďauķe da tsantsan tausayi mugun hali zafin kishi da nadama, dan Allah ki yafeni kidawo gareni nasan ban kyauta miki ba,, ku bibiyeni h...
1.5K 168 22
saukakekken hanyar shiga,Amma naiman hanyar fita it will be diely.......WHEN IN NO WAY OUT
16.2K 859 71
'Ammi ya zan yi da rayuwata? Ya kuke so in yi da zuciyata? Ban taba ba...daidai da rana daya ban taba mafarkin yin rayuwar aure ba tare da Ameer ba...
382K 13.1K 53
Anhay Sharma:- Cold business tycoon who is only sweet for his family. He is handsome as hell but loves to stay away from love life. His female employ...