ZAN SOKA A HAKA

By queenbk2020

392K 23.9K 2.2K

#5 tausayi June 2020. #3 tausayi 20 June 2020. #1 munafurci #8 hausa novel. #2 tear drop june 2021. More

page 1
Page 2
page 3
page 4
page 5
Page 6
page 7
Page 8
Page 9
page 10
page 11
page 12
page 13
page 1⃣4⃣
page 15
page 16
page 17
page 18
page 19
page 20
page 21
pahe 22
page 23
page 24
page 25
page 26
page 27
page 28
page 29
page 30
page 31
page 32
page 33
Page 34
page 35
page 36
AUTHOR'S NOTE
page 37
page 38
page 39
page 40
page 42
page 43
page 44
page 45
page 46
page 47
page 48
page 49
page 50
page 51
page 52
page 53
page 54
page 55
page 56
page 57
page 58
page 59
page 60
page 61
page 62
page 63
page 64
page 65
page 66
page 67
page 68
page 69
page 70
page 71
Page 72
page 73
page 74
Page 75
Page 76
page 78
page 79
page 80
page 81
page 82
page 83
page 84
page 85
page 86
page 87
page 88
page 89
page 90
The end and thanks.

page 41

4.7K 257 4
By queenbk2020

🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨🚨
🚨🚨🚨
🚨🚨
🚨






💎💎💎💎💎💎💎💎
*ZAN SOKA A HAKA*
💎💎💎💎💎💎💎💎
NA
*BILKISU ALIYU KANKIA
👸🏼 *QUEEN BK* 👸🏼








🇸🇦 *ZAMAN AMANA WRITTER'S* *((Z.A.W))*🖊
(Gidan zaman lafiya da Amana  insha Allah🤜🤛 )









*WANNAN PAGE ƊIN GABA ƊAYAN SA SAUDAUKAR WANE GA  ZAMAN AMANA WRITTER'S FORUM, GABA ƊAYAN KU, ALLAH YA ƘARA MA ƘUNGIYA ZAMAN LAFIYA DA AMANA DA ƊAUKAKA, YA KI YAYE KU DAGA SHARRIN MAHASADA, INA YINKU ƳAN UWA ONE LOVE,🥰😍❤💋ILYSVM DEARIES🥰❤❤💋💋*

*AUNTY AISHAN UMMA* .
*AUNTY* *RAHEENAT* _( *tawan* )_.
*🅱K (namesy).*
*SEE SEE.*
*LISSAH* .
*MUMMY'S FRIEND.*
*HAPSAY* .
*QUEEN RUKY.*
*AMISA'S GLAM.*
*MEELAT* .
*MAMAN SURAYYA.*
*MAMAR DEEJAH.*
*HAJ CEEYMAR.*
*MARYAM KWARE.*
*REAL KHADY.*
*UMMU AISHA.*
*SAMIRA HAROUNA*

*WANAN PAGE ƊIN NAKU NE KU KAƊAI KUYI YADDA KUKE SO DA SHI, INA KUMA ROƘAN ALLAH UBANGIJI YABA MA 🅱K LAFIYA YASA KAFFARA CE, TAKWARA GWS PLS.*



*INA KUMA SO IN GODE MA DUKKAN WAENDA SUKAYI MUN BIRTHDAY WISHES, A GASKIYA NAJI DAƊI SOSAI GANIN SAƘONNIN KU DA ADDU'OINKU A GARENI, NA GODE NA GODE ALLAH YABAR ƘAUNA, ALLAH YA BIYA MAKU BUƘATUNKU DUNIYA WAL AKHIRA, ءان اءحبك💋😍.*




Page4⃣1⃣




*KI RIƘE ƘAUNAR ANNABI MUHAMMAD (SAW) SAFIYA DA MARAICE TABBAS YAWAITA SALATI GA ANNABI YANA SAMAR DA LADA MAI YAWA DA ƘARA IMANI, KI SANI YAKE ƳAR UWA WALLAHI BAKI DA KAMAR ANNABI MUHAMMAD (SAW).*
                          QUEENBK.






Ammie ta kamo Asmah ta rungumeta wani sanyi taji kamar ta rungume ƴar cikinta, a hankali take faɗin,

"Asmah na gode na gode ɗiyata".

"Ammie me yasa kike gode mun, banyi abunda ya cancanci godiya ba saboda nima ina son ya Abdallah" ta faɗa tare da sunne kanta cikin kunya.

Ammie ta ɗago da ita tana faɗin "ki dai najin kunya ta ni kamar mahaifiya nake a gareki, kuma ke kika cancancin godiya domin ke kika so Abdallah a lokacin da ba kowa bane zai iya sonsa, dan haka kin gama mun komai Asma'u".

"Dan Allah Ammie ki daina faɗar haka, ni wallahi ina son ya Abdallah ne tsakani na da Allah kuma zan kula dashi har karshe rayuwata matuƙar ni Asmah ina shaƙar lumfashi a doran ƙasa bazan karya alƙawarin nan dana ɗauka ba, kuma ni hasali ma bana ganin wata makusa ta ya Abdallah a haka nake son shi, kuma a haka zan cigaba da sanshi".


Idon Ammie ya cika da hawaye, har bata san sadda suka sulalo ba sai dai taji hannun Asmah na share mata tana faɗin "Ammie dan Allah ki daina kuka kar ki sani nima nayi kukan".


Ammie ta jawo ta ta ƙara rungume ta tace "haƙiƙa ba kowa bane zai iya abunda kika aikata Asmah, ko a cikin ƴan uwanka sai ɗai ɗai, inaji a jiki na kamar akwai alaƙar jini a tsakanin mu, Allah ma sanin gaibu".

"Na gode da karamcinku Ammie, ba kowa bane zai iya abunda kuka aikata ma rayuwa ta, kune kuka haskaka rayuwata kuka bani ilimi boko da arabi, kai gaskiya bazan iya ɗirga mutunci da karamcinku a gare ni ba, inaga ni yakamata ace ni na gode maku, sannan in saka maku da duk abunda bai fi ƙarfi na ba, duk da nasan ban iya taɓa saka maku dukan karamcinku sai dai fatan ubangiji Allah ya saka maku da mafificin alkhairinsa".





*BAYAN KWANA BIYU*

Cikin kwana biyun da suka wuce, Ammie ta sanar da Abbah matakin da ake akan lamarin auren, kuma ya matuƙar jin daɗin yarda Asmah a batun, sannan sun shirya da shi da su ya Aminu da sauransu, sunje gidan mal. Sulaiman (yayan aunty nafy) sun nemi auren Asmah, domin shi Aunty Nafy ta naɗa a matsayim waliyyin Asmah, tunda shi aure ba ayin sa dole sai dai waliyin mace da wakilin namiji, dan haka sunje wajen shi, a yayinda shima ya hafu da wasu manya a cikin ƴan uwan shi, an nemi aure an kuma bada, yanzu haka an sa ranar biki sati biyu domin da su Abbah sunce asa sati ɗaya, su aunty nafy suka ce a ƙara sati ɗaya saboda shirye shirye, duk da Ammie tace masu kar su sai komai, za su ma Asmah komai Aunty Nafy tace duk da haka akwai abunda ya kamata ta shirya ita ma tunda ba za ayi auren Asmah bata yi komai ba, dan haka aka sa sati biyu, amman Ammie tace mata komai zata ma Asmah.

A lokacin da labarin ya kai kunnen Asmah kuwa ba ƙarami tsoro taji ba ganin ansa sati biyu abun yazo mata ba zata, ita bata taɓa jin ansa biki wai sati biyu ba, ita a cewar tama ba yanzu ta shirya ma aure ba, su Mimi ne ma suke kwantar mata da hankali wajen cewa ai aure mutuwa haihuwa duk rubuce suke a wajen ubangiji, kowa ranakun su kawai yake jira.




Yanzu Asmah duk a takure take zama a gidan dan sam bata so su haɗu da Ammie ko Abdallah wai kunya take ji, ta ɓangaren Abdallah kam bai son wainar da ake toya waba, shi dai duk rana burin shi kawai yasa Asmah a ƙwayar idanunshi, ita ko Asmah yanzu sam kunyar haɗuwa take dashi, barin ma Ammie, gashi Ammie ta ce sai ana sauran kwana biyar biki Aunty nafy zata wuce da ita gidanta saboda aje al'ada, wannan kenan.





Tuni Abbah an buga katin biki an raba ma ƴan uwa da abokan arziki da duk wasu masoyan Asmah da Abdallah ba wanda bai samu kati ba, Ammie ma ta buga nata na walimar da zata shirya ranar alhamis ana gobe biki kenan, duk yadda suka so bikin kar yayi tsawo amman sai da yayi domin ƙunguyar sodojin su Abdallah sun shirya mashi sword crossing wanda za'ayi ranar laraba da misalin ƙarfe biyu na rana, wannan kenan.





Asmah kwance take kan gado, tunani kala kala a zuciyarta, duk ta ɗan zuge a ranta tace "wai Allah ashe haka amare suke ji in an kusa bikinsu shi yasa suke ɗan rama, Allah ka taimakeni".






"Ayiririririiriririrrirriiiiiii" muryar Mimi ce da Zarah ke rangaɗa buɗa a tare bayan sun shigo ɗakin tare da katse ma Asmah tunaninta, da sauri Asmah ta kulle idonta kamar tana bacci don bata son su mata tsokanar da suka saba.

Zarah ce ta ɗaka mata duka tana faɗin "ke amarya tashi bacci bai ganki ba".


"Wallahi Zarah Allah sai ya saka mun, ina bacci na mai daɗi zaki wani tada ni, nikam ki ƙyaƙe ni kai na ciwo yake mun" ta faɗa tare da juya masu baya tana ƙara kwanciyarta.


Sai dai bata daɗe da juyawa ba taji sun tadata zaune sun ƙura mata ido, cikin shagaɓa tace

"Tace wallahi ku cigaba baku san ya nake ji ba, wallahi kowa lokacin shi na zuwa zan rama ne yara".



"Asmah ji yadda kika zuge kwana biyu kawai" cewar Mimi.


Zarah ko ta ƙyalƙyale da dariya tace " lallai Asmah da sauranki yanzu akan tunanin aure ne ya ramar dake haka?".



"Shiyasa nace ba kusan ya nake ji ba lokacinku na zuwa zaku gane".


Zarah ta ƙara dariya sannan tace "a hayye ai ni in lokaci na yazo daɗi zanji wane tunani zanyi da har zai sa in rame gidan masoyi fa zani fa ba maƙiyi ba, damuwa ɗaya ce ta rabuwa da iyaye bayada haka ni banga abun tunani ba".



"Irin ku masu cika baki, su suka fiyi ma" cewar Mimi.

Asmah tace "ke dai ƙyaleta ai rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, Allah ya kaimu da rai da lafiya, har zata wani ce ba'a fargaba".

"Ameen Allah ya kaimu, yanzu na gane fargabar me kike to meye a ciki da anyi na rana ɗaya zaki saba ai" cewar Zarah tana jujjuya ido.


"Ahhh Zarah kin fi ƙarfinmu ke babba ce" cewar Asmah da Mimi.

Tace "ohhh da ni ɗin karama ce ashe kuna ruwa ban sani ba, yanzu dai ba wannan ba muyi maganar shirye shiryen biki tun wuri kunga dai ba wani lokaci gare mu da zamu bata ba".


Mimi tace "gaskiyar ki ƴar uwa, me ya kamata mu fara shiryawa yanzu?" itako Asmah kishingiɗa tai da gado tana kallansu.



Zarah tace "yauwa kinga maganar kati muma sai mun buga namu dabam saboda ƙaweye ƴan makaranta da za mu gayyato, a taƙaice dai katin ƴan mata wanda zamu raba da chewing gum, kunga kuma ya kamata mu samu event ɗaya wanda zamu tsara ya haɗu tunda ba lokacin shirye shirye da yawa, shi yasa nace muyi event ɗaya yadda zamu ƙayata abun kun san ba za mu gayyato mutane ba kuma muyi harkar ƙaranta mu zudda ma kan mu mutunci ba, mun fison muyi abu azo ayi a watse ana santi ba wai a tafi ana ƙananam maganganu ba ana ƴan gulmace gulmace, kun dai san halin mutane sarai".


Mimi tace "haka ne ƴar uwa ai ba za muyi harkar ƙaranta ba bikin babban yaya da babbar ƙawa fa kinga ko sai abunda ya ture ma buzu naɗi".

Suka yi dariya suka tafa, ita ko Asmah kallon su kawai take Zarah tace "wai ke wannan amarya baki magana kin bar mu sai surutu muke yanzu wane event ki ke so ne ayi?"


"Uhnmn ku dai ku yanke komai, duk zaɓin ku ya mun banda ta cewa" cewar Asmah.

Zarah tace "za mu saita kine yarinya, zama za muyi mu baki lectures kar mu kaiki ki bamu kunya".

"Ji yadda kike magana sai kace wata babba, Allah ya shiya mun ke Zarah".

"Ameen waye bai san shiriya, maganar kuma babba da ƙarama zamu tantace wannan daga baya, da kanki zaki bini dan na baki sirrin, zaki gane ne".



"Yanzu dai ku aje wannan a gefe, muyi abunda zai fishe mu dan kusan ba lokaci gare mu ba, yanzu Zarah ki ƙyale wannan amarya yau bata cikin mood ɗin yanzu dai muyi shirin da ya kamata, maganar event ɗin ayi kamu ko bridal shower ya kika ce?" cewar Mimi tana kallon Zarah.


"Owk me zai hana ayi kamu ina ga kamar zai fi ƙayatarwa dan hanna hango hall ɗin da yadda za'ayi decourating ɗinsa dan gaskiya correct wedding planer zamu ɗauko ba zamu kwaso waennan koro koron ba, dan abun birgewa za muyi".

"Kai wallahi kin kawo shawara shi yasa nake sanki Zarah, yanzu kuma kinga maganar anko dole mu fitar da wuri muje sahad mu haɗo kawai, kuma kinga sai mun zo mun ɗirga mutum nawa za muyi ma anko ko? ga maganar souvenier da zamu raba ranar ko?".


Zarah tace "maganr ki dutse dole muje fidda anko yau ko gobe, dan sabida telolin yanzu ba suda tabbas, sannan maganar mutane nawa zamuyi ma anko kawai ƴan ajin mu gaba ɗaya zamuyi mawa sai ko ƙawayenki, sannan maganar souverniers kuma me zai hana mu bada a mana posses masu kyau sai a ɗan jejjefa eye linners, maskara janbaki, powder dai dai sautansu a ciki, kin gane muyi abun dai da class".



Mimi tace "yayi amman mu haɗa da memo masu kyau mana sai a sa su cikin babba jaka mai kyau".

Tafa wa sukai suna shewa, Asmah ta taɓa baki ta kalle su tace "ji yadda kuke ɗaukar abun sai kace wani gagarumin abu".

Duka suka taso mata suna faɗin "aiko bikin gagarumi ne a wajen mu da duk masoyanki, ai in kinji ana faɗin gagarumi ɗaya kenan, dan ma baki ji muna maganar step dance ɗin da zamuyi ba, haha ai ni na ƙagara ma abun yazo wallahi kiga rawar gwanja da shoki".



Duka suka ɗau sowa suna ta dariya, da ka gansu kasan suna cikin farin ciki, Ammie ce ta turo ƙofar ta shigo da sallama, duka suka amsa mata, Mimi tace "ga Ammie ga Ammie ga mamar Amarya ga kuma mamar ango".



Ammie tai dariya tace "to ƴan matana nazo ne inji shirunku amare meye naku tsare tsaren?"

Mimi tai katsal tace "yauwa Ammie Allah ya maki albarka abunda muke tattaunawa kenan, kinga Ammie za muyi event ɗaya kamu, ga maganar anko ga kayan amarya wanda zata sa, ga souverniers, ga hall da zamu kama, zamu yo hayar weddng planners, ga make up artist Ammie da abubuwa dai da yawa kawai dai yanzu Ammie a sakar mana masu zafi zafin masu maganar a ƙasa sai muyi hidimar mu".


Ammie ta kalleta tana jin jina kai tace "uhmmm amare kun kwaso ta da zafi, yanzu dai maganar wasu wedding planners da make up artist kayan amarya da zata ci biki dasu wannan duk ba naku bane, wannan namu ne ku har ina kukasan waennan, har kuna da designers ɗin da zaku ma amarya kaya lallai yaran nan ashe ku ana ku ku za kuyi waennan abubuwan ashe gwanda da nazo inji shirin ku kenan, kuce da kum kwafsa mana" ta faɗa tana dariya.


Suma dariyar sukai, Mimi tace "ina ruwan garaje mu bamu sani ba sabon shiga ne".

Itako Asmah shiru tai ta sunne kai tun shigowar Ammie.

Ammie ta cigaba "to kunji dai, ku dai kuyi iya hidimarku kubar mu da tamu, sannan naji kuna maganar hall, yanzu duk iya girman gidan nan bai ishe kuba sai kunje can wani gurin?".


Mimi tace "Ammie chasu fa zamuyi".

"A'a mu bama son kuyi mana bidi'a da yawa a bikin nan, sai in hama ma party ɗin, azo ayi biki ayi walima asa albarka ai shikenan".





Cikin shagwaba Mimi tace "ahh ahh haba Ammie baki gane kallar casun da nake nufi ba rawa ne fa, kuma Ammie yanzu shi ake yi ɗan partyn nan, mu ɗan gayyato ƙawayen mu a ci a sha a taya amarya murna a watse, Ammie mu ko maza baza musa a namu ba imu imu mata mu dai ɗanyi Ammie na lokaci ne fa da ya wuce shikenan, haba Ammie dan Allah kar ki hana mu" ta faɗa kamar zatai kuka.



"Ni bazan hana ku ba amman anan gidan za kuyi yanzu ko garden ɗin can akayi decourating ɗin shi, duk yawan ku ai ya ishe ku har ya maku yawa, kuyi abunku cikin rufin asiri ba wanda yaji balle ya gani, kuna can kuna hidimarku muma muna nan muna tamu".



Zarah tace "Ay Ammie haka ma yafi tsari wallahi".

"Yauwa ko kufa" ta juya inda Asmah take tace "Asmah ke banji kince komai ba?".

"Ammie komai yayi".

"Baki da buƙatar komai yanzu? ke tsaya ma naga duk kin faɗa ne".

Mimi tace "tunane tunane take" tana faɗa Asmah ta watso mata harara ƙasa ƙasa.

Ammie tace " tanani na me kuma?, uhmm kinji ɗiya ta ki kwantar ɗa hankalinki ba'aso amarya na tada hankalinta kinji, ki natsu kar kisa komai a zuciyar ki kinji?"

"To ammie na dena insha Allah, kuma bani da buƙatar komai na gode".

Ammie tace "to yanzu ku maganar hidimar taku kuyi estimating komai da komai sai ku faɗa mun kuɗin na baku, kuma ya kamata yau za ku fara wannan hidimar dan kusan abun da yawa mutuwa ta shiga kasuwa, kuma ba lokaci, sannan ina so in faɗa maku inda amarya kuke nufin za kuyi zirga zirgar nan, to na baku daga yau zuwa gobe da safe, daga gobe ta shiga kulle, don gobe shuwa (wata shuwa dake masu gyaran amare a gidan su Ammie) zata iso kun ga da an fara su dilka ba sauran fita, dan haka yanzu sai kuyi maza ku shirya, ga su Mahmud nan sun zo da wani abokin Abdallah sai su kai ku duk inda kuke so".

Jin an ambaci Mahmud yasa Mimi murmushi tace "Ammie yaushe suka zo?".

"Tun jiya da yanma suna gidan nan".

"To Ammie wai yaushe Naty (kakarta) zata zo?"

"Jibi zata taho".

"Aunty Nana fa?"

"A'a ita dai sai satin bikin, saboda suna ta shirye shiryen jarabawa, dan ma an ɗaga masu ita, amman dai jibi zan iske ta can gida dan tare da ita za muje Dubai".



"Au ai ni nasha tana can makaranta (india)".

"A'a tana mai duguri da yake an basu hutun shirya ma jarabawa".

"To shikenan Allah ya kawo mana ita lafiya"

"Ameen, dafatan yanzu na gama daku ko?"

Dukansu suka haɗa baki wajen faɗin "Ay Ammie" sannan ta fita, Asmah ta tashi ta shiga wanka, lokacin da ta fito ta tarar su Mimi na ta list ɗin abubuwan da suke buƙata, kallon su tayi tace yauwa cikin abubuwan ni dai ina son ayi fulani day, duka suka ɗau sowa, Zarah tace


"ko kefa amarya gwanda dai kiyi magana, kinga kin kawo shawara muyi ƙauyawa day kenan zaifi kawo light tunda ba ma suda maraba sosai".

Mimi tace "yayi wallahi".

Bayan sun karɓo kuɗin suma wankan sukai suka shirya cikin hijabansu, suja fito, suna fitowa Asmah tace "Mimi kije ki ƙara kiran Nihal kice zamu fita kasuwa ta zo muje".



Mimi tace "ban san me ya hau kanta ba naga sai sha shan ƙamshi take mana, ɗazu da safe na kirata don mu tattauna abun nan, tace tana zuwa amman kinga har yanzu ba ta ba dalilinta
ban san me ya hau kanta ba, ta koma sai kace Yasmeen".

Zarah ta taɓe baki tace  "ni ban cika san feleƙe ba wallahi in haka ta zaɓa ku ƙyaleta mana".

Mimi tace "ai shine fa, kar taga kamar ma muna son tayi dole ne".

Asmah tace "a'a ku da kata ba haka ake cin ƙwan makauniya ba, ita duniyar nawa take meye ribar rashin haƙuri kuma, kuje ku faɗa mata in tace bata zuwa shi kenan mu dai mun fita haƙƙinta ko?".

"Ay to da naki maganar Mimi jeki kirata".

Suna tsaye Mimi taje ta dawo, Asmah tace "yana ganki ke kaɗai?"

"Wai kanta ke ciwo".

Zarah tace "ku mu tafi kunji ku ƙyaleta koma meye da kanta zata sauko ta dawo tana binmu".

Suka wuce parking loads ɗin gidan dan su Mahmud su suke jira tuntuni, sai dai har sun sha kwana Zarah ta jawo su, suka maƙale a bango, kallonta sukai suka ce "lafiya?".

Cewa tai "Mimi leƙa mun ki gani anya ido na ba gizo yake mun ba, ya Mustafa fa na gani".


Mimi ta ɗan leƙa kanta ta juyo tace "ke dagaske doctorn ki ne fa a wajen to ya akai yasan ya Abdallah ko ya Mahmud ne ya sani?".

"Nima ban sani ba, tab yau ake yinta kishiya tara rana ɗaya".

"Meye na tsoro kuma ke da kika ce baki jin tsoron komai, kar ki bani kunya mana ke da ko rana ba'asa maku ba" cewar Asmah.

"Ba tsoro nake ji ba, kawai dai banyi expecting ganinsa bane".

"Kya dai faɗi gaskiya" cewar Mimi.

Zarah tace "bari na ɗan leƙa naga kamar suna da yawa fa" bayan ta leka ta juyo tace masu "su huɗu ne hada ya Abdallah".

Ɗukkansu basu ankare ba sai su kaga maza biyu sun shawo kwanar ya Abdallah ne da ɗayan da basu sani ba, turus suka tsaya suna kallonsu, shi Abdallah sai kallon Asmah yake, ɗayan ko yace "barkanku amare ya kuka tsaya anan muna ta jira tun ɗazu".

Duka suka haɗa baki wajen cewa "ina wuninku" abokinne kawai ya amsa, sannan ya cigaba "ni sunana Aiman tare mukai karatu da su Abdallah da Mahmud, yanzu wace amaryar ta mu a ciki, nasan dai wannan ƙanwar muce ta Mahmud kenan" ya faɗa tare da nuna Mimi.

Dukkansu ba wanda yayi yunƙurin bashi amsar shi, kallon Abdallah yayi sai yaga ya ƙura ma Asmah ido ita kuma ta sun kuyar da kai, yace "whoashh na ma gane, ba ƙarya abokina duk ka zuzuce banga laifinka ba, sannu amaryar mu" ya faɗa tare da kallon Asmah, nan suka gaggaisa hadda Zarah sannan suka wuce, Abdallah har yayi nisa ya tsaya ya juyo, Asmah kamar ta sani ta juya suka kuwa haɗa ido da hannu ya yafito ta, ɗaga mashi gira tai alamun "ni", karkatar da kai yayi gefe guda ya cigaba da kallonta, cewa tai "ku jira ni ina zuwa" sannan ta nufi inda yake ta tsaya ɗan nesa da shi, tace "ya Abdallah gani".



Matsowa yayi daf da ita kamar raɗa yace "ina zaki?" cikin mamaki ta ke kallonshi tace "kasuwa".


"Kar ki daɗe" yana gama faɗar haka yabi bayan abokinshi, da kallo ta bishi sai daya ɓille tace "uhmmmn iko tun kan mallaka" sannan ta wuce wajen su suka ce "har an gama love ɗin ne".



Tace "A'a farawa akai" dan ta lura in ba haka tai masu ba baza su shafa mata lafiya ba.


Suka tafa hannu, Zarah na faɗin "yauwa ƴar gari haka ake so".


Suka nufa inda su Mahmud suke tsaye, suku ma a ɓangaren mazan sakin idanu sukai suna bin masoyansu da kallon so, barin ma Mustafa da bai yi zaton ganin Zarah anan ba, har suka isa kusa dasu suka tsaya, sai masoyan suka shiga kallon kallon tsakanin su, ita ko Asmah da taga abun ya isheta kuma basu da alamun daina abunda suke tai gyaran murya tare da cewa,


"To ni bari na koma ciki in kun gama sai ku kirani dan bani da jimirin tsayuwa".


Duka suka sa dariya tare da gane me suke, Mahmud ne yace "ya haƙuri a amaryarmu har mun isa mu saki jira".

"A'a ba komai ai sai in maku uzuri".

Mustafa yace "ni duk abun ya ɗaure mun kai, wai Asmah dama itace amaryar Abdallah?".


"Ah ah dama ka santa ne?" cewar Mahmud.

"Ƙwarai da gaske nasan Asmah ƙawar Zarah ta ƙut fa, ai ga Zarah da nake ta baka labari nan" ya faɗa tare da nuna Zarah, ita kam kanta a ƙasa.





Mahamud cikin mamki yace "ikon Allah to ai ga mai gadon zinari da nake baka labari".

Mustafa ya kalli Mimi yace "Ai nasan Mimi, duka su ukun a tare suke".





Dukan su suka kwashe da dariya, Mustafa yace "in haka ne abu yayi kyau best 3 plus special 3".

Mahamud yace "Haka ne fa, yanzu dai kafin nan mu wuce kan Amarya tayi fushi".

Mustafa yace "aiko".

"A'a ni banyi fushi ba kuma bazan yi ba" cewar Asmah.

Duka suka sa dariya, suka shiga mota suka tafi, gurin buga kati da memo da jakkuna suka fara zuwa, sunce masu katin gobe suke san shi, da yake harka ce ta kuɗi nan da nan suka baje masu isassun kuɗi, sukuma masu abun suka tabbatar masu gobe za su gama su zo ko da safe ne su amsa, sun rubuta abunda suke so ya fito a katin sun bada, sannan suka wuce sahad stor suka shiga fidda anko.








☘☘☘☘☘☘☘

Nasan masu karatu za suce ina na aje masu Auntyn yara, to a halin yanzu dai Auntyn yara bata da lafiya shiyasa kuka jita shiru, tana fama da typhoid ne sosai yau ciwo gobe lafiya, to taje asibiti kuma an ɗora ta akan magunguna yanzu dai tana samun sauƙi a hankali sai dai bata ida warwarewa ba, lokacin da ta tsinci maganar auren ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba dan ita a zatonta Abdallah sai dai ya samu mata ƴar low class da bata da kyau ko matsayi, kuma tasan baza ta taɓa kiran Asmah low class ba saboda ko kyanta kaɗai ya isa ya kaita matsayin, to baya da haka tana da ilimi tana da duk wani abu da mace zata bigi ƙirji tace ita macece, sai da jumman jos ta kwantar mata hankali da faɗin "ki kwantar da hankalinki shafa'atu kar ki manta daga ita Asmah har Abdallan a tafin hannunki suke, ke ke juya su, dan haka meye zaki ɗaga hankali akai, sai fa yadda kikai dasu" sannan ta ɗan kwantar da hankalinta.








Ɓangaren ya Aliyu ko abun ya mai zafi barin ma da yaji an sama Asmah rana dan haka ya tattara kayansa yai America inda zai ƙaro karatunsa dama lokaci yayi, ko da Abbansa yayi mai maganar yarinyar da akai maganar aure fa kawai ce masa yayi an sa mata rana,wannan kenan.






Fiamanillah
QUEENBK👸🏼

Continue Reading

You'll Also Like

16.2K 859 71
'Ammi ya zan yi da rayuwata? Ya kuke so in yi da zuciyata? Ban taba ba...daidai da rana daya ban taba mafarkin yin rayuwar aure ba tare da Ameer ba...
544K 1.9K 3
A story of a young Prince and his Mother with two sisters who have been deprived of their rights by a very heartless woman #MAGAJIYA#.......
84.3K 5K 58
Dr.TAHEER labari ne mai cikeda soyayya mai tsuma zuciya...labarin wani matashin likita daya kamu da matsananciyar soyayyar yarinyar da ya raineta a h...
53.5K 1.9K 12
Just walk in and read, I promise u are going to be mesmerize with the emotional love story embedded in this novel.